Sakamakon tallafa wa al’umma da jari da sauran ayyukan jin ƙai a dukkanin faɗin jihohin ƙasar nan, kula tare da haɓaka harkokin ilimi, fasaha da bai wa tsofaffi kulawa ta musamman da kuma taimako iri daban-daban, ya sa Sanata Oluremi Tinubu kasancewa a matsayin Gwarzuwar Shekarar 2025.
Sanata Oluremi Tinubu: Nuna Tausayi Ga Masu Ƙaramin Ƙarfi
Gwamna Hope Odidikanwa Uzodimma
- Tsarin mulkinsa, ya kawo sauye-sauye tare da dogaro a kan gaskiya, wanda hakan ya haɗa da inganta harkokin ilimi, ƙarfafa fasaha, sabunta kayan aiki da kuma sake fasalin tsaro; don sake fasalin hidimar jama’a a matsayin dandalin ci gaba da haɗin kai; An zabi Gwamna Hope Odidika Uzodimma Gwarzon Gwamnan Shekarar 2025.
Hope Uzodimma: Sake Gina Jihar Imo Da Hangen Nesa Da Jajircewa
- Gwamna Lawal Ya Gabatar da Kasafin Naira Biliyan 861 Na 2026 Ga Majalisar Dokokin Jihar Zamfara
- Xi Ya Jaddada Muhimmancin Inganta Hanyoyin Kula Da Tafiyar Da Intanet Na Dogon Zango
- A Hangen Nesansa wajen jagorancin al’umma, ya mayar da hankali kan masana’antu, sabunta ababen more rayuwa da kuma gina Ɗan’adam; domin mayar da Jihar Nasarawa matsayin wata babbar cibiyar zuba jari a Nijeriya da horar da aikin injiniya tare da kyautata jin daɗin al’ummar jihar; an zaɓi Injiniya Abdullahi A. Sule a matsayin Gwarzon Gwamnan Shekarar 2025.
Injiniya Abdullahi Sule: Wanda Ya Fi Yin Fice Kan Harkokin Masana’antu A Duk Faɗin Arewa
- Shugabancinsa ya yi matuƙar kawo sauye-sauye a Jihar Ekiti, musamman ta hanyar gudanar da mulki na adalci, sabunta ayyukan more rayuwa, ƙarfafa matasa da faɗaɗa aikin gona; sakamakon tawali’un da yake da shi da horon da ya samu wajen tafiyar harkokin kuɗi da gina jama’a tare kuma ƙarfafa al’adun demokuraɗiyya; ya sa aka zaɓi Biodun Abayomi Oyebanji a matsayin Gwarzon Gwamnan Shekarar 2025.
Biodun Abayomi Oyebanji: Wanda Ya Kawo Juyin-juya-hali A Jihar Ekiti
- A sauyin da ya kawo a shugabancinsa, jajircewarsa na kawo ci gaba a fannin tsaro, zuba jari mai yawan gaske a fannin ilimi, kiwon lafiya da sauran ababen more rayuwa; kazalika a ƙoƙarinsa na sake mayar da Jihar Zamfara kan turbar zaman lafiya da ci gaba mai ɗorewa, Dauda Lawal shi ne Gwarzon Gwamnanmu na wannan shekara.
Dauda Lawal: Ceto Zamfara Domin Ci Gaba
- Ya duƙufa wajen mayar da hankali kan manufar da ya sanya gaba, mai taken; “MORE Agenda”, wanda ya sake fasalin tsarin mulkin Jihar Delta ta hanyar zaman lafiya, haɗin kai da kuma jajircewa wajen samar da ababen more rayuwa, ilimi, lafiya da kuma gina al’adun jama’a bisa gaskiya, tsantseni a sha’anin harkar kuɗi ta ɓangarori da dama; Rt. Hon. Sheriff Oboreɓwori, shi ne gwarzon gwamnanmu na 2025.
Sheriff Oboreɓwori: Gwamnan Da Ya Ginu Kan Tabbatar Da Zaman Lafiya Da Ci Gaban Al’umma
- Saboda kasancewarsa mai sasanta mutane da haɗa kansu duk da bambance- bambancensu; ga kuma samar da abubuwan more rayuwa a ƙauyuka, farfaɗo da lamarin kula da lafiyar al’umma, taimaka wa manoma da matasa yadda za su tsaya da ƙafafunsu; tafiyar da gwamnati ta tausaya wa al’umma, yin biyayya da dokoki, da tunanin yadda gaba za ta yi kyau; shi ya sa aka zaɓi Sanata Uba Sani a matsayin Gwarzon Gwamnan shekarar 2025.
