Hukumar kula da babban birnin tarayya Abuja ta bayar da umarnin yin amfani da na’urar nadar bayanai ta tsaro CCTV a duk wuraren da jama’a suke acikin babban birnin, domin inganta tsaro.
Ko’odinetan hukumar kula da harkokin babban birnin tarayya Abuja (AMMC), Umar Shuaibu, wanda ya bayyana hakan a wani taron manema labarai a ranar Laraba, ya sha alwashin cewa, daga yanzu za a sanya ya zama tilas yin amfani da na’urar CCTV cikin sharuddan tabbatar da amincewar siyan fili a Abuja.
Ya kuma bayyana cewa, jami’an hukumar za su zagaya cikin gari domin tabbatar da bin wannan umarnin, acewarsa yin amfani da na’urar CCTV za ta taimaka wa jami’an tsaro sosai wajen yakar masu aikata miyagun laifuka a garin.
Har ila yau, kodinetan ya jaddada bukatar ganin dukkanin gine-ginen jama’a da su samar da ingantattun kayan aikin kashe gobara a gidajen su da ma’aikatun su.