Farfesa Hafsat Ganduje Ta Raba Tallafin Kudi Ga Mutum 1,000 A Karaye

Tallafin

Daga Abdullahi Muhammad Sheka,

Mai dakin Gwamnan Jihar Kano Farfesa Hafsat Abdullahi Ganduje ta jagoranci raba tallafin Naira dubu Goma – Goma ga Mutane 1,000 a Karamar Hukumar Karaye dake Jihar Kano.

Jami’in yada labaran Karamar Hukumar Karaye Haruna Gunduwawa ya shaida wa wakilinmu haka.

An zakulo wadanda suka amfanan ne daga mazabu goma na karamar Hukumar, wadanda suka hada da maza dari hudu da kuma mata dari shida kowannensu.

Da take gabatar da jawabinta a wurin taron, Farfesa Hafsat Abdullahi Ganduje cewa tayi, wannan kudi da aka basu kyauta ne domin zama jari don habaka sana’unsu. Ta sanar da cewa, sama da kananan hukumomi goma sha biyu a Jihar Kano ne suka amfana da irin wannan Tallafi.

Farfesa Hafsat Ganduje ta jadadda cewa,  wannan na cikin kabakin arzikin Gwamnatin Dakta Abdullahi Umar Ganduje na kokarin tabbatar da cewa, Jama’a musamman na kasa na amfana da abubuwan inganta tattalin arziki.

Saboda haka sai mai dakin Gwamnan Jihar Kano ta bukaci wadanda suka amfana da su tabbatar da yin amfani da kudaden domin samun cigaban rayuwa Kamar yadda aka tsara. Daganan sai ta bukaci dandazon mata da matasa a Jihar Kano su ci gaba da shelanta kyakkyawan manufofin Gwamnatin Ganduje domin samun ingantuwar tattalin arziki.

Hakazalika mai dakin Gwamnan ta jinjinawa shugaban karamar Hukumar Karaye Alhaji Balarabe Isyaku bisa nasarorin da ya samu cikin kwanaki 102 na mulkinsa a Karamar Hukumar Karaye. Ta kara da cewa, ayyuka saba’in da shugaban ya gudanar acikin kankanin lokaci abin ayaba ne kwarai da gaske

Da yake gabatar da jawabinsa Kwamishinan Ma’aikatar Kananan Hukumomi da masarautun Jihar Kano Alhaji Murtala Sule Garo ya yabawa Gwamna Ganduje bisa jajircewa kan inganta harkar tsaro a Jihar Kano, don hakan sai Kwamishinan ya tabbatar da cewa Jihar Kano ce tafi sauran jihohi zaman Lafiya a kasarnan.

Alhaji Murtala Sule Garo ya kuma jadadda aniyar Gwamna Ganduje na kammala aikin hanyar Kankare zuwa Kabo wadda ta wuce zuwa Karaye acikin shekara mai kamawa.

Da yake gabatar da nasa jawabin  Kwamishinan Ma’aikatar tarihi da Al’adu na Jihar Kano Alhaji Ibrahim Ahmed Karaye, Madakin Karaye ya jinjinawa Gwamna Ganduje bisa kirkirar makarantar horar da malamai wadda mai Martaba Sarkin Karaye Alhaji Ibrahim Abubukar II ya kirkira da kuma makarantar Ilimin addini mai zurfi.

Madakin na Karaye ya kuma godewa Gwamna Ganduje da mai daukinsa bisa soyayya da kaunar da suke ga al’ummar Karamar Hukumar Karaye, inda ya kalubalanci masu yiwa wannan tsari wata kutunguila dasu sauya tunaninsu.

Tunda farko da take gabatar da jawabin maraba, shugaba Karamar Hukumar Karaye Alhaji Bakarabe Isyaku Yusif cewa ya yi,  Karamar Hukumar sa zuwa yanzu ta samu nasarar aiwatar da ayyuka 70 daga cikin ayyuka 700 da yake fatan aiwatarwa a cikin shekaru uku na mulkinsa.

Shima anasa jawabin Hakimin Karaye Magajin Garin Karaye, Injiniya Shehu Ahmed ya yabawa mai dakin Gwamnan Jihar Kano bisa kaunar da take, musamman ga matan Jihar Kano.

Guda cikin wadanda suka amfana da wannan tallafi, Hajiya Halima Tudun Kaya ta bayyana godiyarsu bisa wannan abin alhairi, sannan tabbatar da alkawarin yin kyakkyawan amfani da tallafin.

Tunda farko sai da mai dakin Gwamnan Jihar Kano ta ziyarci Fadar Sarkin Karaye domin sa albarkarsa.

Da yake karbar tawagar mai dakin Gwamnan Farfesa Hafasat Ganduje, Sarkin Karaye Dakta Ibrahim Abubukar II  ya bayyana ta da cewa jajirtaciyya ce, wadda a  kullum ta ke yiwa mai gidanta fatan alhairi da samun nasara.

Daganan Sarkin ya roki Allah ya ci gaba kare Gwamna da al’ummar Jihar Kano dama kasa baki daya.

Exit mobile version