Girman Darajar Manzon Allah SAW (7)

A uzu billahi minas shaidanir rajim. Bismillahir rahmanir rahim. Wa sallallahu alan Nabiyyil karim. Assalamu alaikum warahmtullahi Ta’ala wa barkatuh. Masu karatu barkan mu da sake haduwa a wannan makon. Muna cigaba da bayani a kan girman darajar Manzon Allah (SAW) a wurin Allah. A makon da ya gabata mun tsaya ne a kan dabi’unsa (SAW) masu girma da Allah ya yabe shi da su a cikin Suratu Nuun. Za mu cigaba kan batun fassarar ayar da ke cewa “Lallai kai (ya Rasulallah) kana kan dabi’u masu girma”.

A wata fassarar kuma, Manzon Allah yana kan dabi’u masu girma ne saboda ba shi da wani nufi a cikin dukkan komai sai Allah, ba son ransa a ciki.

Malam Wasidi ya ce Allah ya yi kirari ga Manzon Allah da kyakkyawan karbarsa ga abin da ya bashi zuwa gare shi daga ni’imonsa, ya fifita shi a bisa waninsa (Allah ya fifita Manzon Allah a bisa waninsa), domin shi Ubangiji a haka ya halicci Manzon Allah da wadannan dabi’u masu girma. Tsarki ya tabbata ga mai tausasawa, mai baiwa, abin godewa (Allah Tabaraka Wata’ala) wanda ya saukake Annabinsa ga alheri kuma ya shiryar da shi zuwa ga alheri sannan ya dinga yi wa Annabin kirari da cewa ya aikata hakan (kyawawan dabi’iun). Har ila yau ya ce ya saka ma shi a kai. Tsarki ya tabbata ga Allah a bisa mamakin da ya game baiwarsa, ya yalwata fifitawarsa.

Bayan haka sai kuma Allah ya ba Manzon Allah hakuri da abin da ya alkawarta ma sa cewa zai yi wa kafiran azaba. Allah ya yi wa kafiran Makka alkawarin azaba tun da sun fada wa Manzon Allah (SAW) miyagun kalamai inda ya ce – ka yi hakuri – “za ka ga abin da zany i da su; su ma za su gani. Za su ga waye fitina za ta sama (kai ko su?). Ubangijinka shi ne ya san wanda ya bace daga tafarkinsa (Ma’ana kafiran Makkah, shi ya san mai shiryuwa (Annabi Muhammadu SAW)”.

Bayan Allah ya yabi Manzon Allah (SAW), sai kuma ya sake zargin makiyin Annabin (Walidu bin Mugira) da fadar mummunan halin makiyin. Allah ya dinga kirga aibobinsa. Ya aibaci Manzon Allah ne da Kalmar “mahaukaci”, a’uzu billahi. Sai Allah Ta’ala ya dinga yi ma sa tonon silili yana fadar aibobinsa a jere; daya-bayan-daya yana kare wa Manzon Allah. Allah ya lissafa abubuwan zargi ga kafiran sama da goma. Allah ya ce wannan da ya fada maka cewa kai mahaukaci ne, na yi ma rantsuwa kai ba mahaukaci ba ne, to shi bari ka ji irin sa: “Kar ka bi shi; makaryaci ne (Mu’umini zai iya yin wasu abubuwa marasa kyau amma ba zai karya ba. Karya mummunar aba ce). Kullum abin da yake buri shi ne ka sayar da lahirarka a kan duniya (kamar yadda ya sayar da tasa. Wannan shi ne almundahana, wato mutum ya mika lahirarsa saboda duniya). Kar ka bi dukkan mai rantsuwa wulakantacce (da ya yi magana kadan sai ya dinga rantse-rantse, ya ce ya rantse da Lata, ya rantse da Uzza. ‘Yan’uwansa kafirai suna jin haka sai suka ce wannan da Walidu ake yi. Da suka zo suka fada ma sa sai ya ce kwarai abin da Muhammadu ya fada gaskiya ne). Mai yawan zunde (yi da wani, mutum ya rika fadar laifin wani. A wurin Turawa wannan ba laifi ba ne, duk abin da wani ya yi in dai gaskiya ne a fito fili a fada, amma a Musulunci ba a son yada fasadi) mai annamimanci (yada jita-jita). Mai hana alheri, mai shisshigi, mai sabo. Mai kakkausan hali, bayan haka dan zina ne.”

