ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Sunday, December 21, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Bukatar Hukunta Masu Jagorantar Kashe-kashe A Nijeriya

by Leadership Hausa and Sulaiman
5 months ago

A kwanan baya ne, Muyiwa Ige, da ga marigayi Cif Bola Ige, ya yi kira ga shugaba Bola Tinubu, da sake bijiro da batun kisan da aka yi wa mahaifinsa, musamman domin a bankado da wadanda suka aikata kisan, tare da hukunta su.

Yau dai, shekaru 24 ke nan, da aka halka Ige, a gidansa da ke a garin Ibadan, a jihar Oyo, wanda aka kashe shi, a ranar 23 na watan Disambar 2001.

  • Hukumar ‘Yansanda Ta Yi Wa Wasu Manyan Jami’anta Karin Girma
  • Gwamna Lawal Ya Yi Ta’aziyyar Sarkin Katsinan Gusau

A cikin rokon da Muyiwa ya yiwa Tinubu na sake bijro da batun kisan na mahaifinsa, ya bayyana irin halin gallazawa da mahaifinsa, ya tsinci kansa a lokacin kisan, musamman duba da cewa, mahaifin na sa, akawai wasu muradu, na rayuwarsa, da ya so ya cimma, amma kisan ya kawo karashen hakan.

ADVERTISEMENT

An dai hallaka Ige ne, a lokacin da yake rike da mukamin Minitan Shari’a kuma Atoni Janar na kasa.

Bayan gaza cafko wadanda ake zargi da aikata kaisan da kuma yadda akai ta kai Gwaro da Mari a gaban kotu kan batun a wadancan shekaru, haka dai lamarin ya sha ruwa.

LABARAI MASU NASABA

Buƙatar Daƙile Kutsen ‘Yan Bindiga Na Iyakokin Jihar Kano

Buƙatar Ɗaukar Matakin Gaggawa Na Daƙile Kutsen Ƙungiyar Ta’addanci Ta JNIM A Nijeriya

Koda ya ke dai, a lokacin ‘yansanda sun yi nisa ban gudanar bincike, amma babu wanda suka iya kamawa, kuma ba a kara shigar da wata sabuwar kara a gaban kotu ba, duk tsawon wadannan shekarun.

Wannan bukatar da Muyiwa ya biro da ita, tamkar bude wani sabon babi ne, kan batun hallaka manyan mutane a kasar, wadda za a iya cewa, tun daga 1999, har zuwa yau, amma shiru ake ji, kan daukar wani kwakwaran mataki.

A wani taro a kwanan baya, babban Lauya SAN Cif Kanu Agabi, ya bijiro da zargin yadda ake gaza hukunta masu aikata manyan laifuka a kasar, inda kuma ake samun dogon jan kafa, kan shari’ar da ta shafi, marasa karfi a kasar.

Wannan zargin na Kanu, ya nuna a zahiri, yadda aka yiwa bangaren shari’ar kasar, rikon Sakainar Kashi, musamman wajen gaza cafko, masu aikata manyan laifuka, domin su fuskanci hunci.

Bugu da kari, a kasidar da ya gabatar a a taron jamia’r NOUN, tsohon shugaban kasa, Cif Olusegun Obasanjo, ya bayyana cewa, yin gaskiya wanzar da zaman lafiya tabbatar da tsaro, tare da bai wa ko wanne dan kasa hakkinsa, su ne, ginshikin da ke bunkasa tattalin arzikin kasa.

Sai abin dubi a nan, wannan yawabin na, Cif Olusegun, ya kasance yana cin karo da juna, domin a lokacin yana kan Karagar shugabancin kasar ne, aka kashe marigayi Ige.

Cafko irin wadannan masu halka manyan mutane a kasar domin a hukunta su, kamar yadda dokar kasa ta tanada, ba wai kawai hakan zai samar da salama ga ahalinsu bane, musamman duba da yadda suka yi babban rashi, amma hakan zai kuma zama wani babban abin ci gaba, ga kasar.

Kazalka, kamo su din, zai zama tamkar wani gargadi ne, da zai nuna cewa, akwai hukuncin da kasar ta tanadar, ga masu aikata irin wannan halin na rashin imani.

A nan, wannan Jaridar, ta yi waiwaye kan kisan rashin imani da aka akatawa mataimakin shugaban PDP na shiyyar Kudu Maso Kudu Cif Aminasoari Kala (A.K) Dikibo shekaru 21 da suka gabata.

Abin takaici, an hallaka shi ne, da tsayiyar rana a kan wata babbar hanya, a ranar ga 4 Fabiraurun 2004.

Sai dai, har zuwa yanzu, babu wani kokari da rundunar ‘yansanda ko hukumar DSS suka yi, na bankado makasan.

