Babban ko’odineta a ofishin Majalisar Dinkin Duniya da ke Nijeriya, Mista Edward Kallon, ya yaba wa mabiya addinin Kirista da ke Tarayyar Nijeriya kan yadda suka kiyaye dokokin Korona a bikin Kirsimeti da sabuwar shekara ta 2021.
Ya ce, duk da cewa babu dadi a ce mutane sun gudanar da shagulgula a irin wadannan ranakun cikin takura, amma Majalisar Dinkin Duniya ta yi farin ciki da bin wannan dokar da Hukumar Lafiya ta Duniya ta fitar (WHO) dangane da yadda annobar cutar Korona ke yaduwa, kamar wutar daji.
Ya kara da cewa, hukumar kula da yaduwar cututtuka (NCDC) ta bayyana yadda cutar Korona ke kara yaduwa a Nijeriya, ta kuma bayyana dokokin da ya kamata a dauka a lokacin shagulgulan bikin ranar Kirsimeti tun daga ranakun 25 ga Dasamba, 2020, zuwa 1 ga Janairu, 2021.
Mista Kallon ya ce, ba a samu cunkoso a guraren majami’u ba, kuma da dama sun gudanar da ibadunsu a kebe, ba tare da tara cunkoson mutane ba.