Aisha Seyoji" />

Dabarun Da Mata Za Su Yi Amfani Da Su Wajen Sana’a – Hajiya Halima Ummi

A yau, mun yi muku tsarabar tattaunawa da wata ‘yar kasuwa wacce za ta koyar da mata dabarun kasuwanci a saukake. Sannan cikin hikima da basira ta yi bayani kan tarihin yadda ta fara kasuwanci domin masu sha’awa su yi koyi da kuma fahimtar kansu idan za su fara. Ga bayananta dalla-dalla kamar haka:

Takaitaccen tarihinta…
Assalamu alaikum warahamatullahi ta’ala wa barakatuhu. Kamar yadda kuka ji sunana Hajiya Halima Ummi, an haife ni a unguwar Yakasai ta karamar Hukumar Birni da kewaye a 1978, na yi karatu primary, secondry sai aka yi min aure har na haifi Yara 6. Sai kuma na koma karatu na yi Diploma a bangaren Harsuna wato Linguistics, na karanci English Islamic Studies, yanzu haka kuma na dakatar da karatu na fi ga harkar kasuwanci. Ina da Yara 6 na aurar da daya, ita ma tana da Yara 3.

Lokacin da ta fara sana’a…
Gaskiya ni na fara sana’a tin Ina budurwa shekaru kusan 25 da suka wuce. Ina karkashin kulawar mahaifana duk kasancewar babu abinda na nema na rasa nakan yi meat pie ina siyarwa, Yara ‘Yan uwana nakan yi kunshi, ban dai na yarda na zauna ba kuma da haka na taso naga manyan yayyu na a gidan mu suna sana’a idan sun kawo Kaya muna karba Kan farashi muna siyarwa tofa shine har izuwa yanzu ban dena ba, ba na damuwa da sana’a, babbba ce ko karama ni kawai nakan duba me zan samu ko yaya ne a cikin ta. Misali kin ga yanzu haka Ina da shago har guda biyu, daya ina siyar da dangin sitturu kayan kwaliyya da sauran su takalma jakunkuna ire iren su daya kuma Ina saida Kayan kitchen da sauran Kaya bukatun gida dangin kayan gado labule da decorations. Ina odan Kaya daga China, Malesia da sauran kashashe. Amma hakan bai hana ni yin odan kayan hada turare daga Maiduguri na zauna na hada na siyar ba. Ina zama ni da yara mu hada kayan rabon biki wato sebuniers to a takaice dai ina iya cewa idan kina jin Ana cewa sana’a goma maganin mai gasa to na hada, ba ni iya zama.
A kaya ina saida : Atampa, Lace, Shadda, Material, Kayan Yara maza da mata, Takalma na Yara na Mata da Zama da na manya, Mayafai da duk abin da ya shafi sitturu da kayan kwalliya dangin mayuka turare da sauran su. Ina kuma saida kayan kitchen da kayan decorations na gida. Ina saida kayan mata magunguna. Ina da shago a cikin unguwar da nake da zama kofar ruwa.

