Dillalan Man Fetur da wasu masu ruwa da tsaki a fannin Mai da Iskar Gas da Man Dizil, a kasar nan, sun yi maraba da dakatar da biyan harajin kaso 15 a cikin dari na harajin shigo da Man daga ketare, zuwa cikin kasar.
Sun bayyana cewa, dakatarwar ta kamata har sai kasar nan, ta kai matakin da matatun Man a kasar, sun kai matakin iya samar da wadacaccen Man da sauransu a cikin kasar.
- Majalisar Wakilai Ta Nemi A Ɗauki Sabbin Ma’aikata A Jami’o’in Nijeriya
- Allah Ya Tsarkake Iyalan Annabi (SAW) Daga Kazanta
Wasu rahotannin sun sanar da cewa, Hukumar kula da harkokin man fetur ta kasa wato, NMDPRA ce, ta sanar da matakin dakatarwar.
Idan za a iya tunawa, ayyana karbar harajin shigo da kayan, ya tayar da ce-ce kuce a masana’antar ta sarrafa Man a kasar.
Sun bayyana cewa, shigo da kayan tamkar wani yunkuri ne, na durkusar da Matatar Mai ta Dangote, wacce ta kasance mafi girma a cikin kasar kuma wacce za ta iya samar da Man da zai wadaci kasar.
A cewarsu, Matatar ta Dangote, na karfin da za ta iya samar da Man Dizil Lita miliyan 25 a kullum, wadda kuma ta bayar da tabbacin cewa, za ta iya ci gaba da samar da Man da dangoginsa a daukacin fadin kasar.
Daya daga cikin dilalan Otunba Adetunji Oyebanji ya sanar da cewa, yana da yakinin cewa, Matatar ta Dangote, na da karfin da za ta iya samar da Man.
Shi kuwa wani Farfesa kan tattalin arzikin Mai Wumi Iledare ya bayyana cewa, dakatarwar da gwamnatin ta yi, siyasa kawai
Ya kara dakatarwar, za ta taimaka wajen ci gaba da dorewar matatun Mai da ke a cikin kasar nan.