Kazalika, tshohon mataimakin shugaba na Kudu Maso Kudu, rusasshiyar jami’iyyar ANPP Marshal Sokari Harry, an kashe shi a Abuja a ranar 5 ga watan Maris na 2003 a lokacin zaben shugaban kasa

Hakazalika, an yiwa dan siyasa Anthony Olufunsho Williams, kisan gilla a gidansa da ke a rukunin gidaje na Dolphin, a jihar da ke Ikoyi, Legas, a ranar 27 ga watan Julin 2005.

An hallaka shi ne, yayin da ake shirin tsayar da shi, dan takarar gwamna a PDP na jihar Legas.

Rashin daukar matakin, na kara zubur da kimar Nijeriya a idon duniya.

Hakazalika, hakan ya sanya, wasu hukumomin a jihohin kasar nan, ke shawartar alumomin, da su dauki matakan kare kansu, daga hare-haren da aka kai wa jama’a, wanda hakan karara, ya nuna gazawar gwamnatin kasar, na kare rayuka da kuma dukiyoyin ‘yan kasar.

A saboda haka, akwai bukatar, a yiwa bangaren shari’a na kasar garanbawul, domin a lalubo da mafita kan lamarin.

Ko da yake dai, majalisar kasa na kan yunkurin sabunta dokar zabe ta 2022.

A matsayin mu a wannan Jaridar, mun kasance kan gaba wajen yin kira da a samar da sauye-sauye a bangaren shari’a, musamman domin a dawo da kimar da bangaren yake da shi, kamar yadda aka san shi, a shekarun baya.

A tunanin mu, samar da wannan sauye-sauyen a bangaren shari’ar, za a samar da kyakyawan yanayi a bangaren na shari’a, tare da gaggawar daukar makai, kan irin wannan kisan gillar da ake yiwa manyan kasar.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Mutane 7 Ne Suka Rasu Sakamakon Zazzabin Cizon Sauro Da Taifod Ba Wata Sabuwar Cuta Ba – Gwamnatin Kano
Ra'ayinmu

Buƙatar Daƙile Kutsen ‘Yan Bindiga Na Iyakokin Jihar Kano

November 28, 2025
Buƙatar Ɗaukar Matakin Gaggawa Na Daƙile Kutsen Ƙungiyar Ta’addanci Ta JNIM A Nijeriya
Ra'ayinmu

Buƙatar Ɗaukar Matakin Gaggawa Na Daƙile Kutsen Ƙungiyar Ta’addanci Ta JNIM A Nijeriya

November 21, 2025
Tinubu
Ra'ayinmu

Batun Yin Afuwa Ga ‘Yan Yankin Ogoni Huɗu

October 17, 2025
Next Post
Jiragen NAF Sun Kashe ‘Yan Ta’adda Da Lalata Baburansu 40 Da Bindigu 6 A Borno

Wasu Mahara Sun Sake Kashe Mutum 14 A Wani Kauyen Jihar Filato

LABARAI MASU NASABA

Tinubu

Dambarwar Naɗa Muƙamai Da Soke Su A Gwamnatin Tinubu

December 21, 2025
Zaben Fidda Gwani A APC: Sanatocin Jigawa Sun Rasa Tikitin Komawa Majalisa

APC Za Ta Gudanar Da Babban Taronta Na Kasa A Watan Maris

December 21, 2025
Mun Shirya Tsaf Domin Lashe Gasar AFCON Ta Bana – Bassey

Mun Shirya Tsaf Domin Lashe Gasar AFCON Ta Bana – Bassey

December 21, 2025
Sarakuna Na Da Rawar Takawa Wajen Kare Muhalli A Nijeriya – Ministan Muhalli

Sarakuna Na Da Rawar Takawa Wajen Kare Muhalli A Nijeriya – Ministan Muhalli

December 21, 2025
Me Ya Sa Ake Fifita Ilimin Boko A Kan Na Addini?

Me Ya Sa Ake Fifita Ilimin Boko A Kan Na Addini?

December 21, 2025
Yadda Itacen Dorawa Ke Warkar Da Cututtuka Daban-daban

Yadda Itacen Dorawa Ke Warkar Da Cututtuka Daban-daban

December 21, 2025
‘Yansanda Sun Kama Ɗan Bindiga Da Kuɗin Fansa Naira Miliyan 5 A Delta

An Cafke Wani Mutum Da Ya Lakada Wa Dansa Duka Har Lahira A Edo

December 21, 2025
Bambance-bambancenmu Shine Ƙarfinmu — Uba Sani

Bambance-bambancenmu Shine Ƙarfinmu — Uba Sani

December 21, 2025
Kotu Ta Fara Sauraren Korafe-korafen Dalibai A Kan Jami’ar MAAUN

Kotu Ta Fara Sauraren Korafe-korafen Dalibai A Kan Jami’ar MAAUN

December 21, 2025
Tinubu Ya Sauya Sunan Jami’ar Azare Don Karrama Sheikh Dahiru Usman Bauchi

Tinubu Ya Sauya Sunan Jami’ar Azare Don Karrama Sheikh Dahiru Usman Bauchi

December 20, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.