Connect with us

LABARAI

Ganduje Ya Bude Sabon Shafi A Kano, Cewar Nasiru Kunya

Published

on

Shugaban karamar hukumar Minjibir a jihar Kano, Alhaji Nasiru Garba Kunya, ya bayyana farin cikinsa da kokarin da gwamnatin jihar Kano a karkashin Dr Abdillahi Umar Ganduje ke yi a tsawon shekara uku da ta kwashe a karagar mulki wajen bude wani sabon shafin inganta rayuwar al’ummar jihar Kano.

Ya bayyana hakan ne a lokacin taron bikin cikar gwamnatin shekara uku da a ka gudanar a gidan gwamnatin jihar, wato Africa House cikin makon nan.

Hon. Kunya ya shaidawa wakilinmu cewa, “mai girma gwamna ya bude wani sabon shafi a nan jihar Kano da Najeria bakidaya, inda yau mu ke murnar cika shekara uku da kafuwar wannan gwamnati ta bisa nasarori da abubuwan raya karkara da ya dabbaka a shekara uku, domin kuwa ba ya nan da ya yi a takaita ne, domin idan zai yi bayani kan duk abin da ya aiwatar, to kwana biyu ma ya yi kadan. Amma sabo da yanayi dole a takaita.”

Ya kara da cewa, “a yanayin da ya karbi jihar Kano na tattalin arzikin Najeriya, amma ya zama a ce ya yi wannan ayyuka a shekara uku, kai ka san abu ne mai kama da wahala, kuma idan ka duba ko aikin da ya gada yanzu an kusa kammalawa. Wannan ya nuna cewa lallai zai iya. Kirana shi ne mutanen jihar Kano da su fito su yi kokari su ga sun zabi mai girma gwamna a 2019.”

Ya cigaba da cewa, “ko kananan hukumomi ma an bar mu su wasu ayyuka, kamar karamar hukumata ta Munjibir na gudanar da aiki a wasu kauyuka na yin rijiyar birtsatse kamar guda 120 a kauyukan da ke kewayen garin Minjibir, sannan na gana makarantu kusan 25, na gyara masallaci wajen 110. Duk masallacin da ka gani da tayil, ni ne na sa shi.

“Don haka za mu cigaba da goyawa gwamna baya kuma a matsayina na shugaban karamar hukumar Minjibir zan cigaba da aikin raya kasa a fadin karamar hukumar, za mu cigaba da shiga lungu da sako, domin mu ga mun sauke nauyin da ke kanmu.”
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: