Daga Umar Faruk,
A jiya ne an ka bukaci mahukunta kasashen Duniya baki daya su kara zage damtse wurin tallafawa lamuran Mata a kasashen Duniya baki daya, kiran ya biyo baya ne a lokacin da Mata ke gudanar da bikin ranar Mata ta Duniya, a Jihar Kebbi tare da kara yin kira ga shugabancin Jam’iyyun Siyasar na kasar Nijeriya da su yi la’akari da shigar da tsarin bada gurabu don tsayawa takarar a cikin kundin tsarin mulkinsu don Karfafa shigar mata cikin harkokin siyasa, don su samun wakilci.
Babbar Sakatariya, Ma’aikatar Harkokin Mata da Jin Dadin Jama’a, Hajiya Aisha Muhammad Maikurata, ce ta yi wannan rokon a cikin wani sako da ta fitar game da bikin ranar Mata ta Duniya.
Sakataren din-din-din, Haka kuma ta kara da bukatar cewa Gwamnati a dukkan matakai da kuma bangaren doka don tabbatar da aiwatar da Manufofin Cigaba Mai Dorewa (SDGs) da kuma tabbatar da Mata sun samu gurabun ayyukan a duk bangarorin gwamnatin masu tasiri tare da ba da dama daidaito ga shugabanci a duk matakin yanke shawara a cikin siyasa, tattalin arziki da yin rayuwa mai walwala cikin al’umma.
Bugu da kari, ta ce Mata na da bukata ta gaggawa ta hanyar baiwa mata cikakkiyar dama zama cikin kasance wa daya daga cikin masu ruwa da tsaki a cikin al’umma, wato (stakeholders) don samun cikakken wakilci.
Hajiya Aisha Maikurata, ta ci gaba da bayyana cewa duk da haka ta yi kira ga kungiyoyin farar hula da su ci gaba da jan hankalin gwamnati a dukkan matakai na Jaha da kuma Tarayya don aiwatar da manufofin da ke inganta daidaiton jinsi na tsakanin Mata da Maza (National Gender Policy) sannan kuma ta janyo hankalin kamfanoni masu zaman kansu da su cire wani bambancin jinsi cikin ka’idojin daukar aikinsu don Mata su samu nasu kaso.
Daga karshe tana Matan kasashen Duniya baki daya murnar zagayowar ranar mata ta duniya. Haka zalika Hajiya Maikurata ta yi kira ga mata da su farka su zama masu dogaro da kai ta yadda za su rage dogaro da mazajensu.