Abdullahi Muhammad Sheka" />

Ganduje Ya Kara Sassauta Dokar Fita Da Kwana Guda

Bisa la’akari matsanancin halin da rufe gari ke haifarwa a Jihar Kano, Gwamna Abdullahi Umar Ganduje, ya amince da kara sassauta dokar bude gari da ranar Litinin, domin ta zama daga cikin Juma’a, Lahadi da kuma Laraba su kasance su zama ranakun da kowa zai cigaba da harkokin yau da kullum, kamar yadda Babban Daraktan Yada Labaran gwamnan, Malam Abba Anwar, ya shaida wa LEADERSHIP A YAU.

Sai dai ya kara da cewa, “mu na horor jama’a da su cigaba da lura da matakan kariya ga cutar ta Korona. Ina sanar da kowa cewa, ranar Litinin yanzu ta zama rana ta hudu a cikin mako da a ka cire dokar hana fita. Yanzu jama’a za su iya fita a ranar Litinin daga karfe 6:00 na safe zuwa 6:00 na yamma.

“Amma dai dole ne kowa ya tabbatar da sanya takunkumin fuska, samar da tazara, amfani da man tsaftar hannu da kuma wanke hannu da ruwa mai gudana.”

Daga Gwamnan ya kara jaddada umarni ga dukkanin kasuwanni da wuraren taruwar al’umma da su cigaba da kiyaye ka’idojin da a ka sanar, “yayin da kuma ya zama wajibi mu hada hannu, domin magance wannan annoba bakidaya,’ a ta bakin gwamnan.

Exit mobile version