• English
  • Business News
Wednesday, October 29, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Cacar Baki Ta Kaure Tsakanin Fadar Shugaban Kasa Da Peter Obi Kan Tallafin Mai

by Yusuf Shuaibu and Sulaiman
5 months ago
Peter obi

Cacar baki ta kauye tsakanin fadar shugaban kasa da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar LP a zaben 2023, Peter Obi, kan cire tallafin mai da manufofin canjin kudi na gwamnatin Shugaban kasa Bola Tinubu.

Obi ya nuna cewa duka tsare-tsaren gwamnatin Tinubu ta aiwatar da su ne ba tare da tsari ba, wanda jefa kasar cikin rikicin tattalin arziki, yayin da fadar shugaban kasar ta zargi Obi da cewa yana da sha’awar samun shugabanci ko ta halin kaka ba tare da ya fahimci yadda ake gudanar da gwamnati ba.

  • Bin Hanya Daya Da Aiwatar Da Matsayar Da Aka Cimma Muhimmin Mataki Ne Na Ba Da Tabbaci Ga Huldar Ciniki Da Tattalin Arzikin Sin Da Amurka
  • Kamfanonin Waje Sun Ce Dole Ne Su Shiga A Dama Da Su A Cikin Kasuwar Kasar Sin

Ko da yake tsohon gwamnan Jihar Anambra ya yarda cewa cire tallafin mai ya zama dole, amma duk da haka, ya yi jayayya da yadda aka aiwatar da shi.

Ya kuma bukaci gwamnatin Tinubu ta bayar da rahoton kudi da aka tara har zuwa yanzu daga lokacin da ta cire tallafin, sannan kuma ta nuna shaida game da kashe kudin da ta yi kan abubuwan more rayuwa kamar ilimi, kiwon lafiyar da rage talauci, kamar yadda ta yi ikirarin.

Idan za a iya tuna dai, Shugaba Tinubu ya sanar da cire tallafin man fetur da sauye harkokin canjin kudin kasashen waje a ranar 29 ga Mayu 2023, wanda ya haddasa matsalar tattalin arziki da kasar ke fuskanta, musamman dangane da hauhawar farashi da rage darajar naira.

LABARAI MASU NASABA

Manyan Kalubalen Da Sabon Shugaban INEC Zai Fuskanta

2027: Peter Obi Ya Shiga Rudani Kan Jam’iyyar Da Zai Tsaya Takara

A wata hira tare da gidan talabijin na Arise, Obi ya ce duk da cewa cire tallafin mai yana da muhimmanci, amma ya kamata a aiwatar da wannan tsari cikin tsari.

Ya ce ya amince cewa tallafin mai yana cike da ta’asa da cin hanci wanda akwai bukatar a kawo karshensa, amma ya yi suka ga hanyoyin da gwamnatin Tinubu take bi, yana bayyana su a matsayin wadanda aka yi ba bisa kwarewa ba.

Obi ya tambayi jagororin kula da kudin da aka ajiye daga cire tallafin, yana cewa, “Tun da aka ce manatallafin man fetur, ana cewa an cire ne saboda ba a so mu dunga ciyo bashi kuma kudaden za su ba da dama wajen zuba jari a muhimman ababen more rayuwa.

‘’Ina biliyoyin kudaden da aka tara? Ina aka zuba su a muhimman yankunan ci gaba? Kowa na sane da muhimman yankunan ci gaba da suka hada da ilimi, lafiya, da fitar da mutane daga talauci. Shin ko daya daga cikin wadannan abubuwan gda uku ya inganta? A’a.’’

Obi ya ce ya kamata a yi musayar farashi mai da masu ruwa da tsaki da kyau ta yadda zai rage tasirin ga matsalolin da ‘yan kasa ke ciki.

Da yake mayar da martini ga Obi, mai taimaka wa shugaban kasa kan batutuwan tsare-tsare, Daniel Bwala, ya bayyana dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar LP a matsayin mutum mai son kansa wanda ba ya da ilimin warware al’amuran da suka shafi tattalin arziki da shugabanci.

