Alkaluman da hukumomin kasar Sin suka gabatar a jiya Juma’a sun nuna cewa, darajar kayayyakin da aka shigar da su kasar Sin, da wadanda aka fitar daga kasar zuwa ketare, a watanni 7 na farkon bana, ta kai kudin Sin Yuan triliyan 30.13, jimillar da ta karu da kaso 17.3 bisa ta makamancin lokacin a bara. Kana a cikin kayayyakin da aka yi cinikinsu, darajar kayayyakin da aka fitar da su daga kasar Sin zuwa kasuwannin ketare ta karu da kaso 14, yayin da darajar kayan da kasar ta shigo da su daga sauran kasashe ta karu da kaso 22, a bisa jimillar bara.
Haka zalika, idan an duba jimillar watan Yuli, za a ga karuwar kudin kayayyaki masu kunshe da fasahohin zamani, da kasar Sin ta fitar da su zuwa kasashen waje, ta zarce kaso 50, jimillar da ta kai kusan kaso 60 a cikin karuwar dukkan nau’ikan kayayyakin da aka fitar daga Sin zuwa ketare.
A ganin kafofin yada labaru na kasashe daban daban, bisa la’akari da yanayin tafiyar hawainiya da dimbin kasashe ke fuskanta a bangaren cinikayya, nasarar da kasar Sin ta samu a wannan bangare ta fi yadda aka zata a baya, kuma ta nuna jajircewar kasar ta fuskar raya tattalin arzikinta, musamman ma a fannin tattalin arziki mai nasaba da sabbin fasahohi, ciki har da fasahar kirkirarriyar basira ta AI.
A ganin shehun malami mai nazarin ilimin tattalin arziki a jami’ar Renmin ta kasar Sin, Wang Xiaosong, dalilin da ya sa kasar Sin samun nasara a fannin ciniki da kasashen waje, shi ne domin yadda kasar ta mallaki cikakken tsarin masana’antu mai inganci, wanda ya ba ta damar samar da dimbin kayayyaki masu daraja, da sanya ta samun bukatar shigar da kaya daga ketare, ta yadda aka aza tushe mai karfi ga ci gaban bangaren cinikayya.
A sa’i daya kuma, dimbin al’umma da ake samu a kasar Sin, da kokarinta na kirkiro sabbin fasahohi, da manufarta ta kara bude kofa ga kasashen waje, dukkansu na samar da gudunmowa ga ci gaban bangaren ciniki a kasar.Ta hanyar tantance sakamako mai gamsarwa da kasar Sin ta samu a fannin ciniki a watanni 7 da suka gabata, kasashe daban daban sun kara fahimtar yanayi mai inganci da kasar ke ciki ta fuskar raya tattalin arziki.
Sa’an nan a watanni masu zuwa, za a shirya dimbin manyan bukukuwa na ciniki da kasuwanci a kasar Sin, irinsu CIFTIS, da CIIE, da dai sauransu, ta wannan hanya kasar za ta samar da karin damammaki na hadin gwiwa da raya tattalin arziki ga sauran kasashe. (Bello Wang)














