’Yansandan Isra’ila sun kama wasu mutane bisa zargin hannu a hare-haren da aka kai wa wata ’yar jarida Ba’amurkiya da wasu jami’an diflomasiyya na Turai a Yammacin Kogin Jordan, wanda Isra’ila ta mamaye.
Rahoton kamfanin dillancin labarai na Associated Press (AP), wanda aka wallafa ranar Litinin, 19 ga Oktoba, 2026, ya ce kama mutanen ya biyo bayan hare-hare biyu da aka kai a ranakun Juma’a da Asabar.
A ranar Juma’a, 16 ga Oktoba, 2026, wata tawagar mazauna matsugunan Isra’ila ta kai hari kan Heidi Levine, mai ɗaukar hotuna ga jaridar The Washington Post, yayin da take ɗaukar rahoton girbin zaitun a ƙauyen Abu Falah.
Rahoton ya ce Levine ta samu munanan raunuka, ciki har da karyewar wasu ƙasusuwan bayanta da haƙarƙarinta.
Ta kuma yi tiyata a yatsar da ta kusa tsinkewa sakamakon harin.
A ranar Asabar, 17 ga Oktoba, 2026, wasu mazauna matsugunan Isra’ila da suka rufe fuskokinsu sun kai hari kan jami’an diflomasiyya daga ƙasashen Turai da wasu mutane a ƙauyen Taybeh, wanda ke da al’ummar Kiristoci a Yammacin Kogin Jordan.
Jami’an diflomasiyyar da abin ya shafa sun haɗa da wakilai daga Belgium, Faransa da Poland, tare da wani magajin gari daga Faransa da wakilan addinin Kirista.
A ranar Litinin, 19 ga Oktoba, ’yan sandan Isra’ila sun sanar da kama mutane 10 dangane da hare-haren.
Sai dai ba su bayyana sunayen waɗanda aka kama ko takamaiman zargin da ake yi wa kowannensu ba.
Hukumomin Isra’ila sun ce ana ci gaba da bincike, yayin da hare-haren suka jawo suka daga jami’an Amurka da na ƙasashen Turai.














