Leadership News Hausa
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership News Hausa
No Result
View All Result

Bukatar Mu Fahimci Masu Matsalolin Kwakwalwa Don Taimaka Mu Su

by
2 years ago
in SHARHI
4 min read
Bukatar Mu Fahimci Masu Matsalolin Kwakwalwa Don Taimaka Mu Su
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram
ADVERTISEMENT

Ranar 10 ga watan Oktoba rana ce da aka ayyana domin bikin ranar masu fama da matsalolin da suka jibinci lafiyar Kwakwalwa ta duniya (tabin hankali) da makamancinsa wato Mental Health a turance.

Tun da daga lokacin da aka fara bikin ranar masu fama da matsalolin lafiyar Kwakwalwa ta duniya a shekarar 1993, ko wace shekara akan ayyana wani take domin alamta wannan rana. An yi amfani da take kamar su Ciwon bacin rai (wato depression), da kisan kai-da-kai(wato suicide) ciwon hauka na schizophrenia da kuma rayuwa da wadannan matsalolin kwakwalwa, da dai sauransu.
Taken bikin na wannan shekarar shine ‘karin zuba jari domin kula da masu fama da matsalar lafiyar Kwakwalwa.’
Kamar a sauran bangarorin duniya, a nahiyar Afirka ma, masamman a Nijeriya, ana bukatar karin yunkuri don zuba jari akan masu fama da matsalar lafiyar Kwakwalwa; gwamnatoci a dukkan matakai da kuma daidaikun jama’a muna da muhimmiyar rawar da za mu taka domin shawo kan kalubalen matsalar lafiyar Kwakwalwa. daya daga cikin mafi mahimmancin abu shine bukatar dake akwai na mu fahimci masu fama da matsalar, hakan zai taimaka sosai wajen inganta lafiyar da kuma fahimtar masu fama da matsalar lafiyar Kwakwalwa .
Al’ummar mu ta yi wa matsalar lafiyar Kwakwalwa gurguwar fahimta, ta yadda idan mutum yana fama a matsalar kwakwalwa shi kenan ya zama abin kyama ko nuna sa a matsayin muhaukaci kai tsaye, wani lokacin har a gurin ‘yan uwansa; wasu lokutan kuma mu kan ma yarda masu matsalanr abin dariya, muna kara shashatar da su, wanda hakan ya kan kara munana matsalar ta Kwakwalwa su. Wannan ya sa mutane da yawa suna fama da matsalolin lafiyar Kwakwalwa amma suna tsoron su fada ko kuma su nemi taimako a wurin malam lafiya. Saboda haka akwai bukatar mu gyara fahimtar mu dangane da lafiyar kwakwalwa.

Tarihin Matsalar Lafiyar kwakwalwa:
Kafin zuwan likitanci mai amfani da kimiyya, an tafi akan cewa dukkan matsalolin kwakwalwa su na da alaka da miyagun aljanu ne. Saboda da haka da zarar mutum ya yi dabi’a wacce ta saba wa hankali sai a ce mutanen boye ne su ka shafe shi.
Yawanci maganin matsalar Kwakwalwa a wancan lokacin ya shafi kiran mutanen boye da yin surkulle, don su rabu da mutumin da ya ke fama da matsalar.
Malamin Falsafa Hippocrates (wanda masana tarihi suka hakkake cewa an haifeshi a shekaran 460 kafin Annanbi Isa Alayhis salam), shine mutumin da a tarihin likitanci na zamani ya fara fito wo fili, a cikin rubuce-rubucensa, ya soki ikirarin cewa mutanen boye ne suke jawo dukkan matsalolin kwakwalwa.
Hippocrates ya yi ikirarin cewa matsalolin lafiyar Kwakwalwa suna da alaka da tsarin halittar jiki, inda ya ambaci wasu sinadaran jiki guda uku, ciki har da yawu da kaki, a matsayin su ne su ke jawo matsalar Kwakwalwa.
Duk da cewa masana a bangaren likitanci sun zo sun yi watsi da wannan ikirarin na Hippocrates a kan abubuwan da suke jawo matsalar lafiyar Kwakwalwa, sun yarda da abin da ya fada cewa matsalolin lafiyar kwakwalwa su kan samu nasaba da tsarin halitta da kuma yadda jiki ya ke aiki (wato biological causes).
Malamai a bagarorin Kwakwalwa (Psychology) sun zo da wasu hanyoyi daban-daban wajen fahimtar matsalolin lafiyar Kwakwalwa.
Masana Kwakwalwar dan adam kamar su Sigmund Freud, Alfred Adler, Carl Jung da sauransu, sun bayyana abubuwan da suke ganin su suke jawo matsalolin lafiyar Kwakwalwa. Da yawa daga cikin masana, sun yi amanna cewa matsalolin lafiyar Kwakwalwa suna samuwa sakamakon nakasar aikin wani bangare na jiki, kamar jini ya daina zuwa wani bangare na kwakwalwa (a misali).
Wani bangare na malaman Kwakwalwar dan Adam yana ganin matsalolin lafiyar Kwakwalwa suna faruwa ne sakamako cakuduwa na masarrafar tunanin Dan Adam (wannan ita ce mahangar psychodynamic); wasu kuma suna ganin cewa dabi’un da ba sa kan hankali koyansu ake yi, kamar sauran halayya; Akwai kuma masu ganin cewa mutanen dake fama da matsalolin lafiyar Kwakwalwa tun farko ba su samu kulawa wacce bata nema sakayya ba ne, ma’ana ba a nuna mu su so da kauna ba tare da an nemi lada ko sakayya daga wurinsu ba da dai sauransu.
A zamanin yau, matsalolin lafiyar Kwakwalwa ana magance sune ta hanyar likitanci da kuma tattaunawar gyaran kwakwale (wato psychotherapy); za mu iya cewa dukkan matsalolin lafiyar kwakwalwa a na iya magance su ko kuma a rage bayyanar su ta yadda mai fama da su zai rayu kamar sauran jama’a.

