ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, September 10, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

2027: Shugaba Mai Gaskiya Da Hangen Nesa Nijeriya Ke Buƙata —Ahmad Shu’aibu

by Sulaiman and Bello Hamza
1 month ago
Nijeriya

A wannan tattaunawar da wakilinmu Muhammad Baƙir Bello ya yi da Ahmad Shu’aibu Isa, shugaban wata ƙungiya mai fafutukar wayar da kan al’umma a kan harkokin siyasa, ya jawo hankain al’umma a kan irin shugaban da ya kamata su zaɓa da kuma yadda za su guji sayar da kuri’un su a zaɓen da ke tafe na 2027. Ga dai yadda hirar ta kasance.

Za mu so ka gabatar mana da kan ka.

Assalamu Alaikum. Sunana Ahmad Shu’aibu Isa, kuma ni ne Shugaban Tafiyar MIDA (Moɓement for Inclusiɓe Deɓelopment Alliance) ƙarƙashin ICRP (Initiatiɓe for Conciliation and Right Protection).

ADVERTISEMENT

Ganin harkokin siyasa na ƙara kankama a ƙasar nan, wanne irin shugaba kake fatan ya jagoranci Nijeriya?

A ra’ayina, Nijeriya tana buƙatar shugaba mai gaskiya, riƙon amana, adalci, da hangen nesa. Shugaban da zai fifita muradun ƙasa da jin daɗin al’umma fiye da nasa muradun kansa. Ya kasance mai iya magance matsalolin rashin tsaro, rashin aikin yi, talauci, da kuma ƙarfafa fannoni kamar ilimi, lafiya, noma, tattalin arziki da abubuwan more rayuwa. Haka kuma, ya zama shugaba mai haɗa kan al’umma ba tare da nuna bambanci na ƙabila, addini ko yanki ba.

LABARAI MASU NASABA

Dole Al’ummar Arewa Su Rungumi Hanyoyin Kasuwanci Na Zamani —Alfa Musa

Ba Mu Taba Biyan Kudin Fansa Ba Kuma Ba Za Mu Biya Ba – Kwamishinan Katsina

Wanne shawara kake da shi ga al’umma wajen cimma wannan burin?

Shawarata ga al’umma ita ce su yi amfani da ƙuri’arsu cikin hikima. Kada a zaɓi shugaba saboda son zuciya, kuɗi, ƙabila ko addini kawai. A duba cancanta, nagarta, tarihin aiki da irin mafitar da ɗan takara yake bayarwa ga matsalolin ƙasa. Idan muka zaɓi shugabanni bisa cancanta, za mu samu ingantacciyar shugabanci da ci gaba mai ɗorewa.

Mene ne shawarar ka ga ƴan siyasa wajen gudanar da yaƙin neman zaɓe mai tsafta tare da kauce wa kalaman ɓatanci?

Siyasa ba taƙaddama da gaba ba ce, hanya ce ta gabatar da manufofi da neman amincewar jama’a. Ina kira ga ƴan siyasa da su gudanar da yaƙin neman zaɓe cikin mutunci, su guji kalaman ɓatanci, ƙarya, tunzura jama’a da haddasa rikici. Su mayar da hankali wajen bayyana shirye-shiryensu da manufofinsu domin al’umma su tantance su cikin adalci.

Ko kana da saƙo na musamman ga al’umma?

Saƙona ga al’ummar Nijeriya shi ne mu kasance masu haɗin kai, zaman lafiya da kishin ƙasa. Mu kiyaye dokoki, mu mutunta ra’ayoyin juna, kuma mu zaɓi shugabanni bisa gaskiya da cancanta. Idan muka haɗa kai muka fifita muradun ƙasa, za mu gina Nijeriya mai adalci, ci gaba da wadata ga kowa.

