‘Goje Ne Ya Kawo ‘Yan Daban Kalare Gombe’ – Gwamna Inuwa

Daga Sulaiman Ibrahim,

Gwamnan jihar Gombe Mohammed Inuwa Yahaya a ranar Talata ya yi zargin cewa Sanata Danjuma Goje ne ya kawo ‘yan ta’addan da aka fi sani da ‘yan Kalare a jihar.

Ya yi wannan jawabi ne ga manema labarai a fadar shugaban kasa da ke Abuja.

Hakan ya biyo bayan Wasu da ake kyautata zaton ‘yan bangar siyasa ne sun kai wa ayarin motocin Goje hari a ranar Juma’a a yayin da ya ziyarci Gombe domin halartar wani daurin aure.

Gwamna Yahaya ya shaida wa manema labarai a Abuja ranar Talata cewa amma tarzomar ta lafa.

Exit mobile version