Gwamna Bello Matawalle na Jihar Zamfara, ya ce shi da takwarorinsa sun kai Gwamnatin Tarayya gaban kotun koli ne domin ceto tattalin arzikin kasar nan daga durkushewa.
Kamfanin Dillancin Labarai (NAN), ya bayar da rahoton cewa, gwamnoni uku na jihohin Kaduna, Kogi da Zamfara sun maka gwamnatin tarayya a kotun koli, inda suke neman ta dakatar da shirin sauya fasalin Naira na Babban Bankin Nijeriya (CBN).
- Mata Na Da Rawar Da Za Su Taka Wajen Ci Gaban Al’umma Idan Aka Ba Su Dama – Maryam Abacha
- Da ɗumi-ɗuminsa: Mataimakin Gwamnan Sakkwato Ya Koma APC
NAN ya kuma ruwaito cewa a ranar Laraba ne kotun koli ta dakatar da CBN daga aiwatar da wa’adin ranar 10 ga watan Fabrairu na daina amfani tsofaffin takardun kudi.
Wata sanarwa da aka fitar a Gusau a ranar Alhamis, ta hannun mai ba shi shawara ta musamman kan wayar da kan jama’a da yada labarai da sadarwa, Malam Zailani Bappa, ta ce wadanda suka yi adawa da matakin da suka dauka da nasarar da suka samu a kotun koli sun yi kuskure.
“Bayan kalaman rashin gaskiya da ke biyo bayan hukuncin da Kotun Koli ta kasa ta yanke na saurare da kuma aiwatar da bukatar gwamnonin da suka yi nasara a kan musayar Naira, Matawalle ya bayyana ra’ayinsu a matsayin siyasa kawai.
“Na tabbata cewa wadanda suka yi adawa da matakin da muka dauka na Kotun Koli ko dai sun rude ne ko kuma sun makantar da su saboda son zuciya.
“Ni da takwarorina na jihohin Kaduna da Kogi mun ga ya dace mu tunkari kotun koli domin ceto tattalin arzikin Nijeriya daga fadawa cikin mawuyacin hali.
“Kuma don kawar da radadin da talakawan Nijeriya ke fama da shi ta fuskar karancin kudi na tsofaffi da sabbin kudin Naira,” in ji Matawalle.
A cewarsa, yana da kyau a ce dole ne CBN da bankunan kasuwanci su samar da sabbin takardun Naira domin gudanar da harkokin kasuwanci na yau da kullum kafin a ayyana daina amfani da tsofaffin takardun kudi.
Gwamnan ya nuna rashin jin dadinsa da kalaman abokan hamayyarsa na siyasa, inda ya kara da cewa jam’iyyun siyasar da ke kalubalantar hukuncin kotun ba su da muradin kasar nan a zuciya.
“Hukuncin da alkalan kotun koli masu hikima da mutuntawa suka yanke kan wannan lamari, ita ce hanya mafi dacewa don magance matsalar da ake fama da ita da kuma sakamakon da ke tafe a halin yanzu.”
Matawalle ya kara da cewa, “A wannan mawuyacin lokaci na mika mulki, kishin kasa ne kawai ke gabanmu, mu ajiye tunanin siyasa a gefe tare da magance kalubalen da ke gabanmu.”