Connect with us

MANYAN LABARAI

Buhari Ya Shugabanci Majalisar Zartarwa Karo Na Hudu Bayan Bullar Korona

Published

on

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya shugabanci taron wannan makon na majalisar zartarwa ta kasa wanda ake yinsa ta hanyar talabijin a fadar shugaban kasa da ke Abuja.

Taron wanda aka fara shi da misalin karfe 10 na safiya a zauren fadar ta shugaban kasa, daga cikin masu halartan taron akwai mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo (SAN); Sakataren gwamnatin tarayya (SGF), Mista Boss Mustapha; mai bai wa shugaban kasa shawara a kan harkokin tsaro (NSA), Janar Mohammed Babagana Monguno (Rty.); da shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Farfesa Ibrahim Gambari, duk suna cikin mahalarta taron.

Hakanan daga cikin mahalarta taron majalisar zartarwa ta kasan wanda shi ne karo na hudu da ake gudanar da taron tun bayan da aka sake dawowa da gudanar da ayyuka a fadar ta shugaban kasa a bayan da aka dan kulle fadar, sun hada har da wasu Ministoci guda goma wadanda takwarorinsu suka yi tarayya da su ta hanyar talabijin.

Ministocin sun hada da Ministan ayyuka da gidaje, Mista Babatunde Fashola; Ministan samar da hasken lantarki, Saleh Mamman; Ministar kudi, kasafin kudi da tsare-tsare ta kasa, Uwargida Zainab Ahmed; da Ministan sadarwa da al’adu, Alhaji Lai Mohammed.

Sauran Ministocin sun hada da, Ministan harkokin cikin gida, Ogbeni Rauf Aregbesola; Ministan bunkasa yankin Neja Delta, Sanata Godswill Akpabio; Karamin Minista a ma’aikatar bunkasa yankin na Neja Delta, Sanata Omotayo Alasoadura; Ministan albarkatun ruwa, Injiniya Suleiman Adamu, da kuma Ministar kula da harkokin mata, Dame Pauline Tallen.

An fara gudanar da taron ne jim kadan da gama karanto taken kasa da kuma bude taron da addu’a, inda ake sa ran Ma’aikatun gwamnatin tarayya da suka hada da Ma’aikatar harkokin cikin gida, ma’aikatar bunkasa yankin Neja Delta da ma’aikatar kula da harkokin mata duk za su gabatar da wasu jawabai a wajen taron.
Advertisement

labarai