Bwala, a cikin wata sanarwa da ya wallafa ta shafinsa na sada zumunta na Tuwita, ya bayyana cewa ya yi mamakin yadda Obi ya yarda da manufofin tattalin arzikin Shugaba Tinubu, musamman kan cire tallafin mai da hada-hadar kudaden waje, amma ya jaddada cewa Obi sauran manyan ‘yan adawa suna neman samun iko ne kawai ko ta wani hali a wannan lokaci.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Manyan Kalubalen Da Sabon Shugaban INEC Zai Fuskanta
Tambarin Dimokuradiyya

Manyan Kalubalen Da Sabon Shugaban INEC Zai Fuskanta

October 17, 2025
peter
Tambarin Dimokuradiyya

2027: Peter Obi Ya Shiga Rudani Kan Jam’iyyar Da Zai Tsaya Takara

October 17, 2025
peter
Tambarin Dimokuradiyya

Peter Obi Ya Bukaci INEC Ta Tabbatar Da Shaidar Karatun Dan Takara Kafin Shiga Zabe

October 10, 2025
Next Post
Wani Gidan Gona A Jihar Ogun Zai Fitar Da Tarwada Ta Kimanin Naira Biliyan Shida A 2025

Wani Gidan Gona A Jihar Ogun Zai Fitar Da Tarwada Ta Kimanin Naira Biliyan Shida A 2025

LABARAI MASU NASABA

Binciken ‘Yan Sanda Kan Wanda Ake Zargi Da Tawayen “‘Yancin Kan Taiwan” Mataki Ne Na Adalci Don Kare Hadin Kan Kasa

Binciken ‘Yan Sanda Kan Wanda Ake Zargi Da Tawayen “‘Yancin Kan Taiwan” Mataki Ne Na Adalci Don Kare Hadin Kan Kasa

October 29, 2025
Afuwar Tinubu Ga Fursunoni: Saura Ƙasa Da Shekaru 6 Maryam Sanda Ta Shaƙi Iskar ‘Yanci

Afuwar Tinubu Ga Fursunoni: Saura Ƙasa Da Shekaru 6 Maryam Sanda Ta Shaƙi Iskar ‘Yanci

October 29, 2025
Xi Jinping Zai Gana Da Donald Trump

Xi Jinping Zai Gana Da Donald Trump

October 29, 2025
Gwamnatin Rikon Kwarya: Shirin DSS Ne Na Damke Atiku Da Peter Obi Kafin Rantsar Da Tinubu

DSS Ta Kama Wani Matashi Da Ya Yi Kira A Yi Juyin Mulki A Kafofin Sada Zumunta

October 29, 2025
An Kashe Ɗan Sanda Da Ɗan Hakimi A Rikicin Manoma Da Makiyaya A Gombe

An Kashe Ɗan Sanda Da Ɗan Hakimi A Rikicin Manoma Da Makiyaya A Gombe

October 29, 2025
Ribadu Ya Gargaɗi ‘Yan Siyasa Kan Tayar Da Hankali A Zaɓen Anambra

Ribadu Ya Gargaɗi ‘Yan Siyasa Kan Tayar Da Hankali A Zaɓen Anambra

October 29, 2025
ADC Ta Gargaɗi Gwamnatin Tarayya Kan Amfani da Zargin Juyin Mulki Wajen Yaƙar ‘Yan Adawa

Ba Matakan Tinubu Ne Suka Karyar Da Farashin Kayan Abinci Ba – ADC

October 29, 2025
‘Yan Ta’adda Sun Yi Barazanar Sanya Wa Majalisa Bam – Ɗan Majalisa

‘Yan Ta’adda Sun Yi Barazanar Sanya Wa Majalisa Bam – Ɗan Majalisa

October 29, 2025
Sanusi Ga ‘Yan Nijeriya: Ku Dora Wa Buhari Alhakin Matsatsin Tattalin Arziki Ba Tinubu Ba

Tsoron Boko Haram Ne Ya Sa Jonathan Ya Fasa Cire Tallafin Man Fetur – Sanusi II

October 29, 2025
Firaministan Sin Ya Yi Kira Da A Kara Bude Kofa Da Karfafa Daidaita Dabarun Samar Da Ci Gaba

Firaministan Sin Ya Yi Kira Da A Kara Bude Kofa Da Karfafa Daidaita Dabarun Samar Da Ci Gaba

October 28, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.