ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Saturday, October 24, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

UTME: Ɗalibai 108 Daga 39,000 ’Yan Ƙasa Da Shekaru 16 Ne Suka Cika Sharuddan Shiga Jami’a

by Muhammad
3 days ago

Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa ɗalibai 108 kacal daga cikin kusan 39,000 da ba su kai shekara 16 ba, waɗanda suka rubuta jarrabawar shiga manyan makarantu ta UTME ta shekarar 2026, ne suka cika sharuddan da za su ba su damar neman shiga jami’a da wuri.

Ministan Ilimi, Dakta Tunji Alausa, ne ya bayyana hakan ranar Laraba a Abuja, yayin da yake karɓar ɗalibai biyu da suka fi kowa maki a jarrabawar UTME ta 2026 da wasu fitattun ɗalibai shida da ba su kai shekara 16 ba. Magatakardar Hukumar Shirya Jarrabawar Shiga Manyan Makarantu (JAMB), Farfesa Segun Aina, ne ya gabatar da ɗaliban ga ministan.

A cewar Alausa, ɗaliban sun samu wannan nasara ne bayan sun bi matakai daban-daban na tantancewa domin tabbatar da cewa sun cancanci fara karatun manyan makarantu tun suna ƙanana.

ADVERTISEMENT

Ya ce cikin ɗalibai 2,244,149 da suka yi rajistar jarrabawar UTME ta 2026, mutum 2,174,396 ne suka zauna jarrabawar, inda kusan 39,000 daga cikinsu ba su kai mafi ƙarancin shekarun shiga manyan makarantu na 16 ba.

Ministan ya bayyana cewa ɗaliban da suke neman a keɓe su daga sharadin shekarun shiga jami’a dole ne su samu aƙalla maki 320 cikin 400 a UTME, wanda yake daidai da kashi 80 cikin 100.

LABARAI MASU NASABA

Gwamnatin Gombe Ta Biya Biliyan 10.32 Kuɗin Garatutin Masu Ritaya 6,665

Ɗalibai Sun Yaba Wa Gidauniyar Dangote Kan Shirin Rabon Hannun Jari Kyauta

Haka kuma, ana buƙatar su samu aƙalla kashi 80 cikin 100 a jarrabawar Post-UTME ta jami’o’in da suka zaɓa, su cika irin wannan sharadi a tantance sakamakon jarrabawar kammala sakandare, sannan su yi nasara a tantancewar da za ta tabbatar da ƙwarewarsu ta tunani da kuma balagar zuciya da tunani da ake buƙata domin karatun jami’a.

Alausa ya ce ɗalibai 391 ne kawai daga cikin waɗanda ba su kai shekara 16 ba suka samu maki 320 ko sama da haka a UTME. Bayan ƙarin tantancewa, adadin waɗanda suka cika sharuddan neman shiga jami’a ya ragu zuwa 108.

Ya bayyana waɗannan ɗalibai a matsayin masu hazaka ta musamman, yana mai cewa sun kai kusan kashi 0.005 cikin 100 na ɗaliban da suka zauna jarrabawar.

Ministan ya jaddada cewa manufar sanya mafi ƙarancin shekarun shiga manyan makarantu a 16 ba wai don hana ƙwararrun yara ci gaba da karatu ba ce, sai dai domin tabbatar da cewa suna da balagar da za ta taimaka musu wajen fuskantar ƙalubalen rayuwar jami’a.

A cewarsa, sakamako mai kyau a jarrabawa kaɗai bai isa ya tabbatar da cancantar ɗalibi shiga jami’a tun yana ƙarami ba, domin ana kuma buƙatar ya kasance da ƙwarewar tunani, daidaituwar zuciya da kuma iya mu’amala da ƙalubalen zamantakewa da ilimi.

Ya ce sakamakon tantancewar ya nuna cewa ɗaliban sun nuna kwarin gwiwa, ƙwarewar tunani da kuma iya amsa tambayoyin da aka yi musu domin auna shirye-shiryensu na shiga manyan makarantu.

Alausa ya buƙaci ɗaliban da suka cika sharuddan da su ɗauki hazakarsu a matsayin nauyin da ya rataya a wuyansu na taimaka wa al’umma, ba kawai wata dama ta samun shiga jami’a da wuri ko ci gaban kansu ba.

Ya ce matasan na da damar samar da sabbin dabaru da hanyoyin magance matsalolin da ke addabar Nijeriya da sauran ƙasashen duniya.

Ministan ya danganta bunƙasa hazakar matasa da ci gaban ƙasa, yana mai cewa yawan matasan Nijeriya wata babbar dama ce da ya kamata a ilimantar da su yadda ya kamata domin su taimaka wajen samar da sabbin abubuwa da za su inganta rayuwar al’umma.

Ya ƙiyasta yawan al’ummar Nijeriya da kusan miliyan 220, inda ya ce matsakaicin shekarun al’ummar ƙasar su ne 18.5, yayin da kusan kashi 70 cikin 100 na al’ummar ba su kai shekara 30 ba.

Ya ƙara da cewa gyare-gyaren da gwamnatin tarayya ke yi a ɓangaren ilimi na da nufin faɗaɗa damar karatu ga matasan ƙasar da kuma ƙarfafa hanyoyin da za su mayar da hazakarsu zuwa sabbin dabaru da za su amfani al’umma.

