Connect with us

Tauraruwa Mai Wutsiya

Dalilin Da Ya Sa Dan Shekara 23 Ya So Ya Bindige Iyayensa

Published

on

Ranar Laraba ce kotun majistare ta Kaduna ta yanke ma Musa Habila hukuncin zaman shekara daya a gidan kurkuku saboda ya sace motar maigidan shi.

Mai shekaru 26 Habila yana zaune ne a unguwar Rigasa Kaduna, ya amsa aikata laifin ne, inda ya ce, ya sayarwa Nura motar akan kudi Naira milyan 3 da dubu 500,000.

Bayan ya amince da aikata laifin satar mota majistare Mr Ibrahim Emmanuel, ya bayyana cewar kotun bata da wani mataki wanda ya wuce, ta yanke ma shi hukuncin zaman gidan yari.

Emmanuel ya ce, shi matakin da aka dauka zai zama darasi ne ga wadanda ke da niyyar yin haka nan gaba, bugu da kari kuma ala’amarin sata, yanzu abin yana neman zaman ruwan dare game duniya.

Amma duk da hakan y aba wanda ya aikata laifin shawarar cewar nan gaba, ya kasance wanda ke da hali mai kyau, saboda kotu ba zata yi wanisako sako ba, idan aka sake kawwo shi wurin.

Tun farko dai Sajen Chidi Leo, ya bayynawa kotu cewar Omoya Alonge wanda ke zama a Bictoria Island Lagos, shi ya kai rahoton zuwa Hukumar binciken diddike ta jihar wanda ya shafi aikata laifuka.

Leo ya kara bayanin cewar ita wadda aka aikatawa laifin ta dauke shi aiki a matsayin direban ta, ta kuma bashi dama da motarta Ledus Jeep.

Bugu da kari cikin watan Disamba 2017, Alonge sai ya gano cewar Habila ya gudu da motarta, zuwa wani wurin da ba wanda ya sani, duk kuma wani kokarin da ka yi a sami inda yake, ba a samu cimma sa’a ba.

Leo ya nuna  cewar ‘’ lopkacin da Alonge ya kai rahon al’amarin zuwa SCIID,  an gano Habila a garejin Mando Kaduna’’.

Mai gabatar da masu laifi ya bayyana cewar shi wanda ya aikata laifin bayan an yi ma shi wasu ‘yan tambayoyi, sai ya yi bayanin ya sayar da ita motar.

Leo ya bayyana cewar Habila ya fadawa ‘Yansanda cewar ya saida ma Nura Abdullahi motar akan kudi Naira milyan 3 da dubu 500,000.

Shi laifin da aka aikata kamar yadda ya ce, ya sabawa sashi na 271 na dokar Penal Code ta jihar Kaduna.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: