Gwamnatin Tarayya ta ce mayakan Boko Haram sun hallaka malaman makarantu 2,295 a jihohin Borno da Yobe da Adama tsakanin shekarar 2009 zuwa 2018, yayin da suka raba sama da dubu 19 da muhallansu.
Kwamandan Rundunar Tsaron (NSCDC), Ahmed Audi ne, ya bayyana haka lokacin da yake kaddamar da wani sabon shirin samar da tsaro a makarantun Nijeriya.
- Zan Ware 10bn Don Inganta Ilimin Matasa Idan Na Ci Zabe – Atiku
- Sin Ta Fitar Da Kundin Bayani Na Farko A Shekarar 2023 Mai Kunshe Da Manufofin Raya Karkara
Audi, ya ce wadannan ‘yan ta’adda sun lalata makarantun da yawansu ya kai 1,500, tare da jikkata dalibai 1,280 tun daga shekarar 2014 kafin a yi nasarar dakile karfinsu.
Kwamandan ya ce wadannan munanan hare-hare sun yi matukar illa a kan harkar koyarwa da kuma ci gaban kasa, abin da ya sa gwamnatin tarayya ta bullo da wannan sabon shiri na samar da tsaron da zai bai wa malamai da dalibai kariyar da suke bukata.
Gwamnatin Tarayya ta dora alhakin samar da tsaro a makarantu a kan rundunar tsaron ‘Civil Defence’ domin ganin an samar da yanayin da ake bukata na bai wa dalibai ilimi.
Shugaban gwamnonin Nijeriya, Aminu Wazirin Tambuwal ya bayyana cewar daukacin jihohi 36 da ke kasar na shirye wajen hada kai da gwamnatin tarayya domin ganin na samu nasarar aikin.