Nijeriya ta gabatar da buƙatu guda bakwai a taron Majalisar Ɗinkin Duniya (UNGA) karo na 81 da aka gudanar a New York.
Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, wanda ya wakilci Shugaba Bola Tinubu ne, ya gabatar da buƙatun.
Ga muhimman abubuwan da Nijeriya ta nema:
1. Kujeru A Kwamitin Tsaro Na Majalisar Ɗinkin Duniya: Nijeriya ta nemi Afirka ta samu kujeru biyu na dindindin da kujeru biyar na wucin gadi.
2.Mutunta Dokokin Ƙasa da Ƙasa: Nijeriya ta buƙaci ƙasashe su bi dokokin ƙasa da ƙasa tare da amfani da diflomasiyya wajen warware matsaloli.
3.Warware Rikice-rikice: Ta buƙaci a ƙara amfani da diflomasiyya wajen kawo ƙarshen yaƙe-yaƙe, musamman a Sudan, tare da kare fararen hula.
4.Amfani Da Fasahar AI: Nijeriya ta ce ya kamata a yi amfani da fasahar AI wajen bunƙasa lafiya, noma, ilimi da tattalin arziƙi.
5.Sauya Tsarin Kuɗin Duniya: Ta nemi a sauƙaƙa wa ƙasashe masu tasowa samun rance da kuma biyan basussuka.
6.Ƙarfafa Zaman Lafiya: Ta buƙaci Majalisar Ɗinkin Duniya ta ƙara ƙoƙarin hana rikice-rikice da yaƙi da ta’addanci.
7.Sauyin Yanayi: Nijeriya ta nemi ƙarin kuɗi, fasaha da ilimi don taimaka wa ƙasashe masu tasowa wajen yaƙi da sauyin yanayi.
Me Ya Sa Tinubu Bai Halarci Taron Ba?
Fadar Shugaban Ƙasa ta ce Tinubu bai halarci taron da kansa ba saboda yana hutu a Faransa.
Shettima ne ya wakilce shi.
Sai dai tsohon Jakadan Nijeriya, Ambasada Aminu Iyawa, ya ce rashin halartar Tinubu na iya hana Nijeriya samun damar ganawa da shugabannin ƙasashe, musamman kan batutuwan bashi da jawo masu zuba jari.