Sanata Uba Sani: Mai Haɗa Kan Al’ummar Da Suka Rarrabu
Gwarzon Ɗan Majalisa Na Shekarar 2025
- Saboda yadda ya shahara wajen yin doka, wakilci, nuna damuwa da sai abu ya kasance; yadda yake da hazaƙa, sa ido kan ci gaban inda yake wakilta, da ƙoƙarin samar da zaman lafiya, tsarin da ya sa aka samu cimma buri a gyaran tsarin mulki, haɗin kan ƙasa;. Honorabul Benjamin Okezie Kalu, PhD, CFR don haka shi ne ɗan majalisar shekarar 2025.
Benjamin Okezie Kalu: Wakili A Majalisa Saboda Haɗin Kan Ƙasa, Zaman Lafiya, Da Ci Gaba
Gwarzon Ma’aikacin Gwamnati Na Shekarar 2025
- Bisa la’akari da yadda ya tafiyar da sha’anin kawo gyara a lamarin tara haraji, abin da aka aiwatar ta yadda ya dace a yi da gaskiya domin haɓɓaka hanyoyin samun kuɗaɗen shiga ba ta hanyar man fetur ba, amma ta hanyar ɓullo da wasu dabaru ta kafar sadarwa ta zamani; da yake an ɗauki hukumomin gwamnati da su ma abokan tafiya ne domin samun ci gaba, ba tare da an sa wani abu na matsi ba; Dakta Zacch Adedeji a yanzu shi ne gwarzon ma’aikakaci na shekarar 2025.
Dakta Zacch Adedeji: Wanda Ya Ƙara Ɗaukaka Darajar Haraji A Nijeriya
Gwarzon Ɗan Kasuwa Na 2025
- Saboda hangen nesansa wajen kawo gyara a lamarin bunƙasa samar da takin zamani a Nijeriya da kuma harkar kasuwancin amfanin gona; don tallafa wa miliyoyin manoma hanyar amfani da abubuwan gida. Da kuma ƙoƙarinsa na samar da wata hanyar taimakawa masu ƙaramin ƙarfi yadda za su cimma burinsu na maida aikin gona a matsayin wata hanya da za ta taimaka wa al’umma; don haka Thomas Etuh shi ne gwarzon Ɗan kasuwa na shekarar 2025.
Thomas Etuh: Gwarzo Wajen Samar Da Hanyoyin Dogaro Da Kai Ga Matasa
Gwarzon Shugaban Kamfani Na Shekarar 2025
- Domin jagorantar ɓangaren haƙar mai da iskar gas na tekun Nijeriya da ya yi nasarar samar da ganga miliyan 1.8 na man fetur a kowace rana; da kuma jagorantar hukumar NUPRC ta zarce burinta na samun kuɗaɗen shiga da kashi 84.2 cikin ɗari, Injiniya Gbenga Komolafe shi ne Gwarzon Shugaban Kamfani na Shekara ta 2025.
Gbenga Olu Komolafe: Jagorantar Tsarin Samar Da Makamashi A Nijeriya
Gwarzon Ma’aikacin Banki Na Shekarar 2025
- Domin jagorantar harkar kuɗi ta hanyar ƙirƙire-ƙirƙire tare da ƙarfafa samar da ƙanana da matsakaitan sana’o’i (MSME) 700,000 da ƙarfafa tubalin tattalin arziƙin Nijeriya da kuma sake fasalta banki; an zaɓi Dakta Tony Okpanachi a matsayin Gwarzon Ma’aikacin Banki Na Shekarar 2025.
Dr Tony Okpanachi: Gina Makomar Nijeriya Ta Hanyar Tallafa Wa Ƙananan Kamfanoni
Wanda Da Ya Fi Tasiri A Kafofin Sada Zumunta Na Shekarar 2025
- Domin sauya rikici zuwa haɗin kai, da tashin hankali zuwa ci gaba mai ma’ana da ƙirƙirar ayyukan yi, samar da zaman lafiya da sabunta zamantakewa, al’adu da tattalin arziƙin Neja Delta da zuba jari a ilimi, kiwon lafiya, muhalli da ƙarfafa ci gaba, an zaɓi Babban Sarki Oweizide Ekpemupolo (Tompolo) a matsayin mafi tasiri a Kafofin Sada Zumunta na 2025.
