Babban sakataren kungiyar masu sarrafa Takin zamani da rabar da shi na kasa FEPSAN Mista Gideon Nagedu ya bukaci shugaban kasa Ahmed Bola Tinubu da ya yi bincike akan masana’antar samar da Takin zamani kan yadda ta kasance a shekaru bakwai da suka gabata.
Nagedu a wata hirarsa da manema labarai ya bayyana cewa, abinda muka bukata daga gun gwamnatin shugaba Tinibu shine ya yi bincike akan masana’antar samar da Takin zamani kan yadda ta kasance a shekaru bakwai da suka gabata.
- Hajjin Bana: NAHCON Ta Samar Da Biza 73,310, Tare Da Kai Alhazai 46,000 Kasar Saudiyya
- Zan Yi Aiki A Bayyane Tare Da Shugabannin Majalisa Ta 10 – Tinubu
Sai dai, sakataren ya yi nuni da cewa, idan zamu yiwa tsohuwar gwamnatin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari adalci, gwamnatin ta samar da gagaruwar ci gaba wajen habaka fannin samar da Takin zamani a kasar nan
Ya ci daga da cewa, a lokacin tsohuwar gwamnatin ta Buhari, an samar da Takin zamani da ya karu zuwa tan miliyan 1.6 wanda wannan ne ya kasance na karon farko a kasar nan.
“An samar da Takin zamani da ya karu zuwa tan miliyan 1.6 wanda wannan ne ya kasance na karon farko a kasar nan a lokacin tsohuwar gwamnatin Buhari.”
Nagedu ya kara da cewa, za ka iya gani da Idonka a karkashin shirin samarr da Takin zamani na fadar shugban kasa a lokacin tsohuwar gwamnatin ta Buhari, an samar da ci gaba matuka.
A cewarsa, a kungiyance, duk irin nasarar da tsohuwar gwamnatin ta Buhari ta samar a fannin aikin noma a kasar nan, muna kira ga shugaba Tinibu da ya dora kan sanar da gwamnatin baya ta samar a fannin.
“Duk irin nasarar da tsohuwar gwamnatin ta Buhari ta samar a fannin aikin noma a kasar nan, muna kira ga shugaba Tinibu da ya dora kan sanar da gwamnatin baya ta samar a fannin.”
Daya bangaren da muka bukatar gwamnatin ta Tinubu ta mayar da hankaili akai Sakataren ya sanar da cewa, muna kira ga Tinubu da ya mayar da hankali wajn bunkasa samar da kudaden musaya na ketare, inda hakan zai kara bai wa habaka fannin na aikin noma.
Ya bayyana cewa, daya bangaren da muka bukatar Tinubu ya mayar da hankali akai shine magance yadda wasu masu sarrafa Takin zamani ke gurbata shi, inda hakan ke janyo wa masu zuba jari a fannin da kuma manoma asara.
A cewarsa, matukara gwamnatin ta kawo karshen wannan matsalar, manoman kasar nan za su samu sukunin yin girbe amfanin gonakan su mai yawa.
“Muna bukatar shugaban kasa Tinubu ya mayar da hankali akai shi ne magance yadda wasu masu sarrafa Takin zamani ke gurbata shi, inda hakan ke janyo wa masu zuba jari a fannin da kuma manoma asara.”
A wani labarain kuwa, Manoman Albasa sunce sun yi asarar sama da Naira biliyan uku a duka shekara saboda rashin sarrafa ta yadda ya dace a cikin kasar nan.
Shugaban kungiyar manoman Albasa da sararrafa ta na kasa Isah Aliyu ya bayyana hakan, inda ya ce, Nijeriya na noma Albasa metric tan miliyan biyu na Albasa a duk shekara.inda hakan ya kai kimanin kashi 40 a cikin dari na jimlar Alabsar da ake nomawa a kasar.
“Nijeriya na noma Albasa metric tan miliyan biyu na Albasa a duk shekara.inda hakan ya kai kimanin kashi 40 a cikin dari na jimlar Alabsar da ake nomawa a kasar. “
Aliyu wanda ya sanar da hakan a taron kaddamar da kamfanin sarrafa Albasa da Tafarnuwa wanda ya kasance irinsa na farko a jihar Sokoto ya ci gaba da cewa, duk da cewa Nijeriya ta kasance kan gaba wajen noman Albasa da Tafarnuwa a duniya, amma ta kasance tana shigo da amfanin cikin kasar nan saboda rashin kayan da za a sarrafa wadannan amfanin biyu.
“Kasance irinsa na farko a jihar Sokoto ya ci gaba da cewa, duk da cewa Nijeriya ta kasance kan gaba wajen noman Albasa da Tafarnuwa a duniya, amma ta kasance tana shigo da amfanin cikin kasar nan saboda rashin kayan da za a sarrafa wadannan amfanin biyu.”
Shugaban ya kara da cewa, rashin kayan da za sarrafa amfanin biyu a kasar nan, na ci gaba da zamowa manoman da ke noma su, babban tarnaki.
A cewarsa,”Sama da metric tan miliyan biyu 2 na Albasa ake nomawa a kasar nan a duk shekara, inda jihar Sokoto ke noma kashi 40 a cikin dari.”