A ’yan watannin da su ka gabata, farashin Albasa ya tashi matuka, inda aka danganta hakan, musamman kan karancinta da kuma wasu abubuwa da su ka janyo hakan.
Sai dai kuma, a yanzu farashin na Albasar ya ragu saboda noman sabuwarta da aka yi a kakar noman bana.
Manomanta da dama sun danganta faduwar farashinta kan yawan girbinta da aka yi a jihohi da da ma da ke a kasar nan.
An ruwaito cewa, a yankin Kwalkwalawa da ya yi fice wajen nomanta, an ga manomanta da dama su na ta yin girbinta, inda kuma wasun su ke kan shirye-shiryen fara shuka wasu sabbin irin na Albasar.
Malam Buhari Malamawa ya kara da cewa, Albsar ta yi karanci ne saboda ambaliyar ruwan sama a wancan lokacin a wasu jihohin da ke kasar nan, inda ya ci gaba da cewa, a wancan lokacin ana sayar da buhunta daga naira 60,000 zuwa naira a 70,000, inda kuma wasu su ke sayar da buhunta daga naira 80,000 zuwa naira 90,000, amma a yanzu farashinta ya dan ragu ganin cewa, a cike wasu kananan kasuwanni da ita.
Shi ma wani mai sayar da Albasar a Kasuwan Dajin Kasuwan Dajin Malam Kasimu Malam Abdul Dajin ya sanar da cewa, Allah ne ya kaddara farashinta ya ragu.
Malam Kasimu ya ci gaba da cewa, farashinta ya tashi a wasu ‘yan watanni da su ka wuce, amma a yanzu, farashinta ya fadi, inda ya sanar da cewa, ba wai dabararmu ba ce, a saboda haka, mutane su dai na zarginmu kan cewa, mu ne muka kara farashinta domin a lokacin, babu wani abu da za mu iya yi.
A cewarsa, kafin zuwa yanzu, dan karamin kwandonta ana sayar da shi daga naira 6,000 zuwa naira 7,000, amma a yanzu, ana sayar da shi daga naira 3,000 da kuma zuwa naira 3,500.
Shi ma Sakataren kungiyar manoman Albasa Umar Usman Dandare ya sanar da cewa, akwai bukatar gwamnati ta daidaita farashin Albasa a duk yayin nomanta, inda ya kara da cewa, manoman Albasar ba sa samun wani dauki daga gun gwamnati
Umar Usman Dandare ya kuma yi kira ga gwamnatin tarayya ta sa manomanta a cikin shirin aikin noma na Anchor Borrowers, inda ya kara da cewa, masu da tsaki da sauransu suna kan kokarin tabbatar da ana sayar da Albasar da farashinta bai wuce kan naira 30,000 a jihar Sokoto da kewaye.
A jihar Kebbi kuwa, wani manomin Albasa Bala Aliero ya bayyana cewa, tun lokacin da aka fara yin girbinta a watan Disambar da ta wuce, farashinta ya fara sauka, inda ya kara da cewa, farashinta ya fadi ne saboda ta fara cike kasuwanni.
Shi ma wani dilan Albasa a jihar ta Kebbi Mallam Muhammadu, ya danganta faduwar farashin na Albasa kan cewa, wani abu ne da ba a saba gani ba, inda Mallam Muhammadu ya kara da cewa, a lokacin da farashinta ya fara sauka, haka kuma farashin na Albsar zai iya kara tashi.
Sai dai, a wani bincike da aka gudanar a wasu jihohi da kuma a garin Fatakwal da ke a cikin jihar Ribas ya nuna cewa, farashinta zai kara sauka nan da ‘yan kwanuka masu zuwa.