Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya sanar a kwanan baya cewa, ba zai gayyaci Afirka ta Kudu ta halarci taron kolin kungiyar G20 da za a gudanar a birnin Miami na kasar Amurka a shekara mai zuwa ba.
Kasancewarsa muhimmin dandali na hadin gwiwar tattalin arzikin duniya, wakilci da hakuri su ne tushen kungiyar G20. Daga cikin kasashe mambobin kungiyar G20, kungiyar tarayyar Afirka (AU) da kuma kasar Afirka ta kudu, su biyu ne kadai suka fito daga nahiyar Afirka. Don haka, ba kawai kasar Afirka ta Kudu na wakiltar kanta ba ce, har ma tana dauke da nauyin fitar da muryar kasashen nahiyar game da gudanar harkokin tattalin arzikin duniya. Amma sai ga shi Amurka ta sanya bukatarta sama da matsayar sassan kasa da kasa, tana mai daukar odar duniya a matsayin wadda za ta iya takewa, tare da kallon hukumomin kasa da kasa a matsayin dan wasan dara da za ta iya sauyawa wuri a duk lokacin da take so, wanda hakan ya shaida yadda Amurka ke nuna fin karfi a duniya, da ma matsalar da ake fuskanta a tsarin kula da al’amuran duniya.
- Ma’aikatan Shari’a Sun Fara Yajin Aiki Kan Bashin Albashi Da Kuɗin Hutu A Kogi
- Ko Kwalliya Za Ta Biya Kuɗin Sabulu Kan Sauye-sauyen Tinubu Na Inganta Tsaro A Nijeriya?
Amma irin yanayi na nuna fin karfi da Amurka ke yi ba zai dore ba, ta la’akari da jerin wasu muhimman tarukan da aka gudanar a watan Nuwamban da ya gabata, wadanda suka samu muhimman nasarori ko da yake ba tare da hallarar kasar Amurka ba.
A ranar 7 ga watan Nuwamban da ya gabata, hukumar kula da hakkin bil Adam ta MDD ta kira taron musamman, don yin nazari a kan harkokin hakkin bil Adam na kasar Amurka a karo na hudu. Tsarin nazarin harkokin hakkin dan Adam na kasa da kasa muhimmin tsari ne da MDD ta kafa don neman inganta musaya da hadin gwiwa a tsakanin kasa da kasa ta fannin kare hakkin dan Adam. Tun kafuwarsa a shekarar 2007, an gudanar da nazarin a kan kasashe mambobi 193 na MDD har sau uku, amma Amurka ta ki a yi mata sabon zagaye na nazarin. Duk da haka, sassan kasa da kasa sun tabbatar da gudanar tsarin nazarin ba tare da tsayawa ba, ta hanyar tsara sabon jadawali, da kuma gabatar da sabbin shawarwari, ta yadda tsarin kula da hakkin dan Adam na duniya zai kara kare adalci da samar da tasiri mai muhimmanci.
Haka nan kuma a ranar 10 ga watan Nuwamban, an gudanar da taron masu sa hannu a yarjejeniyar sauyin yanayi ta MDD (COP30) a birnin Belém na kasar Brazil. Amurka a matsayinta na kasar da ta fi yawan fitar da hayaki mai dumama yanayi a tarihi, ba ta tura wakilai masu babban matsayi zuwa taron ba, ban da wani mai taimakawa sakataren harkokin wajen kasar da ke kula da harkokin muhalli. Sai dai hakan bai haifar da cikas ga taron ba, bisa shawarwarin da mahalarta taron suka shafe tsawon kwanaki 13 suna yi, taron ya zartas da shawara mai taken “kira ga duniya: hadin gwiwa don tinkarar sauyin yanayi”, shawarar da ta bukaci kasashe masu ci gaba su taimaka wa kasashe masu fama da koma baya, wajen inganta kwarewarsu ta fannin tinkarar sauyin yanayi.
Ya zuwa ranar 22 ga watan Nuwamban, an kaddamar da taron kolin G20 a birnin Johannesburg na kasar Afirka ta Kudu, taron da ya kasance irinsa na farko da aka gudanar a nahiyar Afirka. Amma gwamnatin kasar Amurka ba ta halarci taron ba, har ma ta yi ta yi wa kasar Afirka ta Kudu mai masauki baki matsin lamba tun ba a fara taron ba, ta kuma ki yarda da taron ya bayar da sanarwa bisa taken daidaiton kungiyar G20 ba tare da samun amincewarta ba. Duk da hakan, mahalarta taron sun cimma daidaito a ranar farko da aka bude taron, har ma suka zartas da “sanarwar Johannesburg ta shugabannin G20” wadda ke kunshe da tanade-tanade 122, wanda hakan ya kafa sabon tarihin G20.
Lallai jerin abubuwa da suka wakana sun shaida yadda al’ummomin duniya ke rungumar hadin gwiwar cin moriyar juna a maimakon nuna fin karfi da ra’ayi na kashin kai. Zamanin da komai sai ya samu amincewar Amurka yana dab da karewa, kuma ana fitowa da sabon tsarin da kasa da kasa ke binsa a hadin gwiwarsu, yayin da suke kula da harkokin duniya. Yadda Amurka ke kauracewa tarukan bai haifar da komai ba, illa yin watsi da ita a fannin kulawa da harkokin duniya. Harkokin duniya na gudana yadda ya kamata, ko ba tare da Amurka ta sa hannu a ciki ba, kuma duniya za ta kara kyau in ba a nuna fin karfi.














