ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Sunday, October 25, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

FIFA Ta Dakatar Da Ƙudurin Cefanar Da Gasar Kofin Duniya Bayan Shan Turjiya

by Rabilu Sanusi Bena
3 months ago

Shugaban hukumar FIFA Gianni Infantino ya ce ya soke shirin bayar da damar saka hannun jari ga mutane masu zaman kansu a gasar cin kofin Duniya bayan samun togiya daga hukumomin kwallon kafa a Duniya, Infantino a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na X ya rubuta “Manufarmu a koyaushe ita ce mu hadu mu inganta harkar kwallon kafa a Duniya”.

FIFA hukuma daya tilo dake kula da kwallon kafa ta duniya, ta gabatar da shirin cefanar da hannun jari a gasar kofin Duniya a ranar Talata, tana mai cewa za ta iya samun riba har zuwa dala biliyan 4.2 a sabon shirinta na FIFA Forward Enterprise (FFE), wani reshe na kasuwanci da ta gabatar domin gudanar da kasuwanci a gasar cin kofin Duniya da kuma gasar cin kofin Duniya na kungiyoyi, ta ce, idan aka amince da kudurin, kowace kasa dake zama mamba a hukumar kwallon kafa ta FIFA zata samu akalla dala miliyan 20 a farkon shekarar 2027.

Manyan hukumomin kwallon kafa a Duniya da suka hada da hukumar kwallon kafa ta Turai (UEFA), takwararta ta nahiyar Amurka (CONCACAF), hakazalika da hukumar kwallon kafa ta yankin Asiya (AFC) duka sun nuna turjiya akan kudurin na shugaban hukumar FIFA Gianni Infantino, inda suka ce duk wani shiri da zai iya shafar kwallon kafa a duniya ya kamata a gabatar da shi tare da tattaunawa da Hukumar Kwallon Kafa ta Duniya, Majalisar FIFA, Membobi Kungiyoyi (MA) da sauran masu ruwa da tsaki a kan lokaci.

ADVERTISEMENT

A farkon wannan makon, hukumar kula da kwallon kafa ta Turai UEFA ta ce babu daya daga cikin tawagoginta na kasa da zata shiga gasar FIFA muddin wadannan shawarwari na cefanarwa suka ci gaba da wanzuwa. Hukumar Kwallon Kafa ta Asiya (AFC) da hukumar Arewacin Amurka da Caribbean (CONCACAF) suma sun yi Allah wadai da matakin, inda suka ce bazai yiwu kwallon kafa ta zamo wata hanyar neman kudi ta kowace irin hanya ba.

Infantino ya cigaba da fuskantar matsin lamba bayan da babban mai ba da shawara Carlos Cordeiro yayi murabus, inda ya kira kudurin da “mummunar yarjejeniya ga mambobin FIFA, ga kwallon kafa, da kuma makomar wasan na dogon lokaci”, kungiyar hadin gwiwar kasashen kudancin Amurka CONMEBOL, wacce ake daukar shugabanta Alejandro Dominguez a matsayin babban aminin Infantino, ta bukaci karin bayani game da tsari da shugabanci da kuma tasirin da kudurin zai iya haifarwa”.

LABARAI MASU NASABA

EUROMATCH NPFL: Katsina United Ta Raba Maki Da Plateau United

Real Madrid Na Tattaunawa Da Bellingham Don Tsawaita Kwantiraginsa

A cikin sanarwar da aka fitar a daren jiya, Infantino ya ce an tsara kudurin ne a matsayin hanyar karfafa membobin kasashen FIFA, kuma zai cigaba ne kawai idan mafi rinjayen kasashe suka goyi bayansa, yace “bayan sauraron duk ra’ayoyin kasashen da kyau, ya bayyana cewa kudurin ya haifar da rarrabuwar kawuna, sakamakon haka an dakatar da kudurin da tun farko aka tsara” in ji shi.

