Idris Aliyu Daudawa">
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home KIWON LAFIYA

Ciwon Hanta Ya Fi Cutar Kanjamau Nakasu A Jiki – Likita

by Idris Aliyu Daudawa
January 5, 2021
in KIWON LAFIYA
2 min read
Ciwon Hanta
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Dr. Bello Kumo likita ne da ke aiki da asibitin koyarwa na jami’ar Ahmadu Bello da ke Shika a Zaria, ya bayyana cewar Ciwon Hanta (Hepatitis B) ta fi Cutar Kanjamau yi wa jikin mutum lahani fiye da yadda ake tunani.

Dr. Kumo ya bayyana haka ne a taron wayar da kan mutane kan cutar Hapatitis B wanda Gidauniyar Kashim Ibrahim Fellows (KIF) ta shirya a garin Kaduna.

samndaads

Ya ce, wayar da kan mutane kan wannan cuta zai taimaka wajen samar musu da kariya daga kamuwa da cutar bayana nan kuma da hana yaduwarta.

“Mutane masu yawa da suka kamu da cutar ba su da masaniyar cewa su na dauke da ita. Bugu da kari kuma, ba su da masaniyar cewa wanda ke tare da su ka iya kamuwa da cutar balle har su iya neman magani, domin su ceci kansu ba. A dalilin haka mutane da dama ke mutuwa, yaduwar cutar ta ki ci ta ki cinyewa,” in ji shi.

Ya ce, hanyar samun kariya daga kamuwa da cutar shi ne idan mutane na yin gwajin cutar akai-akai da kuma yin rigakafi.

“Da zarar ka yi gwajin cutar kuma sakamakon ya nuna cewa baka dauke da ita kamata yayi mutum ya yi rigakafin cutar amma idan mutum na dauke da cutar sai ya gaggauta fara shan magani domin hana yaduwar cutar.

“Bayan haka da ya ke mika godiyarsa ga Gidauniyar KIF kan shirya wannan taro gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufa’i ya ce samun nasarar hana yaduwar cutar ya dogara ne ga irin goyan bayan da mutane za su bada,” in ji shi.

Ya kuma ce, kamata ya yi mutane su zo a hada hannu da gwamnati, domin ganin an samu nasarar hana yaduwar cutar.

Idan dai ba a manta ba a 2018 ne El-Rufa’i ya kafa gidauniyar ‘Kashim Ibrahim Fellows’, domin inganta rayuwar matasa a jihar yadda za su zama shugabanni na gari nan gaba.

A wannan shekar kungiyar KIF ta kebe mako daya daga ranar Litini zuwa juma’a domin inganta rayuwar mutane a jihar.

Bayan haka kuma gidauniyar zata horad da matasa sana’o’in hannu kamar gyaran kai na mata, aski da wayar wa mutane kai game da mahimmancin tsaftace jikin su kuma muhallinsu.

SendShareTweetShare
Previous Post

Kashi 75 Na Matan Nijeriya Na Shafa Man Canja Launin Fata – Bincike

Next Post

Mece Ce Matsalar Coutinho A Barcelona?

RelatedPosts

Hanyoyi Biyar Na Rage Kiba Ba Tare Da Fuskantar Wani Hadari Ba

Hanyoyi Biyar Na Rage Kiba Ba Tare Da Fuskantar Wani Hadari Ba

by Idris Aliyu Daudawa
9 hours ago
0

Abincin da ake samu ta jikin dabobbi ya kunshi wasu...

Dalilan Da Za Su Sa A Koma Amfani Da Cimakar ‘vegan Diet’

Dalilan Da Za Su Sa A Koma Amfani Da Cimakar ‘vegan Diet’

by Idris Aliyu Daudawa
9 hours ago
0

Wasu ‘yan shekaru kadan da basu dade da wucewa ba,...

Hawan Jini

Yadda Hawan Jini Yake

by Idris Aliyu Daudawa
1 day ago
0

Akwai wani ma’auni da ake amfani da shi wajen kula...

Next Post
Coutinho

Mece Ce Matsalar Coutinho A Barcelona?

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version