Ga yawancin ‘yan Nijeriya wannan ba lokaci ne na walwala a harkokin yau da kullum ba, don kuwa kusan dukkan harkokin yau da kullum na al’umma sai tashi yake yi a kullum garin Allah ya waye lamarin yana kokarin kaiwa matakin bantsoro.
Kuma babu wani fatan za a warware matsalar a nan kusa, babban abin da ke a gaban mahukunta a halin yanzu shi ne na yadda za su cigaba da rike madafun ikon tafiyar da kasa a zaben shekarar 2023, a kan haka mutum zai iya cewa, babu wani nau’i na alamun tafiyar da mulki a kasar nan a gaban su gaba daya.
Ra’ayin wannan jaridar shi ne, a halin yanzu yakamata dukkan matakan gwamnati su dawo da akalar su a kan harkokin da suka shafi a’umma don kuwa wannan shi ne nauyi na farko da suka daukar wa kansu kuma shi ne yafi muhimmanci a kan dukkan alkawurran da suka yi a yayin da suke yakin neman zabe da kuma rantsuwar kama aiki da suka yi tun da farko.
Muna jawo hankalin masu tafiyar da gwamnati a dukkan matakai na rashin dacewar yadda aka mayar da al’umma baya, sun zama wasu da basu da wata fata na cimma wani muhimmin abu a raywarsu.
Yana da matukar sauki ‘yan Nijeriya su fahimci cewa, matsalolin da ake fuskanta a sassan kasar musamman abin da ya shafi tafiyar da rayuwa suna kara karuwa ne a kullum kuma babu wata rana da ake tunanin kawo karshen su.
Tun daga darajar Naira zuwa yadda wutar lantarki ta tabarbare da kuma yadda ake samun hauhawar farashin kayyakikn abnici, abin takaicin kuma shi ne ko a jikin ‘yan siyasar mu, duk kuwa da muna cikin kakar zabe inda yakamata a rinka tattauna irin wadannan matsaloli tare da bayanin yadda za su magance su. Ba abin da ya shafe su don kuwa a wannan zamanin sayen kuri’a ake yi ba maganar abin da aka kuduri yi wa al’umma ba.
Wannan jaridar ta lura da cewa, lallai kafin a gudanar da tarukan siyasa tare da zabar ‘yan takara a manyan jam’iyyunmu darajar Naira ta fadi warwars amma lamarin ya kara tabarbarewa ne a lokacin da aka shiga harkokin siyasar gadangadan saboda yadda aka rika kasha wa wakilai masu zabe (Deliget) kudadden kasashe wajen don sayen kuri’arsu.
‘Yan Nijeriya na kallo Naira ya ta faduwa irin faduwar da ba a taba gani ba a ‘yan shekarun nan, wanda hakan kuma ya shafi harkokin saye sayarwa a cikkin al’umma.
A ra’ayinmu babu wata bangare na tattalin arzikin kasar nan daya fi fuskantar matsalar kamar bangaren wutar lantarki.
A tsawon watanni ke nan farashin iskar gas, dizel da man fetur suka yi tashin gwauron zabi, layuka sun kara bayyana a gidajen mai kuma babu wanda zai fada maka ranar da ake ganin za a kawo karshen lamarin.
Lamarin ya kara tabarbarewa ne ta yadda aka samu labarin matsalar da ta fadawa bangaren samar da wutar lantarki inda (National grid) ya rushe.
Wadanna matsalolin sun kuma kara tayar da hankali ne ganin yadda farashin kayyakin abinci suka cigaba da ta’azzara kusan suna neman fin karfin masu karamin karfi, a halihn yanzu koda fiya wata yana neman zama wata alfarma ga ‘yan Nijeriya.
Matsalar tsaron da ake fuskanta a sasan kasar nan ya kara canza tsananin rikicin da ake fuskanta, mun yi magana sau da dama a kan wannan bangaren kuma bai kamata mu sake makalewa wajen tattauna wannan ba.
Wasu na bayar da uzurin cewa, gwamnatin nan na bayar da muhimmanci ga samar da hanyoyi da wasu aikace-aikace na raya kasa, amma a nan muna masu cewa, tabbass rayuwar al’umma yafi wani gyaran titi da za a yi, ina amfanin badi ba rai?, yakamata a bayar da karfi wajen bunkasa rayuwar al’umma.
A yanayin da manyan makarantunmu ke kulle, asibitoci suka zama kufai, kashe-kashe ya zama ruwan dare, sai a fara tunanin ko gwamnnti bata san abin daya kamata ta muhimmantar ba kenan.
Muna kira ga gwamnati a dukkan matakai su dauki abubuwan da suka shafi rayuwar al’umma da muhimmanci, Allah ya taimake mu.