ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Tuesday, September 8, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

by Leadership Hausa
49 minutes ago

Ƙungiyar shugabannin ƙananan hukumomi da sakatarorin ƙungiyoyin jam’iyyar APC a Jihar Katsina ta bayyana cikakken goyon bayanta ga Gwamna Dikko Umaru Radda, bisa la’akari da yadda ya jagoranci jihar cikin shekaru uku da suka gabata.

An cimma wannan matsayar ne a ranar Talata, a zauren majalisar zartarwa na Gidan Muhammadu Buhari da ke Katsina, yayin da ƙungiyar ke miƙa rahoton rangadin da ta gudanar a mazabun tarayya 15 da ke jihar.

Shugaban ƙungiyar, Alhaji Salisu Mamman, ya ce gwamnatin Gwamna Radda ta samu ci gaba a fannonin ababen more rayuwa, ilimi, kiwon lafiya, noma da bunƙasa ɗan Adam.

ADVERTISEMENT

Ya ce salon shugabancin gwamnan, wanda ya ginu kan gaskiya, riƙon amana da bai wa kowa dama, ya dawo da amincewar jama’a tare da kawo ci gaba zuwa matakin ƙananan hukumomi da al’umma.

Alhaji Mamman ya ƙara da cewa ƙungiyar ta miƙa wuya ga jagorancin gwamnan, tare da bayyana aniyarta ta ganin APC ta samu nasara a zaɓen 2027 a ƙarƙashin jagorancinsa.

LABARAI MASU NASABA

2027: Atiku Na Amfani Da Tallafin Mai A Matsayin Dabarun Siyasa – Fayemi

Muna Da Yan Takarar Gwamna A Jihohi 28 Don Shiga Zaben 2027

Ya kuma gabatar da rahoton kwamitin da ya gudanar da rangadin, inda ya ce aikin ya ba su damar tattaunawa kai tsaye da masu ruwa da tsaki na jam’iyyar a matakin ƙasa, tare da gano abubuwan da ke ƙarfafa haɗin kai da kuma ƙalubalen da ake fuskanta.

A cewarsa, dukkan ƙananan hukumomi 34 na jihar suna da kwamitocin tuntuɓa da gangamin jama’a masu aiki a matakan ƙaramar hukuma, mazabu da rumfunan zaɓe, ciki har da tsare-tsaren da suka shafi matasa, mata da dattawa.

Ya kuma bayyana wasu muhimman batutuwan da aka gabatar yayin rangadin, inda ya buƙaci gwamnan da ya duba shawarwarin tare da amfani da su a matsayin taswira wajen ƙarfafa jam’iyyar gabanin zaɓe.

A nasa jawabin, Gwamna Dikko Umaru Radda ya gode wa masu ruwa da tsakin bisa biyayyarsu, jajircewarsu da sadaukarwarsu ga jam’iyyar.

Gwamnan ya yaba musu bisa gudanar da rangadin tare da samar da sahihin bayani daga matakin ƙasa, yana mai cewa irin wannan hulɗa na da matuƙar muhimmanci wajen ƙarfafa APC.

Ya kuma buƙace su da su tabbatar da haɗin kan da ya kasance alamar jam’iyyar zuwa zaɓen 2027. Ya yi kira gare su da su ƙara himma wajen tattara jama’a domin ganin an sake zaɓar Shugaba Bola Ahmed Tinubu, da kuma dukkan ’yan takarar APC a Jihar Katsina.

Ya ce samun nasara a zaɓen na buƙatar haɗin kai da aiki tare.

Taron ya samu halartar Shugaban Ma’aikatan Gwamna, Hon. Abdulkadir Mamman Nasir; Kwamishinan Filaye da Tsare-tsaren Birane, Dr. Faisal Kaita; Mai Ba Gwamna Shawara kan Harkokin Siyasa, Hon. Yau Umar Gwajo-Gwajo, da Mai Ba Gwamna Shawara kan Hulɗa da Jam’iyya, Hon. Shafiu Abdu Duwan.

Leadership Hausa
+ postsBio
  • Leadership Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/leadership-hausa/
    Jerin Gwarazan Taurarinmu
  • Leadership Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/leadership-hausa/
    Jerin Gwarazan Taurarinmu
  • Leadership Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/leadership-hausa/
    “Ba Gudu Ba Ja Da Baya Game Da Tsarin “Call-up system” A NPA”
  • Leadership Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/leadership-hausa/
    Gwarzon Ma’aikacin Gwamnati Na Shekarar 2025, Dakta Zacch Adedeji

MASU ALAKA

2027: Atiku Na Amfani Da Tallafin Mai A Matsayin Dabarun Siyasa – Fayemi
Manyan Labarai

2027: Atiku Na Amfani Da Tallafin Mai A Matsayin Dabarun Siyasa – Fayemi

September 8, 2026
Siyasa

Muna Da Yan Takarar Gwamna A Jihohi 28 Don Shiga Zaben 2027

September 6, 2026
Siyasa

Fafatawa Kan Kuri’un Kano Miliyan 5.9 Na Ƙara Zafafa

September 6, 2026
Next Post
Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.