Shugaban Rukunin Kamfanonin Dangote, Alhaji Aliko Dangote, ya jinjinawa Hukumar Kula da Tashoshin Jiragen Ruwa ta Kasa NPA.
Dangote, ya yabawa NPA ne, bisa kokarinta na wanzar da tsarin Gwamnatin Tarayya na sayar da Danyen Mai da kuma Man Fetur, da sauran dangogin Man Fetur da ake tacewa a cikin gida Nijeriya, kan farashin Naira.
- Al’umma Na Kokawa Kan Tsadar Kayan Miya A Sassan Kasar Nan
- Wata Motar Tankar Mai Ta Kama Da Wuta Tare Da Kone Wasu Motoci A Ibadan, Jihar Oyo
A saboda hakan ne, Dangote, ya bayar da kyautar sabuwar motar Bas kirar Coaster, domin karfafawa kwamitin da zai aikin, guiwa, wanda a turance, ake kira da One-Stop-Shop.
A cikin wata wasika da Dangote ya rattabawa hannu, ya kuma bayar da tabbcin cewa, Kamfaninsa zai ci gaba da samar da hanyoyin da zai rinka taimakwa kwamntin, domin ya samu gudanar da aikin da aka dora masa, bisa umarnin Fadar Shugaban kasa.
“Mun ammana da cewa, wannan motar Bas din, kwamitin zai yi aiki da ita yadda ya kamata, duba da cewa, Kamfanin na, zai ci gaba da bai wa kwamtin goyon baya,” Inji Dangote.
Idan za a iya tunawa, Shugaban karamin kwamitin na wanzar da sayar da Danyen Man da kuma sauran dangogin Man Fetur da ake tacewa kasar kan farashin Naira Zacch Adedeji, ya jabawa hukumar ta NPA, bisa samar da aikin a cikin sauki
Adedeji, ya yi wannan yabon ne, lokacin da ya jagoranci tawagar kwamtin zuwa hukumar ta NPA, inda kuma ya yabawa tawagar kwamtin, da ke a karkashin NPA, kan gundunmawar da take ci gaba da bayar wa, domin a samu cimma burin da aka sanya a gaba.
“Mun lura da cewa, babu shakka wannan kokarin na hukumar ta NPA ya nuna irin kishin da hukumar take da shi a zahir, wajen cimma nasarar da aka sanya a gaba, “A cewar Adedeji.
“Ina mai kara maku kwarin guiwar cewa, kar ku gajiya wajen cimma burin da aka sanya a gaba, musamman domin a samu cin nasarar aikin, kuma muna mika godiyar mu, ga sauran hukumomin da suke ci gaba da bayar da goyon bayansu”. In ji shi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp