Connect with us

TATTAUNAWA

Bisa Amincewar Matasan Kumbotso Na Fito Wannan Takara, inji Abubakar Kadawa

Published

on

Alhaji Abubakar Salisu Kadawa Matashin dan Siyasa wanda yanzu haka ya sauya alkiblar siyasar Kumbotso, musamman idan akayi la’akari da salon tallafinsa ga marayu da marasa galihu  ga kuma kokarin samawa matasa gurabun ayyukanyi a matakai iri daban daban. A tattaunawarsa da Wakilinmu a Kano Abdullahi Muhammad Sheka Kadawa ya bayyana halin da takararsa ta Majalisar Dokokin Jihar Kano Ke ciki, sannan kuma yace fitowarsa wannan takara nema yake a wurin Allah tare da bayyana wasu daga cikin nasarorin Gwamna Ganduje. Ga dai yadda tatattaunawar ta kasance.

Yanzu Haka bayanai sun bayyana cewa ka sayi fom din takarar kujerar wakilcin Karamar  Hukumar Kumbotso a majalisar dokokin Jihar Kano, shin ko wane hange ake yiwa wannan takara?

Alhamdulillahi kamar yadda ni  Alhaji Abubakar Salisu Kadawa aka sani an haifeni a cikin Karamar Hukumar Kumbotso, nayi karatun firamare a Tukuntawa daga nan na wuce makarantar Sakandiren  Shahuci, sai kuma na wuce zuwa makarantar nazarin harkokin Shari’a ta Malam Aminu Kano. Bayan nan ne kuma muka tsunduma cikin harkokin kasuwanci kamar yadda aka san Bakano da harkar kasuwanci, wannan shi ne takaitaccen tarihin rayuwa ta.

Kamar yadda kowa ya sani ina cikin masu takarar wannan kujera wadda na fi kowane dan takara karacin shekaru, wannan tasa matasa ke ganin cewa lallai lokacinsu ya yi, domin babu wani dalili zai sa a mayar da matasa ‘yan turin mota, bayan kuma kashi 90% na dukkan zabuka matasa ke yinsu.

Wannan tasa na ke kara jaddada cewa na shigo wannan takara ce bawai ko a mutu ko ayi rai bane, a’a na shigo ne domin da farko mu nunawa duniya cewa siyasa ba gado ba ce, kuma akwai bukatar idan kayi- kayi ya kamata ka matsa matasa suma su gwada irin tasu basirar da kishin cigaban al’ummar mu. Saboda haka yanzu Maganar da ake tuni na sayi fom din takara har kuma na cike mun mayarwa uwar Jam’iyya, kuma alhamdulillahi kowa yaji salon zaben fidda gwanin da za’a gudanar a wannan karon na kato bayan kato ne, kenan kaga iya ruwa fidda kai, kowa halinsa ne zai kaishi gaci.

 

Baka ganin akwai wadanda suka jima akan wannan kujera kuma basa sha’awar bari, kuma kai gashi ana ganin kamar yaro ne kai?

Ai abinda ma yasa kenan muka fito wannan takara, domin sanin muhimmacin mu yasa mai girma shugaba Muhammadu Buhari ya rattabawa dokar rage shekarun tsayawa takara domin amfanin Matasa, saboda haka babu wani dalili da zai sa matasa su jada baya, domin wannan lokacin na matasa ne kuma ana sa ran samar da sabuwar Gwamnati wadda ake fatan ganin matasa masu yawa acikinta domin fara haska makomar Jihohin mu dama kasa baki daya. Domin babban abin la’akari  shi ne ya kamata a sani idan da ace suma wasu basu jada baya sun basu wuri ba da har yanzu turin motar suke. Wannan tasa muke kara godewa iyayen mu a siyasance irinsu Alhaji Sule Unguwar rimi wanda kowa yasan dattijon arziki ne da kuma matasa irin Alhaji Mustapha Buhari Bakwana, babu shakka an kamo bakin zaren baiwa matasa damar gwada irin tasu sa’ar a karamar Hukumar Kumbotso.

 

Mene kake ganin zai zama sabo idan aka zabe ka a matsayin wakilin al’ummar Kumbotso a majalisar dokoki  Jihar Kano?

Hakane, kamar yadda aka sani shi halin mutum jarinsa wannan kiranye kiranye suka sa na amince da shiga wannana takara, kuma muna ta yiwa jama’a bayani cewar shi komai da lokacinsa, amma dai abinda kullum na ke fadawa masoya shi ne a kara hakuri muga yadda harkokin siyasar zasu kasance, alhamdulillahi yanzu lokaci ya yi kuma ina tabbatarwa da jama’ar Kumbotso cewa insha Allahu ba zamu watsa masu kasa a ido ba, domin tamu ba irin tasu bace.

 

Idan Allah ya baka wannan dama a matsayinka na matashi ta ina zaka fara, kasancewa akwai abubuwa da dama wanda suka yiwa jama’a batan dabo a aikace?

Alhamdulillahi ina kara jajantawa al’ummar mu ta Kumbotso irin halin da muka tsinci kanmu a ciki duk da cewar wannan karamar Hukuma ta Kumbotso karamar Hukuma ce da Allah ya tarawa tarin albarka, amma mun ka sa gane a ina gizo ke sakar daga mu ne ko shugabannin da muke zaba a matakai daban daban. Bayan haka kuma kamar yadda aka sani yanzu ma da bamu da mulki a hannu mu, amma ina kokarin zakulowa matasa ‘yan gurabun ayyukanyi domin amfanin matasanmu. Wannan tasa muna da kyakkyawar fahinmta da bangarori masu yawa kuma al’ummar Kumbotso ina tabbatar maku da cewa za’a amfana da wannan baiwa da Allah ya yi mana. Sai kuma batun inganta harkar ilimi da koyar da sana’un dogaro da kai, musamman harkar noman zamani, wadanan da ma wasu tarin sirruka na nan cikin kundin da muka tanada da zarar Allah ya amince da bamu wannan dama zamu ci gaba da aiwatar dasu insha Allah. Amma duk da haka ina jan hankalin matasa dasu san inda ke masu ciwo lokacin zama kara zube ya wuce,

 

Honarabul idan muka kalli Gwamnatin Ganduje a shekara uku doriya da tayi akan karagar mulkin Jihar Kano, shin idan da ace za’a bukaci ka bata maki shin ko maki nawa zaka baiwa gwamnatin ta Ganduje?

Duk da ni ba Malamin Lisssafi bane, amma dai ko hasidin iza hasada, komai kauron makin mai duba jarrabawa, ya yi duk abinda zai yi dole ya baiwa Gwamna Ganduje Maki 95%, dalili na anan shi ne akwai manyan ayyukan da suka gagari wasu Gwamnatoci  baya, wadanan ayyukan da ire irensu sun ai 2,100 wadanda aka gadarwa Gwamna Ganduje, ga kuma bashin sama da Naira Biliyon 300,  amma Gwamna Ganduje tuni ya ci gaba da aiwatar dasu, kuma abin ta’ajiba ma shi ne ire iren wadannan ayyuka basa cikin alkawuran da ya yiwa Kanawa

Dubi aikin Lungu Kalkal Karkara Salamu Alaikum, abaya duk an tare ayyuka akwaryar birni jama’armu na Karkara an barsu kawai, amma jeka kananan Hukumomin Jihar Kano 44 ko ina ire ire iren wadannan ayyuka tuni sun isa garesu, wannan tasa ako yaushe Kanawa ke luguden addu’o’i ga gwamnatin Ganduje, sannana kuma yanzu lokaci yayi tunda Gwamna Ganduje ya amince dasake tsaya zamu tabbatar da ganin ya samu kuri’u sama da wanda suka samu a zaben day a gabata shi da aminsa Shugaban kas muhamamdu Buhari.

 

Yanzu haka da guguwar zabens shekara ta 2019 ke kara kadawa, ana tsamun wasu mutane dake dawowa cikin Jam’iyyar ta ku ta APC, shin me  hakan ke nunawa?

‘Yan Jarida Kenan ina tabbatar maka da cewa duk wani mai kishin cigaban Jihar Kano dole ya dawo tafiyar Gwamna Ganduje da Buhari, domin kowa na gani a kasa, alhamdulillahi kamar yadda aka gani ahalin yanzu tsohon Gwamna Malam Ibrahim Shekarau ya dawo wannan Jam’iyya, kuma daman ai akwai mamakin gaske zamansa cikin Jam’iyyar PDP. Saboda haka ina tabbatar maka da cewa haduwar wadanan gwaraza biyu kiyamar wasu ce ta tsaya a siyasar Jihar Kano, saboda haka muna kara jinjinawa Gwamna Ganduje bisa yadda kyakkyawar akidar ke karawa Jam’iyyar APC kima a idon duniya baki daya.

 

Mene Sakon ka ga Al’umamr Kumbotso wadanda kake neman sahallewarsu wakiltar su a majalisar dokokin Jihar Kano?

Alhamdulillahi babban sakona ga jama’r Kumbotso shi ne yanzu haka zaben fidda gwani ake shirin gudanarwa, saboda haka suna da kyakkyawar damar canja duk wnai wakili da suka fahimci kansa da iyalansa kawai ya sani ba cigaban al’ummar Kumbotso ba, su fahimci cewa yanzu lokaci ne na matasa, sannan kuma an ga halin da matasa suka tsinci kansu a wannan karamar Hukuma, ina jan hankalinsu da suyi karatun ta nutsu domin ware tsaba da tsakuwa daban. Su zabi wanda zai kula da ci gaban wanan karamar Hukuma da al’ummar cikinta. Sannan kuma ina kara jijinawa shugabanin mu a wannan Karamra hukuma, musamman jagoran siyasarmu a Kumbotso Alhaji Mustapha Buhari Bakwana, mai kishin ci gaban matasa da kuma sauran shugabannin jam’iyya da iyayen kasa. Muna addu’ar Allah ya amsa addu’o’inmu  baki daya.

 
Advertisement

labarai