Mun taba tattauna wannan batu a shafin da muke tattaunawa tare da tsokaci a kan al’amuran zamantakewa na Taskira. Amma saboda muhimmancinsa na ga ya dace na sake dawo da shi a wannan bangare na Marurun Zuciya, saboda wata matsala ce da har yanzu ake fama da ita a cikin al’ummarmu.
Wannan matsala da ke afkuwa ga wasu samarin, bayan kai kudi na gani ina so. Wasu daga cikinsu na daura damarar yin aure, wanda kuma har takan kai da an tura iyaye kai kudin na gani ina so, wanda hakan ke nuni da shaidar an bawa saurayi yarinyar da yake so bisa al’adar Malam Bahaushe.
- Hadin Abincin Kajin Gidan Gona Masu Saurin Girma
- Kotun Ƙoli Ta Sake Tabbatar Da Zaɓen Abiodun A Matsayin Gwamnan Ogun
Wanda kuma hakan ke sa a saka ranar auren masoyan zuwa tsahon wani lokaci. Sai dai wani hanzari ba gudu ba, saka lokaci mai tsaho na aure kan janyo targarda na rugujewar yin auren ga wasu matasan.
Wanda bayan shudewar wasu lokuta da saka rana, iyayen yarinyar kan mayar da kudin auren ba tare da dalilin komai ba. A tawa fahimtar ana samun wannan matsalar ta kowanne bangare, ga su iyayen yarinyar da yarinyar har ma da shi kansa saurayin. Wasu iyayen yarinyar na zaba wa diyarsu namijin da za ta aura ta hangen abin da saurayi yake da shi, musamman wajen ganin yadda yake kashe wa diyarsu kudade masu yawa, yayin da suka samu wanda ya fi shi sai su yanke shawarar mayar wa da yaron kudinsa, musamman in muka yi duba da wannan zamani.
Wasu kuma ba haka bane, bunciken da suka yi ne akan saurayin tun a farko bai yiwu ba, sai bayan lokacin da aka saka ranar aure, sa’annan suke kara samun wasu bayanai a kan yaron, wanda suke ganin yarinyarsu sam! ba ta dace da tsarin yaron ko ahlin yaron ba. Yayin da wasu kuma ke kallon yawan dage-dagen auren da ake yi ke sawa su canja ra’ayinsu gudun kar yarinyarsu ta tsufa a gida. Wasu kuma ganin babu muhallin zama ko kadan ke sawa su fasa bawa yaron ko da kuwa yana da sana’ar yi. Wasu kuma rashin aikin yi da rashin muhalli ke sawa su fasa ba da diyarsu, Wasu kuma umarnin ‘Yarsu kawai suke bi, musamman in ta shiga babbar makaranta sai ta ga sam! ba ajinta ba ne, ko kuma idan ta sami wanda ya fishi sai ta nemi a fasa, su kuma iyayen ba sa duban ka da su zama kananun mutane idan suka maida kudin, amma a haka za su mayar gudun ka da su bata wa diyarsu rai.
Ta bangaren samarin kuwa wasu iyayen saurayin ke sa buri cikin auren wanda har takan kai a rasa lokacin gabatar da auren ko da kuwa an saka ranar auren, akan yawaita daga lokacin auren har ma ya zo ya wuce ba a yi ba, sakamakon burin da aka daukarwa bikin har zuwa lokacin bai gama tabbatuwa ba, har ta kai ga iyayen yarinyar sun gaji da jira sai su fasa. Wani saurayin kuma ya gina soyayyar ne bisa karya, abin da bai da shi ya nuna cewar yana da shi alhalin bai da komai, wani sa’in ma iyayen hayo su yake ba nasa ba ne, komai nasa na aro ne ya ki bayyana kansa a matsayin da yake da shi, wannan ya sa a duk lokacin da gaskiya ta bayyana sai iyayen yarinyar su fasa bawa yaron, domin ko kusa bai dace da diyar su ba.
Wani kuma saurayin yakan boye wasu dabi’unsa ne wanda su kansu iyayensa ba su san yana da dabi’un ba, musamman ta fannin addini ko wasu munanan dabi’un da basu dace da shi ba, a duk lokacin da iyayen yarinya suka gano hakan sukan fasa bawa saurayin diyarsu. Akwai abubuwa da dama wanda ke faruwa har takan ja a mayar da kudin na gani ina so, wanda wajen ya yi kadan a bayyana shi, sai dai a fade su a takaice. Ko shin laifin waye tsakanin Iyayen yarinyar, da yarinyar da shi saurayin? Ko me yake jawo hakan? Ta wacce hanya za a magance matsalar? Za ku iya aiko mana sakonninku ta wannan lamba: 09063836033