Muna godiya

Na gode ƙwarai.

shugaba
Sulaiman
+ posts Bio
  • Sulaiman
    Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna
  • Sulaiman
    Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba
  • Sulaiman
    Xi Ya Aike Da Gaisuwa Albarkacin Ranar Malamai Yana Mai Kira Da A Samar Da Matasa Masu Hazaka Domin Kara Farfado Da Kasa
  • Sulaiman
    Renon Matasa A Kan Kyakkyawar Turba Ginshiki Ne Na Gina KasaBy
shugaba
Bello Hamza
+ posts Bio
  • Bello Hamza
    https://hausa.leadership.ng/author/bello-hamza/
    Jihar Kano Za Ta Amfana Matuka Da Gidauniyar Aliko Dangote – Masu Ruwa Da Tsaki
  • Bello Hamza
    https://hausa.leadership.ng/author/bello-hamza/
    An Nuna Damuwa Kan Sake Kamun Da DSS Ta Yi Wa Boɗejo Bayan Samun Belin EFCC
  • Bello Hamza
    https://hausa.leadership.ng/author/bello-hamza/
    Dole Al’ummar Arewa Su Rungumi Hanyoyin Kasuwanci Na Zamani —Alfa Musa
  • Bello Hamza
    https://hausa.leadership.ng/author/bello-hamza/
    Ba Mu Taba Biyan Kudin Fansa Ba Kuma Ba Za Mu Biya Ba – Kwamishinan Katsina

MASU ALAKA

Dole Al’ummar Arewa Su Rungumi Hanyoyin Kasuwanci Na Zamani —Alfa Musa
Tattaunawa

Dole Al’ummar Arewa Su Rungumi Hanyoyin Kasuwanci Na Zamani —Alfa Musa

August 28, 2026
Ba Mu Taba Biyan Kudin Fansa Ba Kuma Ba Za Mu Biya Ba – Kwamishinan Katsina
Tattaunawa

Ba Mu Taba Biyan Kudin Fansa Ba Kuma Ba Za Mu Biya Ba – Kwamishinan Katsina

August 20, 2026
Adadin Masu Amfani Da Intanet A Sin Ya Kai Sama Da Mutane Biliyan 1.12
Tattaunawa

Yadda Na Yi Amfani Da Intanet Wajen Bunƙasa Sana’ata —Fatima Mubaraka

August 8, 2026
Next Post
Kasar Sin Ta Yi Kira Da A Magance Raunata Bangaren Ilimi Na Kasar Sudan

Kasar Sin Ta Yi Kira Da A Magance Raunata Bangaren Ilimi Na Kasar Sudan

LABARAI MASU NASABA

Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna

Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna

September 9, 2026
An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

September 9, 2026
Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba

Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba

September 9, 2026
Xi Ya Aike Da Gaisuwa Albarkacin Ranar Malamai Yana Mai Kira Da A Samar Da Matasa Masu Hazaka Domin Kara Farfado Da Kasa

Xi Ya Aike Da Gaisuwa Albarkacin Ranar Malamai Yana Mai Kira Da A Samar Da Matasa Masu Hazaka Domin Kara Farfado Da Kasa

September 9, 2026
Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu

Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu

September 9, 2026
Renon Matasa A Kan Kyakkyawar Turba Ginshiki Ne Na Gina KasaBy

Renon Matasa A Kan Kyakkyawar Turba Ginshiki Ne Na Gina KasaBy

September 9, 2026
Bikin CIFTIS Zai Ingiza Bude Kofa A Kasar Sin

Bikin CIFTIS Zai Ingiza Bude Kofa A Kasar Sin

September 9, 2026
“Ajin Tashar Sararin Samaniya Na Hong Kong Da Macau” Ya Kara Wa Matasa Sha’awar Kimiyya Da Karfafa Kishin Kasa

“Ajin Tashar Sararin Samaniya Na Hong Kong Da Macau” Ya Kara Wa Matasa Sha’awar Kimiyya Da Karfafa Kishin Kasa

September 9, 2026
’Yansanda Sun Cafke Matar Da Ta Kwara Wa Maƙociyarta Tafasasshen Ruwan Zafi A Abuja

’Yansanda Sun Cafke Matar Da Ta Kwara Wa Maƙociyarta Tafasasshen Ruwan Zafi A Abuja

September 9, 2026
Taron Kolin Urumqi Ya Mayar Da Hankali Kan Kwarewar Shugabanci A Xinjiang Da Muhimmancinta Ga Duniya

Taron Kolin Urumqi Ya Mayar Da Hankali Kan Kwarewar Shugabanci A Xinjiang Da Muhimmancinta Ga Duniya

September 9, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.