Abdulkadir Kurawa" />

Dalilin Fara Shekarar Musulunci Daga Al-Muharram maimakon Rabi’ul Auwal

Tambaya: Shin mene ne dalili da ya sa a ka fara kidayar shekarar Musulunci daga watan Muharram maimakon watan Rabi’ul Auwal, wanda  shi ne a ka yi hijira?

Amsa: An fara aiki da Shekarar Hijira ne bayan shudewar shekaru 17 da yin hijirar Sayyidina RasululLahi (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam), wato a zamanin halifancin Amirul-muminina Umar Bn al-Khaddab (Allah ya kara yarda da shi), inda a ka zabi watan al-Muharram ya zamo shi ne mafarin shekara, duk kuwa da cewa Sayyidina RasululLahi (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) ya isa garin Madina a Hijirarsa ne a watan Rabi’ul Awwal.

Dalilin da ya sanya hankali sahabbai ya juyo wajen samar da matsaya game da tsarin kalanda kuwa shi ne, Sayyiduna Abu Musa Al-Ash’ariy (Allah ya kara yarda da shi) ne ya aika wa Sayyiduna Umar da sakon cewa, “Wasiku masu yawa su na zuwa ma na daga gare ka, amma babu kwanan wata.” Alal misali, sai a ce abu kaza ya faru a watan Sha’aban ba tare da an bambance watan Sha’aban na wace shekara ba.

Hakan ya sanya Sayyiduna Umar (Allah ya kara yarda da shi) ya tara sahabbai domin duba wannan al’amari. A lokacin ne wasu su ka ce mu fara shekarar Musulunci daga lokacin da a ka aiko Sayyiduna RasululLahi (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam), wasu kuma su ka ce ya kamata a fara ne daga lokacin hijirarsa (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam).

Sai Sayyiduna Umar (Allah ya kara yarda da shi) ya zabi a fara daga Hijira, ya na mai cewa, “Hijira ce ta bambance tsakanin gaskiya da karya.” Da haka a ka zabi Hijira ta zamo farkon shekarar Musulunci.

Game da zaben watan da za a fara shekarar da shi kuwa, shi ma an sami shawarwari mabambanta. Wasu su ka nuna a fara daga watan Ramadhan, ta yiwu saboda kasancewarsa watan da a ka saukar da Alkur’ani mai girma. Sai dai an zabi watan al-Muharram ne kasancewarsa lokacin da mutane su ke kama hanyarsu ta koma wa gida daga aikin Hajji

Wasu kuma su ka ce dalili zaben al-Muharram shi ne kasancewarsa watan da Sayyidina RasululLahi (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) ya fara shirye-shiryen fita zuwa Hijira.

Al-Hafiz Ibn Hajar (Allah ya kara yarda da shi) ya bayyana cewa, an zaɓi wata al-Muharram ne a kan Rabi’ul Auwal, saboda a watan al-Muharram ne a ka fara azamar yin Hijira, domin mutanen Madina sun yi wa Sayyidina RasululLahi (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) mubaya’a ne a cikin watan Zul-Hajji. Wannan mubaya’ar ce ta share fage game da Hijira. Saboda haka sai a ka zabi al-Muharram.

Allah ne masani..

-An kwafo wannan ne daga Abdulkadir  Kurawa.

Exit mobile version