El-Rufai Ga Gumi: Ka Daina Bata Wa Kanka Lokacin Sulhu Da ’Yan Bindiga

Sulhu

Daga Khalid Idris Doya,

Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai ya shaida wa fitaccen malamin addinin Islama din nan, Sheikh Ahmad Gumi cewar ya daina bata wa kansa lokaci wajen tattaunawa da yin sulhu da ‘yan bindiga da suke sassan jihohin arewa maso yamma.

El-Rufai ya shaida cewar, ‘yan bindigan da suke saida saniya kan kudi naira 100,000, ba za su amince wajen ajiye makamansu ba tattare da cewa su na amsar miliyoyin naira daga hannun wadanda suka yi garkuwa da su.

“Mutumin da ya saba samun naira dubu dari a shekara bayan ya saida shanu, yanzu ya dawo yana samun miliyoyin na kudin fansar mutanen da ya sace, ba zai taba daina garkuwa da mutane ba,”

Gwamnan ya ce rashin hadin kai tsakanin gwamnonin yankin na daga cikin abubuwan da suka sa aka kasa shawo kan matsalar ‘yan fashi masu garkuwa da mutane.

A hirarsa da BBC Hausa, gwamnan ya ce yana da ra’ayin a bude wa ‘yan bindigar wuta kuma babu batun sulhu tsakanin gwamnatinsa da masu garkuwa da mutane. 

Sai dai shi gwamna El-Rufai ya bayyana ra’ayinsa na sanya karfin soja wajen dakile ‘yan bindigan a lokaci daya, “Idan Gwamnatin tarayya ba ta ba mu sojoji na sama da na kasa ba, an shiga dazukan nan an kashe ‘yan ta’addan nan a lokaci daya, to za mu ci gaba da zama cikin matsala,” inji gwamnan.

A cewarsa: “Mu a Kaduna muna hada kai da Jihar Neja. Gwamnan jihar na kira lokaci zuwa lokaci muna hada bayanai. Muna abubuwa tare da su.”

Ya bayyana haka ne a yayin da ‘yan bindigar ke ci gaba da cin karensu babu babbaka a yankin.

Kazalika, kalamin nasa ya sha bamban da na wasu gwamnonin yankin wadanda ke ganin yin sulhu da ‘yan bindigar shi ne mafita ga rashin tsaron da ke addabar arewa maso yammacin Nijeriya.

El-Rufai ya nuna cewa matakin malamin addinin shiririta da bata lokaci ne kawai. Ya dage kan cewa muddin gwamnonin arewa maso yamma suka hada kansu za a samu nasarar shawo kan matsalar ‘yan bindigan cikin sauki.

El-Rufai ya ce, bai goyon bayan sulhu da ‘yan bindigan kuma ba zai haifar da wani da mai ido ba, don haka a sake musu ruwan alburusai kawai a cikin dazukan da suke boye.

A cewarsa, “Bafulatanin da ke samun naira dubu dari a shekara bayan ya saida saniya, amma yanzu yana samun miliyoyin naira na fansa da yake amsa daga wurin wadanda ya yi garkuwa da su, ba zai taba daina garkuwa da mutane ba.

“Gumi abokina ne. abun da muka tattauna kan ‘yan bindiga ya sha banban da abun da yake yi. Na yi imanin duk mutumin da zai ce min ta hanyar wa’azi dai jawo hankalin mutanen nan su daina abun da suke yi, ba zan yard aba. Kawai yana yaudarar kansa da kansa da bata wa kansa lokaci ne, ba za su fa daina don hakan ba,” inji El-Rufai.

Gwamnan ya nuna cewa ‘yan ta’addan masu garkuwa da mutane da suka kashe daruruwan jama’a, da kona gidajen jama’a da kadarorinsu sun dace da kowace irin hukunci.

Exit mobile version