Shugabannin jam’iyyar APC na gundumar Kashere da ke karamar hukumar Akko a Jihar Gombe, sun kori Sanata mai wakiltar Gombe ta tsakiya, Danjuma Goje, bisa zargin yi mata zagon kasa.
LEADERSHIP ta ruwaito cewa a kwanakin baya ne jam’iyyar a matakin Kashere ta kafa wani kwamiti da zai binciki zargin cin mutuncin jam’iyyar da tsohon gwamnan jihar, a lokacin zaben 2023 da aka kammala.
- Binani Ta Shigar Da Kara Kotu Kan Bukatar Ayyana Ta A Matsayin Wadda Ta Lashe Zabe
- Mutum 7 Sun Shiga Hannu Kan Kisan Direba A Ondo
Da yake jawabi ga manema labarai a garin Kashere, shugaban jam’iyyar APC na yankin, Tanimu Abdullahi, ya bayyana cewa jam’iyyar ta dauki matakin korar Goje baki daya ne bayan ta same shi da laifukan cin mutuncin jam’iyyar da rashin halartar taron yakin neman zaben jam’iyyar APC a Jihar Gombe wanda jam’iyyar ta kasa ta jagoranta.
Shugaban jam’iyyar APC na kasa Sanata Abdullahi Adamu, ya kara da cewa, ana kuma zargin Sanatan da kauracewa duk wani rangadin yakin neman zaben jam’iyyar a shiyyarsa.
“Kwamitin ya kuma tattauna kan zargin da ake yi wa Goje na yi wa jam’iyyun adawa aiki da ‘yan takararsu da nufin kawo cikas ga nasarar jam’iyyar APC a Jihar Gombe da ma Nijeriya baki daya.
Ya kara da cewa, “Bayan goyon baya ga ‘yan takarar jam’iyyar adawa ta hanyar karbar dan takarar gwamnan jihar na jam’iyyar NNPP da kuma dan takarar majalisar wakilai ta tarayya a jam’iyyar PDP Akko a gidansa tare da bayar da goyon baya ga jam’iyyarsa ta APC da sauran al’amura da dama.
Abdullahi ya ci gaba da cewa, wasu laifukan da Sanata Goje ya aikata sun hada da “kawo cikas ga gwamnatin APC a jihar da kuma daukar nauyin yakin neman zabe da nufin tunzura jama’a kan gwamnatin APC a jihar.
“Bayar da takamaiman umarni ga abokansa da jami’an tsaronsa da su ki yin aiki da manufar jam’iyyar APC a Jihar Gombe.