Alausa ya taya ɗaliban murna a madadin Shugaba Bola Tinubu da Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya, yana mai bayyana fatan cewa hazakarsu za ta haifar da nasarorin da za su amfani miliyoyin mutane.

Ɗalibai takwas, ciki har da waɗanda suka fi kowa maki a UTME ta 2026 da kuma shida daga cikin waɗanda ba su kai shekara 16 ba, sun samu lambobin yabo da takardun shaidar karramawa daga ministan.

Owoeye Daniella Jesudunsin ce ta zo ta farko da maki 372, yayin da Enwere Kingsley Ikenna ya zo na biyu da maki 370.

Muhammad
+ postsBio
  • Muhammad
    ‘Kana Cikin Rudu’ — Atiku Ya Mayar Wa Tinubu Martani Kan Zargin Yunwa Da Talauci
  • Muhammad
    Me Tinubu Zai Yi Wa Arewa Alƙawari A Ƙaddamar Da Yaƙin Neman Zaɓensa A Kaduna?
  • Muhammad
    2027: Matawalle Ya Bai Wa ’Yan Majalisar Zamfara Takwas Motocin Alfarma Kirar SUV
  • Muhammad
    ’Yan Sanda Sun Kama ’Yan Ƙungiyoyin Asiri Takwas da Masu Damfarar ATM Uku A Kogi

MASU ALAKA

Ilimi

Gwamnatin Gombe Ta Biya Biliyan 10.32 Kuɗin Garatutin Masu Ritaya 6,665

October 9, 2026
Ɗalibai Sun Yaba Wa Gidauniyar Dangote Kan Shirin Rabon Hannun Jari Kyauta
Ilimi

Ɗalibai Sun Yaba Wa Gidauniyar Dangote Kan Shirin Rabon Hannun Jari Kyauta

October 5, 2026
Jami’ar Dutse Zata Rabauta Da Isasshiyar Wutar Lantarki
Ilimi

Jami’ar Dutse Zata Rabauta Da Isasshiyar Wutar Lantarki

October 1, 2026
Next Post
2027: Matawalle Ya Bai Wa ’Yan Majalisar Zamfara Takwas Motocin Alfarma Kirar SUV

2027: Matawalle Ya Bai Wa ’Yan Majalisar Zamfara Takwas Motocin Alfarma Kirar SUV

LABARAI MASU NASABA

ADC Da Atiku Sun Zargi Gwamnatin APC Da Yin Watsi Da Jin Daɗin Malamai

‘Kana Cikin Rudu’ — Atiku Ya Mayar Wa Tinubu Martani Kan Zargin Yunwa Da Talauci

October 24, 2026
Allah Ya Bai Wa Annabi (SAW) Mu’ujizozi Fiye Da 2,000 A Alƙur’ani

Tsarin Kwalliya Da Adon Manzon Allah (SAW)

October 24, 2026
2027: Duk ’Yan Arewan Da Ke Takarar Shugaban Ƙasa Maƙiyan Arewa Ne – Akume

2027: Duk ’Yan Arewan Da Ke Takarar Shugaban Ƙasa Maƙiyan Arewa Ne – Akume

October 24, 2026
Sun Haifar Da Yunwa Da Talauci A Nijeriya, Muna Ƙoƙarin Kawar Da Su – Tinubu

Sun Haifar Da Yunwa Da Talauci A Nijeriya, Muna Ƙoƙarin Kawar Da Su – Tinubu

October 24, 2026
Mafarauta Sun Kashe Ƴan Bindiga 14, Sun Kuɓutar Da Mutane 3 Da Aka Yi Garkuwa Da Su A Katsina

Mafarauta Sun Kashe Ƴan Bindiga 14, Sun Kuɓutar Da Mutane 3 Da Aka Yi Garkuwa Da Su A Katsina

October 24, 2026
Yan Bindiga Sun Kashe Mutane 10 A Taraba, Sun Kwashi Kayan Abinci

Yan Bindiga Sun Kashe Mutane 10 A Taraba, Sun Kwashi Kayan Abinci

October 24, 2026
Gwamnatin Kaduna Ta Musanta Zargin Kashe Tiriliyan 2.3 Kan Gangamin APC

Gwamnatin Kaduna Ta Musanta Zargin Kashe Tiriliyan 2.3 Kan Gangamin APC

October 24, 2026
Hukumar Zaɓe Ta Wayar Da Kan Nakasassu Kan Kaɗa Ƙuri’a A Zamfara

Hukumar Zaɓe Ta Wayar Da Kan Nakasassu Kan Kaɗa Ƙuri’a A Zamfara

October 24, 2026
Tinubu Ya Ce Ba Zai Iya Raka ‘Yan Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓensa Kowace Jiha Ba

Me Tinubu Zai Yi Wa Arewa Alƙawari A Ƙaddamar Da Yaƙin Neman Zaɓensa A Kaduna?

October 24, 2026
Taron Kaduna Ya Tabbatar Da Goyon Bayan Arewa Maso Yamma Ga Tinubu — Musa Iliyasu

Taron Kaduna Ya Tabbatar Da Goyon Bayan Arewa Maso Yamma Ga Tinubu — Musa Iliyasu

October 24, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.