Connect with us

KASUWANCI

Fasinja Miliyan 3.65 Suka Bi Ta Nijeriya A Farkon 2018 –NBS

Published

on

Hukumar Kididdiga ta Kasa (NBS) ta sanar da cewar, Fasinjoji miliyan 3.65 suka bi ta Najeriya ta hanyar filayen jiragen kasar nan a farko shekara, sabanin miliyan 3.84 a farkon shekara.

NBS ta bayyana hakan ne a rahoton ta na ma’adanar bayanan ta data yada a kafarta ta yanar gizo na farko shekara da kuma zango na biyu na 2018.

Ta ce, adadin ya sauka da kashi 33.51 bisa dari a shekarar kuma an samu ragin kashi 4.9 bisa dari na Fasinjojin a zagon shekara ta biyu idan aka kwatanta da na shekarar data wuce.

Rahoton ya ce, jimlar jiragen tana sauka shekara bayan shekara, inda duk a zangon shekara ta daya data biyu suka kai kashi (1.4810.17 bisa dari a farkon shekara ta daya da kuma inda a shekara ta biyu ya kai kashi 10.17 idan aka kwatanta dana 2017.

A farkon zangon 2018 jimlar jiragen ta sauka zuwa 96,659, Inda suka kai kashi 5.9 bisa dari an kuma samu karin saukar jiragen dake dakon kaya ta hanyar filin jiegen Jihar Legas a dukkan farkon zangon shekarar daya data biyu, Inda zangon farko a ke da kashi 49.8 bisa dari a zango na biyu kuma a ke da kashi 65.4 bisa dari.

NBS ta ce, hakan ya janyo saukar ta sauka zuwa da kashi 37.8 bisa dari a farko shekarar an kuma samu karin hawa zuwa kashi 25.6 bisa dari a zangon shekara ta biyu da kuma mai zuwa.

Ta ce, kashi 34.2 bisa dari ya karu na jimlar wasikun a farkon tsakiyar shekara idan aka kwatanta da na 3017.

Jimlar kuma wasikun da aka tura a farkon rabin shekarar 2018 ya karu daga nauyin 14,779,558 rabin shekarar 2018, inda aka samu karin kashi 34.2 duk a cikin shekarar

Jimlar wasiku na farkon shekara ta kai nauyin kilogiram 8,313,112, inda ya karu da kashi 38.56 bisa dari zuwa kilogiram  11,518,538 a zagayen shekara ta biyu.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: