Karuwar kafofin bayar da bashi na bogi a kafar sadarwar intanet a Nijeriya ya haifar da manyan matsaloli ga masu mu’amala da su. Yana da matukar muhimmanci a fahinci cewa, wadannan kafofi sun samu karin bunkasa ne a lokacin da aka fuskanci kulle ne hana zirga-zirga sakamakon annobar cutar Korona, abin da ya sa al’umma da dama suka zauna a gida cikin kunci na rashin kudi, a nan ne kafofin suka fito inda mutane da dama suka rungume su saboda suke da saukin ka’dojin bayar da basuka.
Ga ‘yan Nijeriya da dama, a wancan lokacin, al’amari ne da za a yi wa maraba, al’amarin da al’umma da dama suna runguma ganin ya zo a daidai lokacin da mutane ke cikin tsaka mai wuya na matsalar tattalin arziki da kuma zaman gida da annobar cutar korona ta haifar mana. Kamar dai sauran abubuwan da kan zo mana na alhairi, ana cikin haka ne sai bata gari suka shiga cikin harkar, daga nan abin da aka dauka a matsayin ceto sai ya zama tashin hankali da annoba da masu mu’amala da shi.
Abin takaici a nan kuma shi ne yadda abin da aka dauka a matsayin lamarin da zai kawo sauki ga mutum sai gashi ya zama kafar da ake tozarta mutum tare da kulla masa sharri, musamman daga wasu shugabannin kafofin bayar da basukan. An sha samun abubuwan tashin hankali ga masu cin bashin inda a kan damu wasu mutane da kiran waya ana cewa, su tuntubi wanda ya ci bashi, da kuma karin sharrin cewa, wanda ya ci bashin yana dauke da cutar kanjamau da sauransu.
Akwai labarin wani da ya ci bashin kudi a irin wadancan kafafen, inda suka wallafa sanarwar wai ya mutu, mutumin ya razana kwarai da ya ga sanarwar mutuwarsa tana yawo a kafafen sadarwa inda aka ce wai ya mutu ne a ranar 4 ga watan Janairu na shekarar 2022 kuma wai za a yi jana’izarsa a karshen watan. Wani shi ma da irin haka ta rutsa da shi, ya bayyana yadda wata kafar bayar da bashi ta wallafa hoton da sunansa a shafukan facebook.
Ire-iren wadannan cin mutuncin da kafafen bayar da bashi ta intanet ke yi wa al’umma na da yawan hgaske kuma ya kamata a gaggauata dakatar da su, ya kamata hukumomi su dauki matakan kawo karshen wadannan cin mutuncin da ake yi ba tare da bata lokaci ba. Muna jin dadin yadda gwamnatin tarayya ta hannun Hukumar Kare Masu Saye da Mu’amala da Cibiyoyi ((FCCPC) ta fara daukar tsatsaurar mataki a kan ire-iren wadanan kafofi.
A tattaunawar da shugaban hukumar FCCPC, Babatunde Irukera, ya yi da ‘yan jarida kwanakin baya, ya jaddada kudurin hukumar na kulle duk wata kafar bayar da bashi ta intanet da ta dauki cin mutuncin masu mu’amala da ita ta hanyar yi musu sharri da sauran cin mutunci. Shirin hukumar na goge shafin duk wata kafar bayar da bashi da aka kama da laifin cin mutuncin masu mu’amala daga manhajar goggle zai zama babbar darasi ga sauran masu shirin fara irin wannan dabi’ar.
Ra’ayin wannan jaridar shi ne ya kamata dukkan kafafen bayar da bashi da suka rungumi cin mutuncin masu hulda da su su sani cewa, za su fuskanci hukuncin doka sakamakon ayyukansu na cin mutuncin masu mu’amala da su. Shugaban hukumar ya kara da cewa, a yayin da ake maraba da masu harkokinsu ba tare da karya doka ko cin mutunci mutane ba a kasar nan. Wadanda suka rungumi karya doka a matsayin sana’arsu za su dandana kudarsu.
Ta hanyar daukar mataki, Hukumar FCCPC ta dauki kare hakokin ‘yan Nijeriya masu hulda da hukumomi daban daban, wannan kuma abin a yaba ne. Bai kamata a shiga tozarta masu neman cin bashi ta hanyar aika sakonnin karta ta kwana don cin mutuncin su ba, yana da matukar muhimmanci hukumomi su shigo don tsaftace harkokin kafofin bayar da basuka ta intanet tare da samar da dokokin da za su yi aiki da su don kauce wa wuce gona da iri.
Tabbas barazanar da hukumar FCCPC ta yi na goge manhajar duk wata kafar bayar da bashin da aka samu da laifi daga GOOGLE zai taimaka wajen tsaftace hakar ta yadda da mai bayar da bashin da kuma masu karbar za su yi mu’amala cikin mutuntunta juna.
Yana da matukar muhimmanci a fahinci cewa, mutanen da suke shiga matsala wajen biyan bashin da suka ci, mutane ne da suke fuskantar matsalar tattalin arziki na gaskiya, a kan haka suke garzayawa wajen masu bayar da irin wadannan basukan don neman ceto, saboda haka bai kamata a yi amfani da wannan damar ba wajen ci musu mutunci, irin haka zai kara jefa su cikin hali na damuwa da zai kuma iya jefa su cikin matsalar da ba za a iya sanin yadda za ta kare ba.
Ya kuma kamata a kara kaimi wajen wayar da kan al’umma musamman ma masu mu’amala da kafafen bayar da bashi ta intanet a kan hakokinsu, a kuma samar da hanyar da za su iya kai kokarafi a kan duk wani cin mutunci da aka yi musu a yayin da suke karbi bashi.
Hukumar FCCPC na iya samar da kafar aiki tare da masu ruwa da tsaki don sanya ido a kan ayyukan ire-iren kafofin bayar da bashi ta intanet masu cin mutuncin masu hulda da su.