Buhari Ya Sa Hannu A Kasafin Kudin Shekarar 2020

Shugaba Muhammadu Buhari ya sanya hannu kan kasafin kudin 2020 na kudi N10.59 trillion a yau Talata, 17 ga watan Disamba, 2019. Shugaban kasan ya sanya hannu ne kan kasafin kudin tare da mataimakinsa, Farfesa Yemi Osinbajo; shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan; kakakin majalisa, Femi Gbajabiamila.

Hakazalika akwai shugaban kwamitin kasafin kudi, Sanata Barau Jibrin; ministar kudi, Zainab Ahmad, ministan kasafin kudi, Jedi Agba da sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha. A ranar 13 ga watan Disamba, majalisar dokokin Nijeriya ta aikawa shugaba Muhammadu Buhari da kasafin kudin inda fadar shugaban kasa tace shugaba Buhari da majalisar zartarwa zasu zauna domin nazarin kasafin kudin.

A ranar 5 ga Disamba, 2019, Yan majalisan sun tabbatar da kasafin kudin ne bayan kimanin kwanaki arba’in da shugaban kasa ya gabatar da takardan gabansu. Shugaban kwamitin kasafin kudi na majalisar, Sanata Barau Jibrin, ya kawo kasafin majalisa bayan kwamitinsa ta kammala bincikenta.

Yan majalisun sun kara kudin da Buhari ya gabatar daga N10.33 trillion zuwa N10.6 trillion (10,594,362,364,830). Ga kiyasin da aka gina kasafin kudin kai da hotunan taron: Danyen man da za’a rika haka a rana: Ganga milyan 2.18 Farashin kowani Ganga daya a : $57 Farashin Dala: N305 / $ Kudin shigan da ake sa ran samu a shekerar 2020: Dagar arzikin Man fetur : 2.64 trillion Arzikin Sabanin Mai (Haraji) : 1.81 trillion Sauran hanyoyi ( sauransu) : 3.7 Trillion

Exit mobile version