Babban Sarki Oweizide Ekpemupolo (Tompolo): Hiddimta Wa Al’umma Ba Tare Da Gajiyawa Ba
Gwarzuwar Hukumar Gwamnati Ta Shekarar 2025
- Domin faɗaɗa iyakokin aiwatar da doka a Nijeriya tare da dawo da fiye da naira biliyan 10 ga masu amfani da kayayyaki tare da ƙalubalantar rashin adalci na kamfanoni da ƙafa sabbin ƙa’idoji kula da kasuwanci ta kafafen sadarwar zamani da tabbatar da adalci da shugabanci na na gari — Hukumar Kare ‘Yancin Masu Amfani da Kayayyaki ta Ƙasa (FCCPC), ita ce Gwarzuwar Hukumar Gwamnati ta Shekarar 2025.
Hukumar Kare Ƴancin Masu Amfani Da Kaya (Fccpc): Tabbatar Da Adalci A Kasuwa
SkalesShi Ne Gwarzon Mawaƙin Shekarar 2025
- Sakamakon tasirin da ya daɗe yana yi a fannin waƙa a Nijeriya da ƙasashen waje. Shahararriyar waƙarsa “Shake Body”, wacce ta kai ga samun miliyoyin masu sauraro a Spotify da kuma ƙwarewarsa a fannin fasahar haɗa al’umma daban-daban. SKALES ne Gwarzon Mawaƙin Shekarar 2025.
Kanyenyachukwu Tagbo Okeke Shi Ne Gwarzon Mai Zane Na Shekarar 2025
- Saboda sanya Nijeriya a taswira ta duniya tare da Guinness World Record (GWR) na Mafi Girman Zanen Canɓas da mutum ɗaya ya yi a wannan shekara, da kuma wayar da kan jama’a kan cutar autism a Nijerriya, tare da amfani da fasaha wajen ƙarfafa haɗin kai da ilimi ga mutane masu ƙwarewa daban-daban, Kanyenyachukwu (wanda aka fi sani da Kanye) Tagbo-Okeke shi ne Gwarzon Mai Zane na Shekara 2025.
Gwarzon Mai Koyar Da Wasanni Na Shekarar 2025
- Saboda jagorantar Super Falcons zuwa nasarar lashe kofin WAFCON karo na 10, wanda ya ƙara musu tasiri; da nuna ƙwarewa a dabaru da shugabanci da dawo da aminci a ƙwallon ƙafar Nijeriya da kuma ƙarfafa sabon ƙarni na masu horar da ƙwallo a Afirka, Justine Madugu shi ne gwarzon mai koyar da wasanni na Shekarar 2025.
Justine Madugu: Mai Dabaru Dawo Da Darajar Ƙwallon Ƙafa A Nijeriya
Xavid Adeyemi Shi Ne Gwarzon Matashi Na Shekara 2025
- Dangane da haɓaka ƙirƙira, tausayi da ƙwarewa ta hanyar ƙirƙirar manhajar AI wacce ke sauya yadda ɗalibai masu naƙasar gani ke samun ilimi a Nijeriya da wajenta, Xavid Adeyemi shi ne Gwarzon Matashi na Shekarar 2025.
Gwarzon Ma’aikacin Lafiya Na Shekarar 2025
- Domin ganin yadda ya sauya aƙalar samar da kiwon lafiya cikin tausayi da soyayya ga mabuƙata tare da yi wa mutane fiye 2,600 tiyata kyauta a sassan ƙasar nan. Dr Seidu Adebayo Bello shi ne Gwarzon Ma’aikacin Kiwon Lafiya na shekarar 2025.
