Abubakar Abba" />

Cibiyar ‘Interfaith’ Ta Wayar Wa Da Mata Kai A Kaduna Kan Mahimmancin Dasa Itatuwa

An wayarwa da mata kai a jihar Kaduna a kan mahimmancin dasa itatuwa don mangance dumamar yanayi.

Taron ya guda ne a gonar Teku International and Agro Allied Serbice dake  a jihar ta Kaduna, inda mata da dama suka halarci taron na bitar.

A jawabin sa a gurin taron Darakta gudanar da bincike a cibiyar Interfaith dake a garin Kaduna Abdullahi Muhamad Sufi ya yi nuni da cewa, ya zama waji mahukunta a Nijeriya su tashi tsaye don kare dumamar yanayi, musamman idana akyi la’akari da yadda yadda Hamada ke zamowa barazana a wasu kasashen dake a cikin nahiyar Afirka.

Ya kuma yi kira ga matakan gwamnati uku da ake dasu a kasar nan, dasu mayar da hankali wajen wayar da kan alumma a kan mahimmancin kula da muhallan su don kare su daga barazanar dumamar yanayi.

Shima wani jami’i a cibiyar Fasto Joshua Kpyeng ya yi nuni da cea, Allah zai tambaye mu a kan rashin kula da muhallan mu.

Fasto Joshua Kpyeng ya kuma koka a kan yadda wasu masu yin farauta a  kasar nan suke kona dazuzzuka da kuma wasu masu sare bishiyoyi, inda ya yi nuni da cewa, hakan yana iya shafar muhalli da kuma shafar tattalin arzikin kasar nan.

Shima a nasa jawabin a gurin taron, Shugaban gonar ta Teku Alhaji Ibrahim Salisu ya yi nuni da cewa, gaonar sa tana wayar da kan alumma dake a cikin jihar ta hanyar yin amfani da Majami’u da kuma Masallatai yadda kowa zai kare muhallin sa.

Ya yi nuni da cewa, dukkan irin ni’imar da muke bukata a kasar nan, Allah ya bamu ita, amma abin takaici, mune da hannuwan mu muek janyowa kanmu gaurbatar  muhallan mu.

Ya kara da cewa, mata suna da gagarumar gudunmawar da zasu bayar wajen kare dumamar yanayi, musamman a nahiyar Afirka.

Exit mobile version