Hankoron Nijeriya na shiga sahun kasashe masu bunkasar tattalin arzki da masana’antu ya rushe a ‘yan shekarun nan ne saboda rashin tsayayyar wutar lantarki a sassan kasa.
Ga kasar da ke da al’umma fiye da mutum miliyan 200 a yanzu ana iya samar da karfin wutan lantarki ne da ya kai megawatt 13,000 kacal, amma kuma megawatt 4,000 ne kawai ake iya rarraba wa al’umma saboda matsalolin da suka shafi rashin ingantattun na’u’rorin rarraba wutar lantarkin. Ba abin mamaki ba ne yadda ake samun yawaitar rashin wuta da lalacewar na’urorin rarraba wutar, abin da kuma yake haifar da koma baya ga zamantakewa da harkokin kasuwanci a sassan Nijeriya.
- Amsar Xi Jinping Ta Ba Duniya Damar Fahimtar Tsarin Binciken Hada-hadar Kudin Na Kasar Sin
- Gwamnan Zamfara Ya Rage Yawan Adadin Ma’aikatun Jihar Daga 28 Zuwa 16
Watakila saboda ganin muhimmancin wutar lantarki ga harkokin raya kasa ya sanya Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya sanya hannu a kan dokar gyara da kwaskwarima ga bangaren wutar lantarkin Nijeriya a cikin kwanaki 10 da hawansa karagar mulkin, ya sanya hannu a kan dokar wutar lantarki ta shekara 2023 inda aka maye gurbinta da dokar ta shekara 2005, inda aka sake fasalin dokar don ta yi daidai da wannan zamanin da ake ciki.
Dokar za ta samar da yanayin da zai karfafa masu zuba jari a bangaren wutar lantarki musamman a kan abin da ya shafi rarraba wutar lantarki, ta yadda kamfanoni masu zaman kansu za su shigo don aiwatar da tadane-tanaden dokar don amfanin al’ummar kasa da bunkasar tattalin arziki Nijeriya.
A cikin sabuwar dokar, an sahallewa jihohi su bayar da lasisi ga masu zuba jari don su samar da kananan tashoshin samar da wutar lantarki a cikin jihohinsu amma dokar ta haramta rarraba wuta a tsakanin jihohi, ba kamar yadda abin yake a can baya ba.
A karkashin sabuwar dokar ta shekarar 2023, Hukumar Rarraba Wutar Lantarki (NERC) za ta samu damar sanya ido a kan harkokin rarraba wutar lantarki a Nijeriya ba tare da ta yi katsalandan da dokar da da ta ba jihohi ikon gudanar da nasu harkokin ba, amma kuma doka ta bata hurumin sa ido a kan yadda al’amurra ke tafiya a jihohin gaba daya.
Dokar ta kuma bayyana yadda hukumar NERC za ta mika harkokin gudanarwa ga kamfanonin da aka kafa na wutar lantarki a jihohi ba tare da an samu wata matsala ba. Amma kuma NERC za ta ci gaba da sanya ido a kan yadda wadannan kamfanonin ke gudanar da aikinsu har sai jihohin sun kafa nasu dokokin da za su sa ido a kan harkokin kamfanonin da aka kafa. A halin yanzu jihohin Legas, Edo, da Kaduna ne kawai suka samar da dokokin sa ido a harkokin kasuwancin wutar lantarki a Nijeriya.
Wani sabon lamari a cikin sabuwar dokar ya hada da amincewar da aka yi mutum na iya samar wa kansa wutar lantarki don amfanin kansa amma wutar da bai wuce megawatt 1 (MW) ba, amma kuma hukumar NERC ke a ikon sanya ido a kan irin wannan shirin tare da sabunta da lasisi daga lokaci zuwa lokaci.
A mastayinmu na gidan jarida, muna masu yaba wa shugaban kasa a kan yadda ya sa hannu a kan sabuwar dokar, musamman ganin yadda masu ruwa da tsaki suka dade suna ta kiran a samar da yanayin da bangaren wutar lantarki zai yi bunkasar da ta dace, dokar ta fitar da dukkan matsalolin da ke haifar da cikas a kokarin bunkasar bangaren samar da wutar lantarki a Nijeriya, dokar kuma za ta karfafa tare da jawo masu zuba jari a ciki da wajen kasar nan wanda ba sai an fada ba hakan zai samar da bunkasar tattalin arziki saboda manya da kananan masa’nantun Nijeriya za su bunkasa, abin kuma da zai taimaka wajen samar da aikin yi ga dimbin matasan Nijeriya.
Karin jihohi da kanfanoni masu zaman kansu a bangaren samar da wutar lantarki zai karfafa bangaren wutar lantarki ta hanyar samar da sabbin kayan aiki da kwararru daga kasashen waje wadanda za su bayar da gudummawarsu da sabuwar fasahar samar da rarraba wuta lantarkin.
In har aka samu karin jihohi da sabbin kamfanoni a bangaren kamar an yi maganin abin da ya shafi yadda ake samun matsala wajen karbar kudaden wuta ne daga hannun al’umma, hakan zai kai ga samun karin kudaden shiga ga jihohi wanda zai kuma kai ga aiwatar da ayyukan raya kasa da karin zuba jari.
Sau da dama a Nijeriya babbar matsalar da aka fi fuskanta ita ce na aiwatar da tsare-tsare da wai kafa doka ba, a kan haka muke kira da a tabbatar an aiwatar da dokar yadda ya kamata.
Karin kudin wuta da aka yi a kwanan nan da kashi 40 abu ne da ya tayar da hankulan al’ummar Nijeriya, wannan na zuwa ne a yayin da ake fuskantar hauhawar farashin kayan masarufi, tabbas ya kamata a duba wannan karin da aka yi da nufin samar da yanayin da za a rage wa al’umma matsalolin da suke ciki.
Tuni kungiyar kwadago ta NLC ta nemi a gaggauta dakatar da karin kudin wutar lantarkin sai zuwa wani lokaci da al’murra suka daidaita, wannan na da matukar muhimmanci kuma ya kamata gwamnati ta sanya baki don ganin a samar da daidaito a kudin da za a kara don tabbas al’umma da fama matsalar rayuwa.