Dr Seidu Adebayo Bello: Ya Dawo Da Fata Ga Al’umma
Misis Mabel Ijeoma Duaka Shi Ne Gwarzuwar Ma’aikaciyar Jinya Ta Shekarar 2025
- Duk da ayyukan ta’addanci na Boko Haram, yayin da al’umma musamman baƙi ke gudu daga yankuna da dama na Jihar Borno, ta gwammace ta zauna a ƙaramar hukumar Mafa domin ci gaba da bayar da kulawa ga waɗanda suka jikkata na tsawon shekara 21. Mrs Mabel Ijeoma Duaka ce Gwarzuwar Ma’akaciyar jinya ta shekarar 2025
Bankin Proɓidus Ne Gwarzon Banki Na Shekarar 2025
- Saboda kasancewa kan gaba wajen zamanantar da harkokin Banki a Nijeriya da kuma ƙarfafa wa manya da ƙananan masa’na’antu tare da zama a kan gaba wajen ɗaukaka darajar aikin Banki a Nijeriya, Bankin Proɓidus ne Gwarzon bankinmu na shekarar 2025.
Gwarzuwar Matashiya ‘Yar Makaranta Ta Shekarar 2025
- Domin nasarar da ta samu wajen sanya sunan Nijeriya a fagen ilimi a duniya da jajircewa, hazaƙa da bayar da shawarwari don zaburar da sabbin ɗalibai don rungumar harshe Turanci da tabbatar da nasara na iya tasowa daga kowane ɓangare. An bai wa Nafisa Abdullahi Aminu lambar yabo ta Gwarzuwar Matashiyar 2025.
Nafisa Abdullahi Aminu: Yarinyar Da Ta Ɗaukaka Darajar Nijeriya A Idon Duniya
Hukumar NASENI Ne Gwarzuwar Hukumar Da Ta Kawo Sauyi A Kula Da Muhalli A 2025
- Domin yadda ta jagoranci ci gaban masana’antu, samar da makamashi, da fasahohin da suka dace da yanayin da ke rage fitar da iskar carbon mai guba da inganta hanyoyin samar da wutar lantarki mai tsabta; ƙarfafa masu ƙirƙire-ƙirƙire na cikin gida, samar da dabarun tattalin arziƙin mai ɗorewa, da haɓaka dogaro da kai a Nijeriya ta hanyar bincike da kula da muhalli, Hukumar NASENI ce Gwarzuwar Hukumar da ta fi tasiri wajen kare muhalli a shekarar 2025.
Gwarzon Kamfanin Fasahar Kuɗaɗe Na Shekarar 2025
- Don kawo sauyi a harkokin kuɗaɗe ta hanyar fasahar zamani da suka haɗa da ƙirƙira da gaskiya wajen ƙarfafa miliyoyin ‘yan Nijeriya, ƙanana da matsakaitan kamfanoni (MSME) ta hanyar amfani da wayar hannu, don kawo ƙarshen matsalolin kuɗaɗe ta hanyar fasahar zamani, OPay Nigeria ya amsa sunansa na zama gwarzon kamfanin fasahar harkokin kuɗaɗe na shekarar 2025.
OPay Nigeria: Tabbatar Da ‘Yancin Hada-hadar Kuɗi
Kamfanin GEIL: Gwarzon Kamfanin Samar Da Kayayyakin Gida Na Mai Da Gas Na Shekarar 2025
- Domin jagorantar bunƙasawa da gudanar da tashar fitar mai na farko a Nijeriya fiye da shekaru 50, Kamfanin GEIL shi ne Gwarzon Shekarar 2025
Gwarzon Kamfanin Samar Da Kaya Na Shekarar 2025
- Domin haɓaka samar da ruwan sha mai inganci da arha, ɗanɗano da wayar da kan ƴan ƙasa kan amfani da tsaftataccen ruwa, kamfanin Nestlé Pure Life Nigeria Plc shi ne gwarzon samar da kaya a shekarar 2025.
Kamfanin Nestlé Pure Life: Tsarinsa Da Manufa
Kamfanin Trade Modernisation Project: Gwarzon Kamfani Na Shekarar 2025
- Domin sauya tsarin kasuwancin Nijeriya ta hanyar fasahar zamani da inganci, sarrafa ayyuka, ƙara haɓaka samun kuɗaɗen shiga da saukaka gudanar da kasuwanci, bunƙasa haɗin gwiwar gwamnati da masu zaman kansu, samar da ayyukan yi da ƙarfafa gasa, Kamfanin Trade Modernisation Project (TMP) shi ne gwarzon Kamfanin shekarar 2025.