Labarai Masu Nasaba

Matsalar Tsaron Jihar Kaduna: Yadda Al’amura Ke Kara Dagulewa

Ko Babban Taron APC Da Na PDP Danjuma Ne Da Danjummai?

Bukatar Sauyin Fahimta Kan Matsalolin Hankali:
Al’ummarmu tana bukatar ta sauya yadda ta fahimci lafiyar Kwakwalwa da irin tarnakin da ke addabar kwakwale.
Ya na da kyau mu fahimci cewa lafiyar Kwakwalwa kamar lafiyar sauran bangaren jiki take; kamar yadda mutum zai nemi lafiyar jiki idan ba shi da lafiya, haka zai nemi magani idan yasamu matsalar Kwakwalwa.
Matsalolin lafiyar kwakwalwa da dama ba sa farawa lokaci daya, yawanci a hankali suke farawa har su kai yadda za su hana rayuwa gudana. Wasu daga cikin matsalolin kwakwalwa ba sai an je asibiti ba, kamar su matsalolin dabi’a (wato conduct disorder), wasu daga cikin matsalolin tsoro (phobia), da zullumi (wato andiety), matsalolin rashin maida hankali da rashin nutsuwa (wato attention deficit hyperactibity disorder) wanda yawanci ya fi damun yara, da sauran su (wata rana zamu yi magana akan su daya bayan daya).
Wasu matsalolin kuma suna bukatar zuwa asibitin kwakwalwa ko kuma gamayya tsakanin asibiti da kuma tattaunawar gyaran kwakwale (psychotherapy). Don mutum ya je asibitin kwakwalwa (psychiatric hospital) baya nufin shi kenan ya zama abin kyama ko nunawa a din ga zance ko a daukeshi mahaukaci. Mu nuna tausayawa da kulawa, wannan shine mutumtaka.
Mai fama da matsalolin lafiyar Kwakwalwa zai iya samun lafiya, ya koma kamar yadda yake da can, kamar yadda mai fama da zazzabi ko mura zai iya samun lafiya.
Ya zama wajibi mu kawar da kyama da ake nunawa masu fama da matsalolin kwakwalwa. Yana da kyau mu karfafe su, mu mutunta su, domin suma mutane ne kamar kowa. Akwai bukatar karin wayar da kai dangane da lafiyar hankali, kuma akwai bukatar gwamnatoci da sauran jama’a su zuba jari don gani an inganta lafiyar Kwakwalwa a duniya baki daya, kamar yadda ake zuba jari don gani an inganta lafiya a sauran bangarorin lafiyar dam Adam.

Malam Khalid ya rubuto ne daga Jihar Gombe. A na iya riskar sa ta 08064268513 ko Khalidnera@gmail.com.

Like this:

Like Loading...
SendShareTweetShare
Previous Post

Kasafin 2021: Gwamnatin Tarayya Za Ta Biya ’Yan Kwangila Biliyan N15

Next Post

Gwamnati Ta Kara Wa’adin Amfani Da Sabon Farashin Lantarki Da Mako Daya

Labarai Masu Nasaba

Matsalar Tsaron

Matsalar Tsaron Jihar Kaduna: Yadda Al’amura Ke Kara Dagulewa

by Bello Hamza and Shehu Yahya
1 month ago
0

...

Taron

Ko Babban Taron APC Da Na PDP Danjuma Ne Da Danjummai?

by Bello Hamza and Idris Aliyu Daudawa
2 months ago
0

...

Masoya

Bikin Ranar Masoya Ta Duniya A Mizani

by
3 months ago
0

...

Noman Rogo

Kokarin CBN Wajen Sake Farfado Da Noman Rogo A Nijeriya

by
3 months ago
0

...

Next Post
Sabon Farashin Lantarki

Gwamnati Ta Kara Wa’adin Amfani Da Sabon Farashin Lantarki Da Mako Daya

Domin bayar da talla ko neman ƙarin bayani a tuntuɓe mu a: +2348039216372

  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us | English Edition | Fashion Magazine | Business News

© 2022 Leadership Media Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2022 Leadership Media Group .

%d bloggers like this: