Kaudar tumatur na daga cikin hanyar da manoma kan bi wajen adana tumaturi domin yin amfani da shi a lokacin da babau danye, musamman a lokacin bazara ko kuma tsakiyar damuna.
Akwai wurare daban-daban da ake noman tumatur a fadin kasar nan a lokacin rani, Kwanar-gafan da ke karamar hukumar Garun-malam, a jihar Kano na daga cikin manyan kasuwannin tumatur a fadin kasar nan, wadda ake zuwa daga sassa daban-daban domin yin kasuwcin tumaturin.
- Kasar Sin Ta Fitar Da Takardar Bayani Kan Matsayinta Na Warware Matsalar Ukraine A Siyasance
- Shawarwarin Dattawan Arewa Kan Zaben 2023
Ana kai tumaturin zuwa sassa daban-daban na kasar nan, har ma zuwa makotanmu. Manoman wannan yanki na kai tumaturin nasu wannan kasuwa, domin su sayar.
Kasuwar na daga cikin kasuwannanin da ke samar da hada-hadar kasuwanci ga dimbin al’umma daga sassa daban-daban na kasar nan.
Bayan hada-hadar kasuwancin danyen tumaturin akwai wadanda ke hada-hadar kasuwancin kaudarsa, wato busasshensa ke nan.
Mayar da tumaturin zuwa kauda na taimaka wa manomansa rage asara, musamman idan suka daure, suka adana shi zuwa wani lokaci,wato, lokacin farkon damuna, kafin na damuna ya fara shigo wa.
Sai dai duk da haka, a kan yi hada-hadar kasuwancin kaudar tumaturin tun daga lokacin da aka fara shanya shi.
A bana musamman halin da aka shiga na sauyin kudi, ya dakile kasuwar tumatur yadda manomansa suka yi dimbin asara. Masu nomansa da masu kasuwancinsa sun shiga halin tsaka-mai-wuya, saboda matsalar kudin da za yi amfani da su wajen yin safarar ta sa. Wannan ta sa dole manoman suka shiga shanya tumaturin nasu, tunda babu kasuwa.
A makwanni biyu da suka wuce a kasuwar kwanan-gafan babbar kasuwar tumaturin ta Kwanar-gafan kasuwar tunatur ta fadi kasa warwas, inda manoma ke sayar da katon Kwando a kan naira dubu biyu zuwa naira dubu biyu da dari biyar, wannan ta sa yawan masu shanyarsa ya karu. Karuwar masu shanyar ta sa farashin busassahen tumaturin ya fadi kasa warwas.
Duk da cewa, a daidai wannan loacin, lokaci ne na ganiyar samun kaudar tumaturin, kuma yakan yi sauki matuka, wanda har masu sari kan saya su adana shi, to amma a bana faduwar farashin ta yi kasa sosai, saboda wanda yakamata a sayar da shi kuma a yi amfani da shi tun yana danye, yanayi ya sa hakan ba ta yiwu ba.
Manoman tumarurin dai sun koka matuka da faduwar farashin, domin yana taimaka musu wajen samun kudaden yin hidimarsau ta yau da kullum.
Sannan kuma yana taimaka wa manoman wajen yin noman damuna. Saboda haka a bana manoman na tumatur da masu kasuwancin busassahen tumaturin sun shiga halin tsaka-mai-wuya.
Sannan kuma a daidai wannan lokacin da ake sanyi, yawan tumarun da ake diba na karuwa. Ga yawa na karuwa ga farashi na sauka.
Sai dai wani manomi da aka zanta da shi, a kasuwar ta Kwanar-gafan ya tabbatar da cewa, faduwar farashin kaudar tumaturin zai shafi noman damina, domin kudin da suke samu daga noman tumatirin ya ragu kwarai.
Sannan kuma wasu manoman sun bukaci gwamnati da manyan ‘yan kasuwa da su taimaka musu wajen kafa musu masana’antar da za ta sarrafa tumaturin yadda za a iya adana shi, da kuma daukarsa a kai shi sassa daban-daban na ciki da wajen kasar nan. Domin kuwa yin hakan zai taimaka musu wajen rage asarar da suke fuskanta a halin yanzu.
Wani mai kasuwancin kaudar tumaturin da ke zaune a garin Kwanar-dangora, mai suna Sani Bilak, ya koka matuka kan yadda a bana hada-hadar kasuwancin ta su ta samu cikas, wanda ya ce, hakan ta kawo musu cikas matuka.
Don haka, shi ma kiran da nasa ga gwamnati ya yi da manyana ‘yan kasuwa da su samar da hanyar da za a dinga adana tumaturin domin guje wa irin wannan mummunar asara.
Masu shanyar kaudar tumaturin su ma sun ce da gwamnati za ta tallafa musu wajen samar musu da na’urar da za ta busar da tumaturin da an samu saukin yawan asarar da ake yi, sannan kuma zai kasance yana da tsafta, amma a halin yanzu ana sanya shi a wuraen da ba su dace ba. Inda babu cikakkiyar tsafta.