Shugaban kasa, Muhammadu Buhari zai tafi London a yau dinnan domin a duba lafiyars.
Kakakin shugaban, Femi Adesina ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa ana saran Buhari zai dawo gida Nijeriya nan da makonni na biyu cikin watan Nuwamba.
Buhari Ya Jajantawa Koriya Ta Kudu Kan Rasuwar Mutane 151 Yayin Turmutsutsi
“CBN Na Da Goyon Bayana Wajen Sauya Fasalin Naira” —Buhari
BBC ta rawaito cewa, Shugaban Nijeriya ya sha tafiya Landan domin duba lafiyarsa tun lokacin da ya fara jagorantar kasar.
A 2017, Shugaban ya kwashe kwanaki 150 a Burtaniya a wata tafiyar duba lafiyar da ba a bayyana abin da ke damun shi ba.
Buhari ya kara komawa Burtaniya a watan Mayun 2018 domin ganin liktansa, inda ya yi kwana hudu kacal a kasar.
A watan Nuwambar 2020 ne, mai dakin shugaban kasar Aisha Buhari, ta ce akwai bukatar inganta bangaren lafiya a Nijeriya domin a rage tafiye-tafiyen neman magani kasashen waje.