Gwamnatin Faransa ta ce za ta fara jefa kayan agaji ta sama zuwa Zirin Gaza.
Wannan agajin ya haɗa da abinci da sauran kayayyakin jin-ƙai masu nauyin tan 40.
- Sin Ta Dade Tana Aiki Tukuru Kan Kiyaye Zaman Lafiya Da Kwanciyar Hankali Na Yanki
- Rikicin Makiyaya Da Manoma: An Kashe Mutum Daya, Gidaje 31 Sun Kone A Abuja
Ministan harkokin wajen Faransa, Jean-Noel Barrot, ya bayyana cewa za su fara wannan aiki a ranar Juma’a, inda za a fara da tan 10 na abinci.
Ya ce za su yi aikin ne tare da haɗin gwiwar ƙasar Jordan, kuma jirage huɗu ne za su ɗauki nauyin aikin.
A cewar Faransa, akwai tan 52 na abinci da aka hana shiga da su Gaza, duk da cewa yankin yana nesa da inda kayan ke ajiye.
Ministan ya kuma ce ƙasarsa na shirin sanya hannu a wata takarda don neman goyon bayan sauran ƙasashe wajen ganin an kafa ƙasar Falasɗinu da Isra’ila.
A taron Majalisar Ɗinkin Duniya da aka gudanar na kwana biyu, ƙasashe 125 sun amince cewa hanyar warware rikicin Gaza ita ce kafa ƙasashe biyu, wato Falasɗinu da Isra’ila.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp