Umar Faruk Birnin-kebbi" />

Da Dimi-diminsa: ‘Yan Sanda Sun Cafke Dillalan Makamai A Kebbi

Daga Umar Faruk Birnin-Kebbi

Rundunar ‘yan sanda a Jihar Kebbi ta cafke wasu mutane uku da ake zargin dillalan makamai ne.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sanda, DSP Nafi’u Abubakar, shi ya bayyana hakan a wani taron manema labarai na gaggaawa da aka gudanar yau a ofishin rundunar da ke Birnin Kebbi.

DSP Abubakar ya bayyana cewa, rundunar ta kuma kama wani shahararren mai garkuwa da mutane a karamar hukumar Mulki ta Arewa.

Ya ce: “A ranar 27 ga watan Junairu na shekara ta 2021, ’yan sanda da ke aiki a ofishin shiyya, Birnin Yauri, yayin da suke kan sintiri a kan hanyar Malando zuwa Garin-Baka sun kama wani mutum mai suna Ibrahim Bulus, mai shekara 25 da haihuwa a duniya, dan asalin garin Dirin Daji, Karamar Hukumar Sakaba, bisa mallakar bindiga guda uku da aka kera su a nan gida.

“Mun kama bindigogin ganga biyu da kuma bindiga guda daya a cikin jakarsa.

“Inda ya bayyana mana cewa wasu mutane biyu ne suka bashi kwangilar sayo musu bindigogin da aka cafke shi da su, kan hakan ne jami’an rundunar yan sandan suka cafko wadannan mutanen biyu da ya bayyana.

“Lokacin da aka tambaye shi, bai iya ba da gamsassun bayanai game da bindigogin ba, don haka aka kama shi,” in ji jami’in hulda da jama’a na rundunar yan sandan.

Daga karshe ya ce: “Da zarar rundunar yan sanda ta kammala bincike za a gurfanar da su a kotu.”

Wakilinmu ya zanta da daya daga cikin wadanda ake zargi, wato Ibrahim Bulus. Inda ya bayyana cewa: “Na sayo wadannan bindigogin ne a Kasuwar Dirin Daji, a karamar hukumar Sakaba da ke jihar kebbi, a cikin kasuwa ake kasa bindigogin na sayar wa, a nan ne na sayo wadannan.”

Exit mobile version