“Ka iya Turanci sosai, a ina ne ka koyi Turanci mai kyau haka?…Ya yiwu akwai wasu da ke wajen taron nan da ba su kware kamarka ba.” Kwanan nan, shugaban kasar Amurka Donald Trump ya gana da shugabannin kasashen Gabon da Guinea Bissau da Liberia da Mauritania da Senegal a fadar White House. Sai dai a yayin ganawar, shugaba Trump ya yi wa shugaban kasar Liberia Joseph Boakai ba’a game da kwarewarsa ta iya Turanci, ban da haka, a yayin da shugabannin kasashen Guinea Bissau da Mauritania ke jawabi, ya yi ta sa musu kaimin gaggauta kammala jawaban.
Lallai hakan ya faru ne ba sabo da shugaba Trump bai san da’ar diflomasiyya ba, amma sabo da sam bai dauki shugabannin kasashen a matsayin kawayen hadin gwiwa na zaman daidaito ba, kuma rashin sani da girman kai da ya nuna sun jawo suka daga kasashen Afirka, inda mutane da yawa suka yi nuni da cewa, kasancewar Liberia kasa ce da bayi bakaken fata suka kafa, wadanda aka ‘yantar da su daga Amurka a karni na 19, Turanci harshe ne da ake amfani da shi a kasar, amma abin bakin ciki ne yadda shugaban kasar Amurka ya nuna rashin sani game da kasar da ke da irin wannan alaka da kasarsa a tarihi, kuma kalamansa tamkar yabo ne amma raini ne a zahiri. “Na ji ya zage mu ne ai, sabo da Turanci ne muke amfani shi a kasarmu”, in ji Archie Tamel Harris, dan kasar Liberia, wanda ya kara da cewa, “Ba na kallon tambayar da ya yi wa shugabanmu a mtsayin yabo. A ganina, shugaban Amurka har yanzu yana kallon Afirkawa a matsayin kauyawa da kansu bai waye ba.”
- Buhari Na Cikin Ƙoshin Lafiya Kwana Ɗaya Kafin Rasuwarsa – Mamman Daura
- HOTUNA: An Tsaurara Tsaro A Gidan Buhari Da Ke Daura
A hakika, ban da girma kai, taron nan da shugaba Trump ya gudanar da shugabannin kasashen, tun farkonsa ya nuna kwadayin Amurka game da albarkatun ma’adanai na Afirka. A maimakon manyan kasashe masu karfin tattalin arziki na Afirka da suka hada da Afirka ta kudu da Nijeriya da Masar da Habasha, Amurka ta gayyaci kasashen nan biyar na Afirka wadanda suke da muhimman albarkatun ma’adanai duk da cewa ba su da karfin tattalin arziki sosai.
A yayin da ya fara ganawar, shugaba Trump ya ce, kasashen Afirka na da “kyakkyawar makomar samar da wadata da ci gaban tattalin arziki”, wadanda suke da albarkatun man fetur da ma’adanai, kuma Amurka na sauya manufarta game da Afirka daga samar da gudummawa zuwa ciniki. A game da hakan, akwai masanin kasar Afirka ta Kudu da ya yi nuni da cewa, dalilin da ya sa Amurka ta gayyaci kasashen shi ne sabo da na farko, tana kwadayin albarkatun ma’adanai na kasashen, na biyu shi ne don tana fatan tinkarar kasashen Sin da Rasha da tasirinsu ke fadada a Afirka. Ban da hakan, masanin ya jaddada cewa, Amurka na fakewa da sunan “taimaka wa Afirka tsayawa da kafafuwansu” wajen kin samar wa Afirka gudummawa, bisa yadda take sauya manufarta kan Afirka daga samar da gudummawa zuwa ciniki.
A daidai lokacin da shugaba Trump ke mai da hankali a kan shawarwari da shugabannin kasashen Afirka a kan “ciniki” da “albarkatun ma’adanai”, hadin gwiwar Sin da kasashen Afirka na bunkasa yadda ya kamata. Tuni Sin da dukkanin kasashen Afirka da suka kulla huldar diflomasiyya da ita suka daukaka huldarsu zuwa huldar abokantaka bisa manyan tsare-tsare, kuma kasar Sin ta zamanto abokiyar ciniki mafi girma ga kasashen Afirka cikin shekaru 16 a jere. Tun bayan taron kolin dandalin tattaunawar hadin gwiwa a tsakanin Sin da kasashen Afirka da ya gudana a bara, kasar Sin ta zuba karin jarin da yawansa ya zarce kudin Sin Yuan biliyan 13.3 ga Afirka, kuma kudaden tallafin da ta samar musu kuma ya zarce Yuan biliyan 150. Idan ba mu manta ba, a watan da ya wuce, kasar Sin ta kuma sanar da shirin cire kudin kwastan a kan dukannin kayayyakin da take shigowa da su daga kasashen Afirka 53 da suka kulla huldar diflomasiyya da ita. Dalilin da ya sa kasar Sin ke samun karbuwa a kasashen Afirka kuma shi ne, sabo da yadda kasar Sin ke mai da kasashen Afirka a matsayin kawayen hadin gwiwa na zaman daidaito, da ma yadda take neman cimma moriyar juna da fatan ganin tabbatar da samun ci gaba tare da kasashen Afirka, kuma a hakika hadin gwiwarsu ya samar da alfanu ga kasashen Afirka.
Har kullum kasar Sin na ganin cewa, Afirka fagen hadin gwiwar kasa da kasa ne a maimakon fagen takarar manyan kasashe, kuma a ganinta, nauyi ne da ke rataye a wuyan kasa da kasa su tallafa wa ci gaban kasashen Afirka, kuma ya kamata su aiwatar da hadin gwiwa da kasashen Afirka bisa tushen martaba kasashen Afirka da sauraron muryoyinsu, don samar da alfanu ga al’ummomin kasashen na Afirka. Rashin cika alkawari abun kunya ne, kuma girman kai da son zuciya ba za su sa a amince ko ba da hadin kai ba.(Lubabatu)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp