Babban Bankin Nijeriya CBN, ya sake bayar da wani dauki a Kasuwar hada-hadar musayar kudade, bisa nufin samar da sauki wajen samun kudaden cikin kasar.
Hakan ya sanya Bankin, ya saywar da dala miliyan hamsin, ga dilolin da aka yarjewa yin hada-hadar musayar kudade a cikin kasar.
- Allah Ya Bai Wa Annabi (SAW) Mu’ujizozi Fiye Da 2,000 A Alƙur’ani
- Tawagar Atiku Ta Isa Bauchi Don Halartar Jana’izar Sheikh Dahiru Bauchi
CBN ya yi hakan ne domin a tabbatar da samar masu da kudaden musayar masu yawa.
Kazalika, Bankin ya yi hakan ne, domin samar da daidaito, wajen yin hada-hadar musayar kudaden
Naira dai, ta fara fuskantar tarnaki ne, biyo bayan samun raguwar ta kasuwar hada-hadar musayar kudade, inda kuma matukar bukatar dalar, ya kara karuwa.
Bugu da kari, makon da ya gabata, daga tsakanin ranar Litinin zuwa ranar Laraba, an yi musayar dala kan 1,447.7089.
Amma kudaden musaya na cikin gida, farashin su ya ragu zuwa 1,455.5981, inda daga baya suka kai 1,460.5000, inda kafin a rufe kasuwar, suka kulle kan dala 1,455.
Tun bayan da Naira ta samu farfadowa, Bankin na CBN, ya samu sauki kan hada-hadar musayar kudaden da aka yi.
Sai dai, Bankin na CBN ya tura dala miliyan hamsin musamman domin dollin da aka yarjewa, su samu kudaden da yin hada-hadar da dama.














