Sanata mai wakiltar mazabar Bauchi ta arewa, Sanata Adamu Bulkachuwa na Jam’iyyar APC mai mulki, ya bayyana dalilansu na yunkurin tsige gwamnatin shugaba Muhammad Buhari.
Daga cikin dalilan da ya bayyana a wata hira da yayi ta musamman da kamfanin labarai na BBC Hausa, yace, “Mun bi Dokar Kasa, wacce ta bamu dama mu bawa shugaban kasa damar samun cikakken ‘yan ci na shawo kan kalubalen tsaro, kuma mun ba shi kudade isassu.
“Tsarin mulki ya bamu dama, in munyi iyaka yin mu, to mu zauna mu gaya wa shugaban kasa Gaskiya, cewa ya gaza.
“Don haka, muka zauna muka tattauna, muka yanke shawarar mu ba wa shugaban kasa makonni 6 na tafiya hutun mu, akawo sauyi ga kalubalen tsaro kafin mu dawo, wanda Mun gode Allah mun fara ganin sauye-sauye a hedikwatar tsaro ta Jami’an soji.
“Duk Sanatoci sun yarda sai ‘yan kalilan da tsige shugaba Buhari bisa dokar kasa in ba a samu sauyi ba a fannin tsaron Kasar nan har muka dawo.”
Bulkachuwa yayin da yake amsa tambayar cewa, ko ‘yan Majalisa za su goyi bayansu Kan kudurinsu na tsige Shugaba Buhari? Sai ya amsa cewa “Ai, ‘yan Majalisa sun fi mu zafi”