Ayau Talata, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ke jagorantar taron Majalisar Tsaro ta Ƙasa a fadarsa da ke Abuja.
Mahalarta taron sun hada da mataimakin Shugaban kasa Yemi Osinbajo, da Sakataren Gwamanti Boss Mustapha, da Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa Farfesa Ibrahim Gambari, da Ministan Shari’a Abubakar Malami.
Sauran sun hada da Ministan Tsaro Manjo Janar Bashir Salihi Magashi, da Ministan Harkokin Waje Geoffery Onyeama, da Ministan Ayyukan ‘Yan Sanda Muhammad Maigari Dingyadi.
Sai kuma shugabannin tsaro na rundunonin sojin kasar nan da na ‘yan sanda da na farin kaya da masu tattara bayanan sirri.
Taron na zuwa ne a dai-dai lokacin da akayi awon gaba da kashe mutane da dama a arewacin kasar ta Nijeriya.