Ganduje Ya Biya Hakkin ’Yan Fansho Sama Da Naira Billion 47 – Gawuna

Gawuna

Gwamnatin Jihar Kano Karkashin Dr. Abdullahi Umar Ganduje  daga 2015 zuwa yau ta biya hakkin tsofoffin ma aikata da aka fi sani da yan fansho har kimanin kudi har sama da naira million 47 daga hawan ta kawowa yau. Bias tsare-tsaren na hukumar biyan fansho da Garatuti tan Kano Karkashin shugabancin Alhaji Sani Dawaki Gabasawa da Offishin sa dake Titin Sokoto Road a Kanon Dabbo.

Wannan bayanin ya ya fitone daga bakin mataimakin Gwamnan Kano Dr. Nasiru Yusuf Gawuna a lokacin daya wakilci Gwamnan Kano wajen bikin biyan yan fansho su 1113 wanda aka biya su lokaci guda a wani buki da akayi a Dakin taro na Africa House dake tsakiyar Gwamnatin Jihar Kano. Gawuna yace biyan hakki nayau da kullum ambiya yan fansho sama da Billion 36  sai biyan kudin sallama na ma’aikata Garatuti naira Sama da Billion Tara 9 sai kuma wadannan na yanzu su 1113 sukuma sama da Billion Biyu 2 wanda duk aikin Gwamnan Kano ne Karkashin hukumar yan fansho wacce Alhaji Sani Dawaki Gabasawa.

Saboda haka ya yabawa Gwamnan Kano da Kwamishinan kananan Hukumomi Hon. Murtala Sule Garo da Babban Sakatare na ma’aikata da sauran jami’an Gwamnati da suka taka rawa wajen wannan aiki na alkairi inda kuma sha alwashin biyan dukkanin bukatun yanfanshon kamar yada shugaban Kungiyar yan fanshon na Kano Kwamared Gwale ya bukata daga Gwamnatin ta Kano. Inda shima Kwamared Gwale ya yabawa Gwamna Ganduje Akan wannan abun Alkairi na biyan hakkokin su.

Exit mobile version