Da ayar cewa dan zina ne ta sauka, Walidu ya ce duk abin da aka fada a kansa (a ayoyin baya) gaskiya ne, amma abin da aka fada na cewa shi dan zina ne bai san maganar ba. Mugira shi ne babansa; amma kuma Kur’anin Muhmmadu ba ya karya da aka ce ma sa shi dan zina ne. Sai ya zare takobinsa ya nufi wurin uwarsa ya ce ma ta ga abin da Kur’anin Muhammadu ya fada (cewa shi dan zina ne) kuma Kur’anin ba ya karya, ya abin yake ne? Sai uwar  ta ce “i, babanka mai kudi ne na tashin hankali a Makkah amma kuma ba ya iya saduwa da mace. Ni kuma na ji tsoron kar kudin ubanku ya tafi sai na tafi wurin mai kiwon dabbobi na gidanku shi ne aka haife ka”. Daga nan ya ce “haba wannan kuwa, don na san Kur’anin Muhammadu ba ya karya”. Amma kuma kamar yadda Allah yake fitar da haske daga duhu, Walidu yana da da babba a Musulunci, Khalid bin Walid. Dama lamarin iyaye bai shafar ‘ya’ya. Idan kafiri ya musulunta, musulunci ya zama ubansa. Idan shege wanda ba shi da uba yana kafirci ya musulunta, yanzu musulunci shi ne ubansa.

Allah Ta’ala ya zargi makiyin Annabi (SAW) da wadannan abubuwa na banza da yawa har zuwa ayar da Allah ya ce “idan an karanta ma sa ayoyinmu sai ya ce tatsuniyoyin farko ne”. Sannan Allah ya cika wannan magana da narko na gaskiya da cikar tsiyar wannan mutumin, da cikar halakarsa a wurin da Allah ya ce “za mu yi ma sa alama a kan karan hancinsa”. Kila an ce a ranar Yakin Badar an yanke hancinsa, kila kuma aka ce ya rasu kafin ranar yakin amma Allah ya kawo bala’in da ya yanke hancinsa.

Idan aka yi la’akari da duk wadannan, Allah ne da kansa (SWT) ya taimaki Manzon Allah a kan kafiran, ya rika kare ma sa kuma hakan sai ya fi cika da kai matuka bisa ga a ce Manzon Allah ne yake kare wa kansa. Sauran Annabawa da kansu suke kare wa kansu, amma Manzon Allah (SAW) Allah ne ya yi ma sa. Kuma wannan shi ya fi tabbata a cikin janibin girman Manzon Allah.

Ya ‘yan’uwa Musulmi mu yi hankali da taka-tsan-tsan a kan furta kalamai na rashin girma ga Manzon Allah (SAW). Domin tun daga ranar da Allah ya fadi wadancan maganganu a kan Walidu bin Mugira, duk idan ka ga makiyin Annabi (SAW) sai ka same shi da wadannan munanan dabi’un. Don haka kowa ya yi hankali, duk wanda ya fada wa Manzon Allah irin miyagun kalaman da makiya suka gaya ma sa, za ka gan shi da wadannan miyagun dabi’un. Allah ya kiyaye mu da aikata hakan.

Za mu dakata a nan sai Allah ya kai mu mako mai zuwa. Wa sallallahu alal fatihil khatimil hadiy wa ala alihi hakka kadirihi wa mikdarihil aziym.

 

Exit mobile version