Rabilu Sanusi Bena
+ postsBio
  • Rabilu Sanusi Bena
    https://hausa.leadership.ng/author/rabilu-sanusi-bena/
    EUROMATCH NPFL: Katsina United Ta Raba Maki Da Plateau United
  • Rabilu Sanusi Bena
    https://hausa.leadership.ng/author/rabilu-sanusi-bena/
    Real Madrid Na Tattaunawa Da Bellingham Don Tsawaita Kwantiraginsa
  • Rabilu Sanusi Bena
    https://hausa.leadership.ng/author/rabilu-sanusi-bena/
    Abubuwan Da Ya Kamata Ku Sani Kan Wasan Bayern Munich Da Arsenal
  • Rabilu Sanusi Bena
    https://hausa.leadership.ng/author/rabilu-sanusi-bena/
    Abubuwan Da Ya Kamata Ku Sani Game Da Wasan PSG Da Barcelona

MASU ALAKA

EUROMATCH NPFL: Katsina United Ta Raba Maki Da Plateau United
Wasanni

EUROMATCH NPFL: Katsina United Ta Raba Maki Da Plateau United

October 24, 2026
Real Madrid Na Tattaunawa Da Bellingham Don Tsawaita Kwantiraginsa
Wasanni

Real Madrid Na Tattaunawa Da Bellingham Don Tsawaita Kwantiraginsa

October 23, 2026
Abubuwan Da Ya Kamata Ku Sani Kan Wasan Bayern Munich Da Arsenal
Wasanni

Abubuwan Da Ya Kamata Ku Sani Kan Wasan Bayern Munich Da Arsenal

October 21, 2026
Next Post
Gyaran fuska

Yadda Ake Kula Da Fatar Fuska

LABARAI MASU NASABA

An Yi Wa Tinubu Ihun “Ba Ma Yi” A Taron Ƙaddamar Da Yaƙin Neman Zaɓen APC A Kaduna

An Yi Wa Tinubu Ihun “Ba Ma Yi” A Taron Ƙaddamar Da Yaƙin Neman Zaɓen APC A Kaduna

October 24, 2026
Sin Ta Lashe Lambobin Yabo Mafiya Yawa A Gasar Asiya Ta 2026 Ajin Masu Bukatar Musamman

Sin Ta Lashe Lambobin Yabo Mafiya Yawa A Gasar Asiya Ta 2026 Ajin Masu Bukatar Musamman

October 24, 2026
EUROMATCH NPFL: Katsina United Ta Raba Maki Da Plateau United

EUROMATCH NPFL: Katsina United Ta Raba Maki Da Plateau United

October 24, 2026
An Aike Da Masu Aikin Ceto Sama Da 5,000 Bayan Aukuwar Girgizar Kasa Mai Karfi A Jihar Xizang Ta Kasar Sin

An Aike Da Masu Aikin Ceto Sama Da 5,000 Bayan Aukuwar Girgizar Kasa Mai Karfi A Jihar Xizang Ta Kasar Sin

October 24, 2026
Tattaunawa Ta Musamman Da Shugaban Majalisar Dokokin Kenya, Moses Wetangula

Tattaunawa Ta Musamman Da Shugaban Majalisar Dokokin Kenya, Moses Wetangula

October 24, 2026
ADC Da Atiku Sun Zargi Gwamnatin APC Da Yin Watsi Da Jin Daɗin Malamai

‘Kana Cikin Rudu’ — Atiku Ya Mayar Wa Tinubu Martani Kan Zargin Yunwa Da Talauci

October 24, 2026
Fahimtar Cikakken Zaman Kwamitin Tsakiyar JKS

Fahimtar Cikakken Zaman Kwamitin Tsakiyar JKS

October 24, 2026
Allah Ya Bai Wa Annabi (SAW) Mu’ujizozi Fiye Da 2,000 A Alƙur’ani

Tsarin Kwalliya Da Adon Manzon Allah (SAW)

October 24, 2026
2027: Duk ’Yan Arewan Da Ke Takarar Shugaban Ƙasa Maƙiyan Arewa Ne – Akume

2027: Duk ’Yan Arewan Da Ke Takarar Shugaban Ƙasa Maƙiyan Arewa Ne – Akume

October 24, 2026
Wane Irin Tasiri Sabuwar Doguwar Tafiya Za Ta Yi Wa Duniya?

Wane Irin Tasiri Sabuwar Doguwar Tafiya Za Ta Yi Wa Duniya?

October 24, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.