Hajiya Halima

Dabarun da mata za su yi amfani da su wajen sana’a…
Dangane da wannan da aka ce ana so na yi magana a kan dabarun sana’o’i namu na mata, zan iya cewa mace tana iya fara sana’a ko da da Naira dubu daya ne, abin da ya sa na ce mace za ta iya fara sana’a da Naira dubu daya sabida akwai kananun sana’o’i wanda ake yin su da karamin jari ya zamana dai a ce kada mace ta ce za ta dogara da wani ta ce sai an yi mata, ita ba za ta nemi na kanta ba, yau a rayuwa ba mijinki ba ko mahaifinki ne ke da hali ko wani mulki ko wani mukami gaskiya ni dai a shawarce ina baki shawara ka da ki dogara da shi, ka da ki ta’allaka cewa sai dai a yi miki ke ba za ki nema ki yiwa kanki ba sabida duk zuciyar da ta dogara da sai dai a yi mata ita ba ta burin raya kanta la shakka za ta zama matacciyar ZUCIYA, don haka mata mutashi mu nemi na kanka don kuwa duk abin da za ki yi da kanki ya fi wanda za a yi miki.
Yana da ga cikin kananun sana’o’i da mace za ta iya yi da karamin jari za ki iya siyan Madara Ko da ta naira dari shidda ki siyi sukuri gwangwani daya wanda bai wuce naira dari da hamsim ba, ki yi alawar Madara ki yayyanka akalla za ki ci ribar dari biyu, kin ga a nan kin juya Naira dubu daya ta koma daira dubu daya da dari biyu.
Idan Kuma jarinki Mai Dan kauri ne kina iya saro Kaya irin su atampa, mayafi, yari da sarka, takalma da jaka ki dora musu riba ‘yar daidai misali, sabida neman albarka ki siyar. Amma ina bada shawara ga ‘Yan uwa Mata mu guji dora riba mai yawa sabida neman albarka a neman mu.
Sannan a bangaren bashi, gaskiya ba na yin ciniki na bashi domin kuwa yana daga cikin abin da yake kawo nakasu a cikin sana’oin mata, daga lokacin da aka cinye kudin a dalilin bashi sai ki ga kin koma kin rungume hannunki.
Ina so ki gane mace fa tana iya yin sana’a koda ba ta da jari Kuma mace tana iyawa ta hada wata sana’ar musamann masu karamar sana’a misali ina yin sana’ar siyar da alawar Madara ai zan iya hadawa da wata sana’ar irin tamu ta mata ta karfi ta gida kamar wanki, daka da sauran su, na gode wa Allah da ya sanya ina da rufin asari, amma ina ji a raina da a ce ina da bukatu na rayuwa ni da iyalina kuma ba ni da jari to gaskiya zan iya yin ko ma wacce irin sana’a mutukar ba ta sabawa shari’ar addinin musulinci ba don tsira da mutuncina ni da iyalina. Ni a ganina a neman halak babu kaskanci, don haka mata mu jajirce mu nemi na kanmu.

kokarin da take yi na taimaka wa ‘yan’uwanta mata a kan sana’a…
Maganar temako a bangaran sana’a Masha Allah mutum bai yabon kanshi amma dai na san ina ba da gudummawa musamman ta shawara ga ‘Yan uwa Mata sanannan nakan tallafa wa Mata na basu Kaya su siyar su ci riba su bani kudina, sanann nakan kafa karamin dashi nasa Mata marasa jari duk sati sai na hada kudin na bawa mutum daya, kayan dubu hamsim duk sati zan bawa mace daya a haka har dukkan matan da ke cikin dashin kowa ya sami kayan a matsayin jari domin nakan basu kayan a farashin sari daidai yadda ake ba da sari a kasuwa, wannan dashi ne na mata wanda duk sati mace zata dinga biya da dubu biyar-biyar har mu gama.

Shawara ga mata masu tsoron fara sana’a..
A bangaren masu tsoron sana’a ni a ganinana babu wani dalili da zai sa mutum mai hankali da tunani wanda yake mai basira wanda ya san cewa idan ya ji yunwa zai nemi abinci ya ci idan ya ji kishirwa zai bukaci ruwa ya sha. Idan ya tashi shiga cikin jama’a ya yi shiga ta kamala a ganshi fes, to ban ga wani dalili da zai sa ya ce Wai yana tsoron sana’a ba, illa iyaka zan duba na yi tunani wace sana’ar ce ta fi dacewa da ni wacce idan na yi ta ne zan samu cimma buri na dogaro da kaina kuma ba zan ba da bashin da zai sanya na kwana ciki ba.

Batun shigarta cikin kungiyoyi….
Ba na cikin wata kungiya amma a yanzu haka ina nan ina kokarin kafa wata kungiya ta temakon mata zawarawa da suke bukatar yin aure duba da yadda rayuwa ta yi tsada, mace-macen aure ya yi yawa, ana yawan samun sabani a tsakanin maurata har abin ya yi tsamari, ina so na kafa kungiya wacce za ta dinga ba da tallafi da shawarwari ga ‘yan uwa mata don rage musu radadi da takaicin zamantakewar rayuwa.

Batun hada sana’a da hidimar iyali…
Ina tafiyar da harkokina na gida da iyalina da Maigidana tare da kasuwancina; komi bisa tsari da kulawa.

kalubalen da take fuskanta a harkokinta na kasuwanci…
Ba ni da wani kalubale gaskiya bisa ga harkokin kasuwancina. Ina samun temako na tallafi da kuma na shawarwari daga Maigidana da ‘Yan uwana har ma da su yarana manyan ciki.

Exit mobile version